← Book details Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 59

Sashe 49

Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Furzar da iska Zahra ta yi waje ta ce. "Zan barku ku tafi ne kawai saboda kun haÉ—a ni da Allah, amma da ba dan haka ba da saikun sake duk abinda ku ka yi".

Kallonta suka yi a gajiye suka ce. "Mun gode Aunty Zahra".

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Tohh!, yau an kira ni da sunaye kala-kala, wai yau ni na zama Aunty Zahra, harda su Hajiya Zahra, kwa ji da shi chan ta matse muku".

Ta faɗa tana mai nufar hanyar waje domin ta buɗe ƙofan. Ganin hakan ya sa suka tawo a guje.

Tsayawa Zahra ta yi tana mai kallonsu ta ce. "Kada ku fusata ni fa na fasa buÉ—e É—akin".

Da sauri kowanensu ya ja da baya.

Ƙarasawa bakin ƙofan ta yi kana ta saka maƙullin a jiki sannan ta buɗe musu ƙofan. Take suka haɗa ido da Sooraj wanda ke tsaye ƙeƙam ya harɗe hannuwansa a ƙirji.

Da sauri su Gimbiya Saratu suka zo fita. Nan suka ci karo da Sooraj. Kallonsu Sooraj ya yi yana mai yi musu kallon ƙurilla. Ya ce. "Mene ne wannan yarinyar ta aikata muku?".

Shiru kowanensu ya yi yayin da suka ji kunyar furta cewa Zahra ta sa su aiki. Washe haƙora Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Bakomai kawai dai muna ciki muna hira ne, gaskiya Zahra yarinyar kirki ce, domin ta yi mana tarba mai kyau". Ta faɗa suna mai kallon junansu.

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ya naga jikin kowannenku ya yi datti?".

Murmushi Samira ta yi ta ce. "Yahya fa bakomai wasa kawai fa muka yi, kasan muÉ—in ne har yanzu muna ji da yarinta".

Ganin hankalin shi ya karkata izuwa kan Zahra ya sa su saurin barin wajan.

Ƙarasawa inda Zahra ke tsaye Sooraj ya yi, yayin da yaje daff da ita har numfashin kowanensu na bugan na wani.

Take ta ga fuskarsa ta chanza izuwa maƙurar ɓaccin rai. Da sauri Zahra ta ja da baya, ganin cewa zai iya aikata mata komai ya sa ta juya da zimmar shige wa ciki.

Da sauri ya janyo hannunta. Take ta faɗa kan ƙirjinsa. Saurin ɗaga ta yi daga jikinsa sannan ya kwashe ta da lafiyayyun maruka har guda biyu.

Dafe ƙuncinta Zahra ta yi yayin da idanunta suka kaɗa suka yi ja.

Shigar da ita yayi ɗakin nata sannan ya shaƙe mata wuya cikin lion voice ɗin sa ya ce. "Wato abinda ki ka yi mana na abinci ma bai ishe ki ba, sai kin ja su ɗakin ki kin sa su abin da basu yi niya ba ko, to wallahi a yau zan koya miki hankali, harma na sa a kira ki, kice min ba za ki zo ba, lallai na yarda wuyanki ya isa yanka, na niyar rabuwa da ke amma ganin abin da ki ka aikata wa ƴan uwana da gimbiyoyi ya sa saina huƙunta ki". Ya faɗa yana mai ƙara shaƙe wa Zahra wuya.

Kakari Zahra ta fara yi, da sauri ta cire hannunsa daga wuyanta. Tari ta fara yi. Kallonsa ta yi ta ce. "Me ya sa za ka tambaye ni?, kafin ka tambaye ni kaje ka fara tambayar su mene ne suka zo aikata min, zuwa suka yi suka ce za su dake ni, kenen ni naje na same su na jawo su nan?, nayi ƙoƙarin ganar da su cewa suyi wa kansu faɗa su koma amma suka yi kunnen uwar shegu suka ƙi tafiya, kenen sai kace laifi na ne?".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Me ya sa to za ki saka su wanki shara harda wankin toilet sannan ki sa su Gimbiya Saratu suyi miki tausa bayan kuma ke Æ´ar aiki ce.

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Su da ma ba iyayenka ba kaji haushin abinda nayi musu, kai ka san abinda su biyar É—in nan suke aikata wa Mami da baka nan?, haka za su saka ta shara da aiki susa ta wanki".

ÆŠago da idanuwansa Sooraj ya yi wanda suka kaÉ—a suka yi jajir ya ce. "Mahaifiyar tawa suke yi wa hakan?, me ya sa ki ka barsu suka fita?".

Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Saboda sun roƙe ni ne shi ya sa".

Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Tabbas yau sai sun É—anÉ—ana kuÉ—arsu". Ya faÉ—a yana mai fice wa daga cikin É—akin Zahra. Ganin hakan ya sa Zahra ta yi saurin bin bayansa".

*********************
Amrah kuwa kidnapper's ɗin da suka sace ta basu nufi ko ina da ita ba sai wani ƙatoton gidan kango wanda ke tsakiyar jeji. Chan na hango ta an ɗaɗɗaure ta da igiya. Ƙoƙarin kunce kanta take amma hakan ya cutura. Kallonsu ta yi da rinannun idanuwanta cikin ƙaramin muryarta ta ce. "Ku kunce ni". Ta faɗa cikin jin raɗaɗi.

Ɗaya daga cikin su ne ya kira gov. Musa yana mai zayyane masa cewa aiki ya kammala. Murmushi gov. Musa ya yi ya ce. "Ku wuce da ita Lagos idan ya so daga nan sai a wuce da ita ƙasar waje".

Godiya É—aya daga cikin kidnapper's É—in ya yi. Sannan ya kashe wayar. Sakawa ya yi haka kunce.

Miƙe wa tsaye Amrah ta yi tana mai kalle-kalle ta ce. "Ina ne nan wajan?, me ya sa ku ka kawo ni nan?, su waye ku?". Tambayoyin da ta shiga yi musu kenan.

Shiru kowanensu ya yi mata ba tare da ya sanar da ita komai ba.

Basu yi aune ba suka ji tsayuwar mota a wajan. Da sauri gaba É—aya suka juya. Umar ne tare da su Ramlat suna mai nufo wa wajan.

Murmushi su kidnapper's ɗin suka yi. Take gaba ɗaya suka sara masa. Ƙarasowa wajan Umar ya yi yana mai sakin murmushi ya ce. "Nice job guy's". Ya faɗa yana mai maida kallonsa kan Amrah.

Su Ramlat kuwa da sauri suka nufi kan Amrah tare da rungume ta suna mai fashe wa da kuka.

Kallon jami'an nasa Umar ya yi ya ce. "Kun gano wane ne ya sa aka sace Amrah?".

Shiru jami'an suka yi yayin da ɗaya daga cikin su ya ce. "A'a yallaɓai".

Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Ƙarya ne, kada ku ji tsoro, kawai ku gaya min gaskiya".

Cire jikinta Amrah ta yi daga na su Ramlat sannan ta nufi inda Umar yake ta ce. "Me ya sa ka zo nan?, me ya sa ka saka aka sace ni?".

Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya ce. "Amrah zan yi miki bayani daga baya, yanzu bamu da wannan lokacin".

Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "A'a ni yanzu za ka faÉ—a min".

Shiru Umar ya yi na ɗan wasu lokaci sannan daga bisani ya ce. "Na sa an sace ki ne saboda na gano cewar akwai wani wanda ke ƙoƙarin ya sace ki, tun a gidan zoo na fahimci hakan, hakan ya sa na sa jami'ai na suka bibiyi bayan wanda suka zo gidan zoo, a nan muka kama ɗaya daga cikin su ya faɗa mana cewa wani ne ya ce su sace ki amma kuma basu faɗa mana ko wane ne ba, jin hakan ya sa a ranar da kika zubar da abinci na mare ki saboda kiji aushi ki fita idan ya so su kuma jami'ai na su sace ki domin ki kasance cikin tsaro. Amma ina mai baki haƙuri bisa ga marin da nayi miki kinji".

Shiru Amrah ta yi dan ita ba ta wani fahimce shi ba sosai. Waige-waige ta fara yi. Chan ta hango manya manyan bishiyu masu É—aukar ido. Washe baki ta yi tare da sakin murmushi da sauri ta nufi inda bishiyun suke ta fara É—ane su tamkar Æ´ar biri, aka ta fara aye wa kan bishiyu É—aya bayan É—aya tana mai yin tsalle a kansu.

Gaba É—aya babu abin da suke faman yi in banda binta da idanuwa.

Juyawa Umar ya yi ya maida kallonsa kan É—aya daga cikin jami'ansa ya ce. "Ku gaya min wane ne wanda ya sa a sace Amrah, kada ka damu kawai faÉ—a min".

Kallonsa jami'in ya yi ya ce. "Maganar gaskiya ainiyin wanda ya sa a sace Amrah shi ne mahaifin ka wato Gov. Musa Muhammad, mun gano shi ɗin yana aikata miyagun laifuka, yana safaran mata tare da shigo da ƙwayoyi ba tare da izinin kowa ba, am sorry to say sir but your Father is a big terrorist kuma bai cancanci zama Govnor ba".

Jin maganganun jami'in Umar ya yi tamkar saukar aradu. "Mahaifi na, safaran miyagun kwayoyi da kuma mata!". ya faÉ—a yana mai cigaba da nanata maganar.

"I can't believe this, ni fa jami'i ne, ban yarda Baba na zai aikata hakan ba".

"Gaskiya nake faɗa maka yallaɓai, amma idan baka yarda ba shi ke nen". Cewar jami'in.

Nan take ran Umar ya ɓaci yayin da yaji tsanar mahaifin na shi ya shiga cikin ranshi. Duban kowanensu ya yi ya ce. "Ku kulan mun da su zanje Kano yanzu wajan mahaifi na, sannan na kama da na damƙa sa wajan ƴan sanda".

Ya faÉ—a yana mai barin wajan kai tsaye inda motar sa take ya nufa tare da tada motan sannan ya bar harabar wajan.

*******************
*JIGAWA*
Shiga cikin dajin Aliyu ya yi yana mai faka motarsa. Fitowa ya yi daga cikin motan. Chan ya hango Safira zaune kan dutse gaba É—aya idanuwanta sun kumbura saboda kuka.

Ƙarasa wa inda take ya yi. Ganin Aliyu ya sa Safira saurin miƙe wa tsaye tana mai ja da baya ta ce. "Don't you dare!, karka kuskure ka zo inda nake. Nayi maka kallon mutumin kirki, ashe kai ɗin mugu ne, mena yi maka da zaka sa a sace ni?, wai kuma a hakan ni za ka aura?, i have never knew that you are a criminal until now. Na tsane ka Aliyu, wallahi ba zan yafe maka ba, idan kashe ni zaku yi kada ku mata lokaci wajan zaryar da hakan kawai ku aiwatar da abinda ku ke da niyar yi".

Shiru kawai Aliyu ya yi ba tare da ya ce da ita ƙala ba.

********
*KANO*

"Wallahi Gimbiya ba zamu rabu da ita haka ba, dole mu koya mata hankali har ita ta kai ta saka mu wanki muyi". Cewar Gimbiya Saratu.
Chapter 49 · 0% Book details