Sashe 2
Kundin Cinikayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Miƙe wa magatakadda ya yi tsaye sannan ya ce. "Assalamu alaikum Barka da safiya fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya". Ɗaukar takarda da alƙali ya miƙa mai ya yi sannan ya ce. "A wannan rana ta Litinin ɗaya ga watan february, a wannan kotun tamu mai dumbin albarka zamu ci gaba da sauraran ƙaran da wasu suka kawo bisa zargin aikata wannan laifi. Kuma a wannan rana za'a yi zama na ƙarshe na sauraron shari'ar Mrs Laila Abdullahi wanda hake tuhuma da safarar yara da salwantar dasu".
"Shin koh lawyer Mrs Lailah Abdullahi yana nan? da kuma lauya da ke kare wanda suke tuhumar Mrs Lailah Abdullahi yana nan? Idan gaba ɗaya kuna kusa muna bukatar ku Miƙe tsaye. Miƙe wa lawyer dake kare Mrs Lailah Abdullahi ya yi tare da bashi amsa da cewa, "Eh ina nan". Yayin da ɗaya tsagin shima ya miƙe tsaye.
Magana magatakadda ya fara yi kamar haka.
"Bayan hujjoji da haka gabatar a gaban kotu cikin zama da ya gabata na É—aya na biyu dana uku kotu zata bayyana matsayinta hakan wannan shari'ar". Yana kaiwa nan ya zauna.
Kallon lauyoyin dake kare kowane ɓari yayi sannan ya ce. "Shin akwai wata hujja da zaku gabatar koh A'a?".
Amsa wa suka yi da "babu".
Ɗaukar littafin dake kan tebur ɗinsa alƙali ya yi sannan ya ce. "Bisa la'akari da hujjoji da suka bayyana a gaban kotu waɗan da hujjojin duk suna nuna cewa abin da hake tuhuman Mrs Lailah Abdullahi, laifin ta ruga ta aikata kuma ba bu wata da lauyarta ya bayar ƙwaƙwara da zata gamsar da kotu cewa bah ita ta aikata wannan laifin bah. Don haka wannan kotun mai alfarma ta zata yanke mata hukunci kamar haka".
"Bisa dogaro da duba da haka yi da halin yana yin da ki ke ciki na juna biyu. Wannan kotun ta bada umarnin cewa ba za'a rataye ta ba har sai ta haifa abin ke cikinta, sannan wannan kotu mai alfarma ta bada umarnin cewa Mrs Lailah Abdullahi ta samu kulawa daga likitoci da kuma cikin magarƙama tare da bata abinci masu kyau har lokacin da za ta haifi abin da ke cikin ta, sannan nan da shekaru biyar masu zuwa za'a rataye ta. Wannan shi ne".
Kwamitin alkali ne suka tashi tare da cewa. "COURT".
Miƙe wa jama'a suka yi. Yayin da babu wanda yaji daɗin hukuncin da Alkali ya yanke sunso nan ta ke zai bada order da a rataye ta sai kuma suka ji hakasarin hakan sakamakon cikin dake cikinta.
Fita jama'a suka yi daga cikin kotun, yayin da jami'ai suka fito da Mrs Lailah Abdullahi tare da nufar inda motar police ke a fa ke.
Bah zato ta ji saukar mari kan fuskarta. Saurin dafa ƙuncinta Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta kalli matar hawaye ni bin kan ƙuncin ta.
"Allah ya tsine miki albarka, muna fuka maciya amanar ƙasa, dole ki gurbi abin da kika shuka". Cewar wata dattijuwa.
Ganin suna tunkaran inda Mrs Lailah Abdullahi ta ke ya sa jami'ai suka fara kare ta yayin da suka shigar da ita cikin mota. Nan ta ke suka ji saukar talkalma kan jikinsu yayin da suka fara bubbuga jikin motar da Mrs Lailah Abdullahi ke ciki. Ruff da ciki Mrs Lailah ta yi tare da fara rusa kuka. Kukan da ta ke yi ba saboda cin mutuncin da jama'a suka yi mata bah. Tana kuka ne bisa ga nadama da kuma takaicin abin da ya sa ta yarda da mutum. Haƙika yardar da ta baiwa mutane shi ne ya yi silar tarwatse war rayuwarta, shi ne mafarin kuma ƙarshe na rugujewar rayuwarta, tabbas ta aikata babbar dana sani a rayuwarta.
Tun da suka fara tafiya ba abin da ta ke sai kuka har suka isa harabar magarƙamar da ita.
Parking daya daga cikin police ɗin ya yi kafin daga bisani gaba daya suka fito daga cikin motar yayin da warders mata suka nufo motar tare da buɗe wa suka fito da Mrs Lailah Abdullahi waje tare da shigar da ita cikin magarƙamar mata wato ɓangaren mata sannan suka shigar da ita cikin kurkuku tare da ƙulle ƙofar wajan.
Guri Mrs Lailah Abdullahi ta samu ta zauna yayin da ta shiga yin tunanin koh a wane hali Æ´an uwa ta suke ciki a yanzu. Motsi tajiyo daga bayanta. Saurin waigawa ta yi tareda zuba idanuwanta hakan matar da ba za ta wuce shekaru arba'in zuwa sama bah a duniya.
Murmushi matar dake gefenta ta yi sannan ta ce. "Kada ki ji tsoro sunana Hajiya Binta nima kamar ke haka lokacin da haka kawo ni magarƙama na dinga kuka bah tare da aika ta wani laifi bah sa'anan ina ji ina gani na kasa aiwatar da komai saboda fito da gaskiya lamari. Kuma abin takaicin ma kina da juna biyu. Karki damu zan kula da ke tamkar ƴar uwa har ki sauka lafiya kinji?".
Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta ce. "Nagode sosai ƴar uwa". Ta faɗa tare da zaro wani babban littafi a cikin jakarda haka kama ta dashi. Sannan ta miƙa ma hajiya Binta littafin ta ce. "A gaba ɗaya magarƙamar nan ke kaɗai ce wacce na gani naji hankalina ya kwanta da ita, dan haka Ina son ki hadana min wannan littafin saboda yardar da miki domin na san duk abin da ya yi ƙarshe akwai mafarin faruwar sa, ina son ki hadana min shi".
Miƙa hannun Hajiya Binta ta yi tare da karɓar littafin wanda ya ke da matukar girman gaske. Juya littafin Hajiya Binta ta yi a hannunta sannan ta ce. "Wannan littafin fah mene ne a ciki?".
Murmushi Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta bata amsa da cewa. "Tarihi na da mafarin lamarin duk abin da ya shafi rayuwata da kuma abubuwa da dama wanda baki ba zai gama faÉ—ar su bah duk sune a ciki. Ina son ki hadana min shi koh bayan raina idan ina da rabon haihuwa a duniya ki bawa É—an da na haifa wannan littafin domin ya san wane ne shi, idan ma mace ce ki bata domin sanin wace ce mahafiyarta da kuma ita kanta".
"Kai maza ku taso kuyi aiki". Cewar wata warder a cikin magarƙamar.
Miƙe wa suka yi yayin da Hajiya Binta ta ɓoye littafin a ƙarƙashin pillow ɗinta. Tana saka wa suka fice daga cikin ɗakin da suke.
*BAYAN WATANNI UKU*
kwance ta ke yayin da ta ke jin bayan ta nayi mata ciwo ga wata iriyar azababbiyar ciwon mara da ta bi ta addabe ta. Yayin da cikin wanda ya yi tartsotso a gaba yake ta faman motsi.
Nan ta ke ta saki wata iriyar razananniyar ƙara!. A firgice matan dake cikin magarƙamar suka nufi inda ta ke yayin da suka shiga bata taimakon gaggawa. ta ke suka haɗa rufi da tsumma tare da zagaye wajan. Nan da nan mutane suka cunkushe guri ɗaya.
Cikin tsananin azaba na naƙuda take nishi tare da furzar da iska mai zafi yayin da numfashinta ya ke ƙoƙarin sarƙewa.
Ganin hakan ya sa Hajiya binta ta fara danna mata cikin tana ihuu yayin da saura matan suka shiga yi mata addu'ar sauka lafiya.
Ganin tana ƙoƙarin rufe idanuwanta ya sa hajiya binta ta yayyafa mata ruwa tare da tattaɓa fuskarta. Gani ta yi gaba ɗaya ƙarfin ta ya ƙare yayin da ɗan dake cikin ya kasa fitowa.
Ba zato suka ji kukan jaririya ta fito. Nan ta ke farin ciki ya lulluɓe fuskokin su yayin da suka shiga yi wa Allah godiya. Ɗaukar jaririyar Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Masha Allah, ubangiji ya albarkaci rayuwarki". Ta faɗa tare da miƙa wa ɗaya daga cikin matan magarkama suka sanya jaririyar a cikin tsumma tare da rufe ta. Sannan hajiya Binta ta ɗauki placentar yarinyar wanda haka yanke ta haƙa rami a can bayan magarƙamar ta bunne.
Mai da kallon ta kan Mrs Lailah Hajiya Binta ta yi. Nan ta ke Lailah ta kuma fashe wa da wani irin azababbiyar ƙara mai matuƙar razanarwa.
Cikin kiɗima da firgici kowanennsu ya mai da kallon sa kanta. Yayin da suka ga Lailah ta ci-gaba da naƙuɗa.
Zaro idanuwa waje Hajiya Binta ta yi cikin farin ciki ta ce. "Kenen ba guda É—aya bace bah akwai wata a ciki. Allah mun gode maka da ka albarkaci wannan baiwar taka da Æ´aÆ´a waÉ—an da sune za su zamo gata da kuma abun alfaharin ta.
Ganin É—an dake cikin ta kasa yin nishin da zai fito ya sa ta shiga cikin tunani.
Wani dabara ne ya faɗo mata. Miƙe wa ta yi yayin da sauran mata da warders suka bita da kallo.
Wani babban bokiti ta ɗauka mai matuƙar faɗi da girma yayin da ta cika she bokitin tsaff da ruwa. Tare da ƙoƙarin jan bokitin ta nufi inda Laila ta ke. Ganin ta kasa ya sa warders suka taimaka mata ta ɗauki ruwan yayin da suka kai har gaban lailah.
Ajiye wa suka yi yayin da suka cinciɓe ta tare da saka ta cikin ruwan.
Nan ta ci gaba da naƙuɗa yayin da jariri ya ƙi fitowa. Sai da ta ɗau hawanni biyu tana abi ɗaya bah tare da anji labari mai daɗi bah.
Zama hajiya Binta ta yi tare da girgiza kanta ta ce. "Ba za ta iya haihuwa da kanta bah saboda bata samu kulawar da ta ke buƙata bah, wannan aikin ba mune zamu yi bah dole likitoci ne zasu yi kuma wannan bah maganar kawo likitoci magarƙama bane tana buƙatar a kaita asibiti yanzu nan kafin lokaci ya ƙure.
Ɗaya daga cikin warders ɗin ne ta kalli Hajiya Binta ta ce. "Asibiti kuma? Ta ya ya zamu fita da ita cikin magarƙama bayan ita ɗin babbar mai laifi ce kuma kotu bata bamu damar aiwatar da hakan bah.kafin hakan ta faru dole sai da sa hannun kotu tukun nan".