Sashe 98
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba sai ta amsa masa da kai cewar babu komai ta kalli Namra ta yi saurin sauke idonta kasa. Na dauka zaka ce ya jikina Captain Namra ta tambaya tana kokarin kawarta abun da idanuwanta suke dauka. Baki da lafiya ne? Ita yake tambaya amman idonsa suna gurin Hurriya dake motsa siraran yatsun hannunta. Cizon da kunamu suka min jiya Sai a lokacin ya kalleta yayin da yake kokarin rage tsawonsa. Oh gaba daya na manta Wallahi, hankalina yana gurin yarinyar nan na shigo na ga tana hawaye na dauka wani abun ne ya faru Namra ta kalleshi irin kallon nan na yadda ya fada mata haka kai tsaye ba tare da tsoro ko jin nauyi ba. Shi kuma be yi hakan da wata manufa fa face gaskiya, domin ya ji duk wani takurawa da suke son su yi ma Hurriya, kuma ya ga wasu a idonsa, jiya ma ya shigo ya tarar tana kokarin kasheta, hakan sai ya kara masa tausayinta da kuma son ya taimaka mata. Me yasa kake damuwa da abun da ya shafi Hurriya Captain? Tambayar ta kutso ta huda makogaronta ta lakanci halshenta ta fito ta bakinta ba tare da ita kanta ta shiryawa hakan ba, sai dan mamakin jin furucin da bata tsammaci jinsa daga bakinsa ba. Sai da ya kalli Hurriya dake kallon Namra sannan ya aika mata da tambaya ba tare da ya amsa tata tambayar ba. Saboda Uwata ce. Me ye matsakarki da hakan? Ta kalli Hurriya har zata yi doguwar magana sai kuma ta takaita ma kanta wahala. Babu Ta mike tsaye ta aje remote din hannunta ta nufi stairs har ta haura ta shige dakinta bata juyo ba. Hurriya na ganin haka ita ma ta mike tsaye domin barin falon kamar daga sama ta ji yana bata umarni. Shiga Kitchen ki dauko min ruwa Ba tare da tace komai ba, ta juya alakar tafiyarta zuwa hanyar Kitchen din gabanta na faduwa, saboda hukuncin da Namra ko Momy za su yi mata na abun da ya faru yau idan Captain baya gidan yana kusantota tun kamin ta san sakamakonta. Ta bude refrigerator din mai kofa biyu ta d auko ruwan dake gefensa murfin ta dago ta rufe sai ta ga mutum tsaye jikin dayan kofar refrigerator din yana hade hannayensa yana kallonta. Ta dan ja baya kamar ta tsorata sai kuma ta nufi kofar fita daga kitchen din tana rike da gorar ruwan. Wa zaki kaiwa ruwan? Ta juyo ta dawo ta tsaya gabansa ta mika masa ruwan, gaba daya kwarjininsa ya rikitar da ita. Be karba kuma be fasa son sanin dalilin zubar hawayenta ba, ji yake kamar ba shi da natsuwa da sukuni idan be zama silar yayewar damuwarta ba a koyaushe, zuwansa ma a yau na tabbatar da ta ci abinci ne. Me kike yi ma kuka? Banbancin tambayar dazun da ta yanzu, furuci kawai, dazun yana mata ne in a code way a yanzu kuma kai tsaye ya tambaya, yana kallon da ya fi kama da an hallito idonsa ne domin kyakkyawar fuskarta. Ta karantu kuma ta haddace cewar baya son maimaita tambayar, baya bada umarni sau biyu, gashi fa saurin bacin rai wata kila ma yar karamar bindigarsa nan tana nan tare da shi, wata kila kuma idan bata amsa masa tambayarsa a wannan karon ba zai barta ta fice daga gurin ba. Kawai na jidadin yadda Appa yake kula da twins ne ya dora su a jikinsa yana wasa da su, abu ne da be taba yi ba, Twins ba su taba zuwa gidan nan ba sai jiya, ba su taba rike hannun Appa ba, ba su taba zama a jikinsa sai yau shi ne abun ya saka ni farinciki, har na yi hawaye _Me yasa ba su taba zuwa gidan ba? Su ba yayansa ba ne? Me yasa be taba wasa da su ba? Me ya faru?_ kusan lokaci daya wadannan tambayoyin suka jero masa, and then he realized be kamata ya tambayeta any of those questions ba, be ma kamata ya wuce gona da iri ba. Kwalin dake falo na ki ne ke da twins, kin ci abinci? Ta daga masa kai, sannan ta juya zata fice har ta isa kofar kitchen din sai kuma ta juyo, tana tunanin da wani suna zata kirashi, yadda Momy da Namra suke kiransa, a gudun bata masa rai ko rage masa girma ya saka ta raba sunan da sunan da take ganin ya dace. Yaya Captain... Ya kalleta yana hade ruwan da ya cika bakinsa da su, be amsa ba be kuma fasa kallon idonta da ta kasa dagowa ta kalleshi ba. Removed the last sentence Ta dago cikin hankali da natsuwa irin nata, ta kalleshi ta cikin gilashin idonta irin kallon dake kashe zuciyar namiji, da muryar dake narkar da zuciyar mai saurarenta ta ce. ...Ya... Ya... Al'adarsa duk wani wani suna da za a kira shi, idan ya wuce Captain da Jameel kauyanci ne, kalmar Yaya bata masa dadi ko kadan saboda haka ya hana kowa a familynsa yi masa inkiya da Yaya. Sai dai wacan karatun nasa ya kau, dokokin da ya gidanya sun rushe a lokacin da kunnuwansa suka yi kicibus da sautin da ya fito daga bakin Hurriya, she pronounce it so right, so different, so unique, so sweet. Say that again A wani yanayi da ya fi kama da rauni da tausasa halshe ta maimaita. ...Ya.. Ya... In a gentle way ya shigar da lip dinsa na kasa a bakinsa ya jika shi da yawunsa, yadda take furta kalmar YAYA ya san he missed alot, me yasa ba zai so ta kira shi da Yayanba? Ita din ba kamar yar'uwarsa ba ce? Repeat it... ...Yaya.... Ta sake fada da sanyin murya irin mai tsoro aikata kuskure, har tana tambayar kanta ko dai bata furta daidai ba? Ko kuma dai yana son ta yi ta fada ne har ya fusata bayan ta san baya maimaita kansa. _Miracle_ Ya furta a ransa yana kallon idanuwanta da farin yayi fari kamar watsa ruwan madara a ciki. Uhmm mmm Ya amsa irin amsar dake nuna ta fito ne daga kasan zuciyarsa. Ina son na tambayi wani abu... Wani shaukin kallonta ne ya daukeshi ya lulashi a wata duniyar da ya haddasa bugawar zuciyarsa a mabanbantan dakiku, natsuwarta na neman bukata a gurinsa ya saukar masa nishadi da ya samu kansa da lumshe ido ya bude yana kallonta kamar mai jin bachi. Name what ever you want girl... Ta hade hannayenta biyu guri daya ta rankwafar da kai, a wata murya da ta fi kama da tausayi da shagwaba ta ce. Kai ne ka ba ni wata takardar ranar da Hamad ya bata? Har ka yi min alkawari zaka dawo min da shi? Me yasa baki manta ba? Kwaryar ididonta ya fara tara ruwan da aka sirka da gishiri. Har yanzu ziciyata ta kasa amsar cewar Hamad ba zai dawo ba Ta tako ta matso kusa da ita yana kallonta Ni ma zuciyata ta kasa karya alkawarin da na daukar miki... Ya kara motsawa dap da ita ya rage tsawonsa har tana jin saukar numfashinsa. Wata kila zai dawo...! Zuciyarta da mugun karfi, ta bude baki saboda numfashin dake fita ta hancinta na kokarin karewa. Ina fatar haka... Ta furta muryarta can kasa sosai. Shi ma sai ya bata amsa da muryar mai dadi da ta fi kama da rada ya ce Idan wannan ne farincikinki... Ni ma ina fatan haka Hurriya... Duk wani abun da zai yaye miki damuwa ya sakaki a cikin farinciki ina fatan ki same shi Kana da kirki kana damuwa da ni, thank you for understanding me Kamar wata kwarariya haka ta yi masa magana muryarta a kasa fiye da yadda ta muryar shi take a lokacin da yayi mata magana. We all need that someone who get us like no one else, a right when we needed the most, you need shoulder to cry on... hura mata iskar bakinsa mai kamshi a fuskarta, atak, sai ta lumshe ido, murmushi ya fadada fuskarta hawayen bakinciki da suka rikide mata zuwa farinciki suka kawata kyauta. Kamar wanda ta tuna wani abu murmushin fuskarta ya bace bat, sai ta matsa baya da sauri ta bude idonta ta juya da fice daga kitchen din. Murmushi yayi ya taka backwards yana shafa kansa, ya daga gorar ya sha ya aje, sannan ya kai hannunsa saitin da aka aka yi gurbin zuciyarsa. Ajiya ce wannan, please ki ba ni hadin kai, saurin fushi breaking up with so many girls wannan duk na yafe miki, karki raba ni da wannan she's special na gane haka from DAY 1 na san ke ma kin san haka... Ya rufe idonsa ya sauke dogon numfashi, ya kai ma zuciyarsa duka a hankali yana aje mata sako. Idan kika raba ni wannan ni da ke duka zamu cutu, wata kila mu salwanta in one way or the other, so try to be strong please, ki ba ni hadin kai i hope you understand me Zuciyarsa ta buga da karfi tana raba sakon da yayi aika mata ga sauran sassan jikinsa da suka kasance mukarraban aikinta. Ya bude idon yana murmushi, sai farinciki yake kamar wani sabon ango, ba shi da kwashe kwashen mata, amman idan ya ga wanda hankalinsa ya kwanta da ita ya kan tallata mata soyayyarsa, sau uku ya taba yin haka, sau biyu aka yi nasarar saka ranar aurensa aka fasa saboda rashin hadin kan da zuciyarsa take ba shi. Falo ya fito ya zauna yana kallon tv sai dai gaba daya hankalinsa ba a gurin tv yake ba. Ya kusan minti goma shabiyar da zama sannan Appa ya sauko Momy na bayansa waya a kunnesa. Gani nan zuwa Ya fice tare da twins dinsa, sai jan rigarsa suke. Momy ta zauna tana mamakin ganin Captain domin Appa be fada mata tana da bako ba, ko da yake ba zata kira shi da bako ba a yanzu daman tuni ya zama dan gida. Namra ma da ta haura sama da bacin rai bata fada mata Captain ya zo ba. Ban san ka zo ba? Saboda Appa yana nan ne, tun dazun na zo ai Maa Shaa Allah yau dai na san babu aiki yau Sunday, kuma