← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 143

Sashe 5

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya sauka a kunnesu har su fahimta. Gida zan tafi gurin Gwaggo ba na fada miki ba? Sai na haihu zan dawo, za'a rika kai ku kuna duba ni Me yasa ba zaki haihu a nan ba? Kuma kike kuka? Hamad ya tambaya ya tambaya yana kallon cikin idonta kamar mai kokarin kure karyarta. Amma ta yi murmushi ta share hawayenta. Saboda bana jindadi a yanzu, bayan kun fita rashin lafiya ta taso min, kuma ina yawan yin haka a duk lokacin da kuka tafi makaranta, kuma kin fi kowa sanin bana son mai aiki na fi sha'awar na yi komai da kaina, ni da mahaifinku muka yanke shawarar zan koma gida na zauna har sai na haihu na samu lafiya, shiyasa ban tafi ba na jiran har sai kun dawo na sanar da ku, kuma na ja muku kunne dan Allah ku zauna lafiya Kalaman da Amma ta yi a yanzu sun sanyaya zuciyar Hurriya har ta samu kuzarin cire gilashin idonta ta goge hawayenta ta maida abokin rayuwarta. Allah ya baki lafiya Amma, zamu rika zuwa kullum Ba kullum ba dai sai a lokutan da mahaifinku ya zaba, kuma ku masa biyayya dan Allah ku zauna lafiya da kowa, ke dai na san baki da rigima Hamad ne mai matsala Hamad dai be sake cewa komai ba sai kallon mahaifiyarsa yake zuciyarsa na raya masa wani abun na dabam. Ku rike karatunku, boko da Islamiya karku saka wasa In Shaa Allah Amma zamu zama yara masu kirki Hurriya ta fada da murmushi a fuskarta. Hamad kam kallonta kawai yake kamar wadda aka cewa mutuwa zata yi anjima. Je ka saka tufafinka ku rika min kayan na kai mota Ya mike tsaye ya fice daga dakin cikin wani yanayi kamar ba shi ba, yadda ya natsu a lokaci daya wani tunani ya zo masa sai ka dauka wani babban saurayi ne. Amma wa zai rika ba mu abinci? Haka ne na manta ma yau ban girka muku komai ba, sai da ku sarrafa wani abun ku ci, ko kuma ku sha tea, idan mahaifinku ya dawo zai fada muku gurin da zaku karbi abinci, gurin Momy ko Hajiya Kaltume shi zaku tambaya Toh Amma Allah ya dawo mana dake lafiya Ameen Ta amsa tana danne abun da take ji a zuciyarta, sannan ta mike tsaye ta dauki hijabinta ta saka ta fara fitar da kayan Hurriya na taya ta kamin Hamad ya fito shi ma ya saka hannu suka dauka suka kai mata gurin mota. Ta saka wasu a bayan mota wasu kuma a back seat sannan ta shafa kan anta tana murmushi Hurriya ma murmushin take Hamad kuma ya hade rai kamar wadda aka yi ma laifi. Allah ya muku albarka ya tsare ku, kuma na fada muku zan kara jaddada muku ban da fada ku daina fada dan Allah A nan din ma Hurriya ce ta amsa Hamad kuma yayi kamar be ji ba, shi dai sai kallon mahaifiyarsa yake fuska babu annuri. Toh Amma Amma ta kalli Hamad tana jin wani yanayi na rashin jindadi. Hamad ba zaka ce komai ba? Juyawa kawai yayi ya shige cikin falon ba tare da ya ce mata komai ba. Sai ta lumshe ido hawaye suka sauko mata. Hurriya shiga ciki idan ina ganinku ba zan iya tafiya ba Ta fada still idonta na rufe, babu abun da take a zuciyarta sai ambaton Allah. Amma ko mu rakaki mu dawo Ta bude idon da sauri. Aa zan tafi da kaina ku kula da kanku Toh Amma Allah ya baki lafiya ya dawo dake lafiya Ameen Ta bude motar ta shiga tana share hawayenta. Hurriya ta daga mata hannu tana murmushi a tunaninta Amma na kewar rabuwa da su ne shiyasa take kuka, a kurciya da rawarkai irin nata bata damu sosai da tafiyar da Amma zata yi ba a yanzu, domin a ganinta gidan Gwaggo da gidan Appanta duk daya ne kara ma gidan Gwaggo tana musu gata tana barinsu su yi duk abun da suke so, ba kamar nan ba da wani abun Hajiya Kaltume ko Momy zata hana, wani abun kuma Amma ce da kanta zata hana. Juyawa ta yi ta koma cikin falon tana rufe kofar ta nufi dakinta ta cire uniform dinta ta dauki na islamiyarsu ta saka sannan ta sauko ta shiga Kitchen ta dauko cornflakes ta jika a two cups daya nata dayan kuma na Hamad, sai dai wanda yake na Hamad ya fi yawa domin shi baya wasa da cikinsa komai sai ya ci ya ji baya iya tashi yake bari, ita kuwa abinci be dame ta ba, bar ta ma ga kayan kwalama, ko abu mai ruwa dangin tuwo da shimkafa ba babinta ba ne shiyasa kullum gata nan kamar wadda ake diba ana miyar gidan. Jiki na rawa ta dauki cup din Hamad ta nufi dakinsa ta shiga sai ta same shi kwance ruf da ciki yana kuka. Hamad ga cornflakes na jika maka, ka ci mu tafi Islamiya... Yana jin sautin muryarta sai yayi tsif numfashi ma a hankali yake fitarwa dan kar ta ji. Hamad kuka kake yi? Ina ruwanki bana shan ki dauke abunki ki fice daga dakina Na maka kirki ne fa, Amma ta ce mu zauna lafiya amman baka ji ba, miye laifina dan na kawo maka abu Ba zan sha ba bana so Kar Allah yasa ka sha din, wanda baya jin maganar Mamanshi ya ji haushi ai, ko Sallah be yi ba kalleshi Sai a lokacin ya dago daga saman gadon ya sauko fuskarsa shabe-shabe da hawaye ya yi kanta, sanin dukanta zai yi ya saka ta saki kofin cornflakes din ta kama shi da kokawa daman sun saba, abu kadan idan ta yi masa sai ya ce zai daketa saboda ya fita girma jiki da karfi, idan ma ba wanda ya sani ba zai dauka ita ce kanwar shi ne yayan. Suna fara kokawa ya buga kanta ga kofar dakin sai kawai ta saka kuka ya fisge glashin idonta ya jefar a kasa ya saka kafarsa ya taka haka be masa ba sai da ya dauko talkaminsa ya saka ya bubbuga glass din ya fasa shi, domin zuciyarsa ta kawo idan kuma yayi fushi sai ya ji kamar ya tashi gidan, gashi baya tsoron kowa har Appa, idan za a masa dukan mutuwa sai yayi magana, sai dai yana da wata dabi'a na baya shiga safgar kowa sai idan an shiga ta shi. Wayyo Allah na... Hurriya ta fada tana kuka tana lalaba kofar fita dakin, domin ta daina ganin komai da kyau a yanzu sai dishe dishe saboda Hamad ya cire gilashin idon dake bata damar banbance fari da baki. Ta bude kofar ta fita tana lalaben hanya irin yadda makafi suke yi tana kuka har ta sauka kasa, da lalaben ta isa kofar falon ta bude ta fita tana kuka, dishe-dishe ta fita daga part din ta shiga part din Hajiya Kaltume har lokacin kuka take kuma ta san by that time Appanta baya gidan balle ta kai masa karar Hamad, idan kuma Appa baya gidan Yassar ne mai yi ma Hamad hukunci yadda take so, wani lokacin ko Appanta ta fadawa cewa yake ta fadawa Yayanta. Da kuka ta nufi bangaren Hajiya Kaltume ta isa har bakin kofar falon ta tura ta shiga. Hannu ta kai tana kokarin lalabawa ta ji waye a tsaye jikin kofar, sai ta ji an sauke mata lafiyayyen mari a fuska. Tsaye ta yi cak kamar wanda aka daukewa wuta tana kallon kasa, ta san kowa zai iya marinta a bangaren Momy ko Hajiya Kaltume, saboda suna ganin abun da take kamar da gangan take yi, shiyasa dole kawai ke kawo ta bangaren Hajiya, bangaren Momy kuma ko shiga bata yi idan ta shiga sai da wani kwarran dalili, domin Hajiya Kaltume na sake mata fuska irin na munafurci, Momy kam bata sakewa kowa fuska a gidan, har gobe ganin take level dinta ya fi na kowa a gidan, wannan na daga cikin dalilin da ya saka komai nata ko na anta take banbanta shi da na sauran, komai nata is unique and Expensive, gashi bata son ganin an Amma da Hajiya ko kusa da akinta, sai dai ita Hajiya tana karbar an Momy har so take suje a gurinta yanzu da suka girma. Haba Musib Haba Musib miye haka? Musib dake rike da wayarsa a hannu ya kalli Yassar da ya doso inda suke tsaye cikin bacin rai. Baka ga abun da ta yi min ba? Amman dai ka san idan kana gani ba zata maka haka ba? So take ta gane waye a gurin, me yasa kuke kyarar yarinyar nan ne please? Ku ba ku tausayin halin da take ciki? Ba ku ganin lalura da take tare da ita? Tana tare da lalura take yawo babu glass? Ni fa bana daukar wannan iskanci Ya amsa a fusace sannan ya saka talkaminsa ya fice daga falon, har lokacin Hurriya na tsaye bakin kofar ta kasa yin komai sai hawaye, a nan ta gane wani abun ake iya yi ma magana ko kuka, ta sani sarai tana kuka ko furta wani abun zai iya kara mata ko ya rufeta da duka, domin ba yau ya saba ba. Ko kwakkwaran motsi bata yi ba sai da ta ji ta a jikin Yassar ya rumgune yana bata hakuri sannan ta fashe da kuka. Yi hakuri Allah zai saka miki Hajiya Kaltume dake saukowa rike da plate ta soma fadin. Ya saka mata ga wa? Wai Yassar ba zaka daina wannan bakin shisshigin ba? Yadda kake da alaka da ita fa haka yake da alaka da ita, idan ma kwantar da ita yayi ya yanka ina ruwanka? Dagowa Yassar yayi ya kalleta. Haba Hajiya ai ko mai aikin gidan nan wani abu ba zai same ta na yi magana ki ce ina ruwana ba balle kuma Hurriya, marinta fa yayi kamar ya samu babbar mace Hajiya Kaltume ta yi fuskar tausayi kamar gaske yadda ta tambaya sai ka rantse bata san abun da ya faru ba, bayan kuma tana sama a tsaye stairs tana magana da Umm Khairi lokacin da Hurriya ta shigo. Ayya ah gaskiya be kyauta ba, me ta yi masa? So take ta tantance waye
Chapter 5 · 0% Book details