← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 143

Sashe 76

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bukatar yin kwalliya. Ta dauki turare ta mai kamshi ta fesa, sannan ta dauki man baki zata shafa sai ta tuna karyawa zata yi, hakan ya saka ta mayar ta aje ta koma saman gadonta ta kwanta tana duba agogo dakin dake nuna karfe goma daidai. Sai dai duk da haka bata son fita ta karya a yanzu ba dan bata jin yunwa ba sai dan bata son tsaba dokar Momy, sanin kanta ne Momy bata karyawa da wuri idan ta fita ta taba abun da Momy ta aje ba tare da Momy ta ci ba bata san iya hukuncin da zai biyo baya, dan haka ta kara minti talatin akai sannan ta fito kanta a sake babu dankwali gashin kanta sai sheki yake. Masu aikin Momy kawai ta samu a falon dayar na kallo dayar kuma na saka turaren wuta. Dan Allah Momy ta gama breakfast dinta? Wane breakfast kuma Hurriya breakfast tun yaushe har an wanke komai, na rana ma kadan ya rage a gama Hurriya ta ji babu dadi. Dan Allah Inna Shatu idan kuka gama abinci ku rika zuba min nawa dabam, ba sai an hade da na gida ba Toh Hurriya Yauwa na gode Ta nufi hanyar Kitchen kamin ta karasa ta ji muryar Namra a stairs tana kiranta. Me zaki yi a Kitchen Hurriya? Tea zan hada Saboda jindadi ko saboda me? Ban samu breakfast ba, shi ne zan hada tea To ki jira abincin rana ya kusa karasawa ai, idan yayi sai ki ci, kin san baki karya ba kika je kika kwanta kina ta bachi any how Namra ta karasa tare da isowa daidai gurin da Hurriya take tsaye. Hurriya ta sauke kanta ta juya domin barin kofar kitchen din. By the way Momy tace karki sake shigar mata kitchen idan kina bukatar wani abu ki yi magana, ba wai ki shiga Kitchen haka kawai dan jindadi ki ce zaki hada tea ba Hurriya ta juyo ta kalleta ta cikin gilashinta duba mai kyau. Amman Yaya Namra nan gidan ubana ne, ina da iko da komai kamar yadda kike da shi, me yasa kuke kyarata ne? Me na yi muku? Mamaki ya saka Namra rike baki. Ni kike fadawa wannan maganar? To ya kuke son na yi ne? Na zuba abinci a jiya Momy tace kar na sake zuba abinci idan bata ci ba, yau ina jin yunwa amman haka na wuni a daki saboda kar na fito na tararda bata gama karyawa ba, yanzu kuma na fito Inna Shatu tace an wanke komai, yanzu kuma zan hada tea ki ce ba haka ba, ko dan saboda jindadi zan iya hada tea Yaya Namra balle kuma ban karya ba Tana maganar hawaye na sauko mata. Inna Shatu ta aje kaskon wutar dake hannunta tana fadin. Abun be kai haka ba, tafi dakinki bari na hada miko tea din, ai da magana kika min sai na hada miki ma ba sai kin shiga ba A take Namra ta tsaka rantsuwa. Wallahi tallahi ba zata sha tea din nan ba, ke har kin isa? Ki fada min magana? Ina yayarki? Okay yanzu da kika dawo wani sabon rashin kunyar ne kike dawo da shi ko? Har kina wani tutuyar gidan ubanki, uban da baya sonki? Uban da be damu dake ba, uban da ke da banza duk daya a gurinsa? Kamin nan na yi gatan da wata ya a gidan nan bata yi ba, mahaifina ya so ni fiye da kowa a gidan nan, rayuwa ce ta sauya saboda bata tafiyarwa kowa a yadda ta saba ba, kamar yadda bata tafi min a yadda na taso ba? Sai aka sauya min da wata kaddarar mai daci, kuma hakan ba yana nufin zan tabbata a ciki ba, kar wannan ya zama abun gori a gurinki Yaya Namra, domin ke ma baki san a ina rayuwa zata kai ki ba, babu wanda ya san gobensa, kamar yadda ni ma ban san ya GOBENA zata kasance ba, dukanmu muna tafiya ne akan RAI BIYU ran farinciki da kishiyarsa, a WANI GARI rayuwa kaddara zata sauke mu na gaba? Babu wanda ya sani, na sani ni a yanzu tawa kaddara baka ce kamar BAKAR WASIKA, amman ba zan dauwama a haka ba... Bata daina kuka ba kuma bakinta be yi burki ba har sai da ta fashe kurjin dake mata ruwa a zuciya, sannan ta juya ta nufi stairs, har ta shige dakinta Namra bata gama mamakin inda ta samo baki haka ba. Amman zata aikata tun da ta iya munafurci zata iya aikata wannan ma ba mamaki, tab aiko kin dauko tuwa dafa kanki Ta shiga Kitchen ta dauko plantain, har ta yi aikin soyawa ta gama bata daina mamakin yadda Hurriya ta fada mata magana kao tsaye ba. Ji take ta yi sa'a da ni, saboda ya girma kuma Salim ya nuna yana sona ya koma gurinta, sai take jin ita ma ta kai mace.. To yarinya da sauran kuma na gode Allah da zai musanya min da ni, domin da ace CIWON SO ya kama ni na wannan Salim din da Allah kadai ya san yadda zata kalleni ma Wacece ke da ya kamata ki maida hankali ki yo ki gama, kina nan kina shiririta ko? Kuma kin fi kowa sanin halin Captain zai iya fushi yace ba zai ci ba, balle ma ya fada min da bako zai zo gidan nan Momy ta tambaya tana tsaye kofar kitchen din, mundayen zinarin dake wuyan hannunta suna amo. Namta ta juyo ta kalleta. Bako kuma? Haka yace amman be fada min ko waye ba Namra ta dan kalli gafe tana tunawa da maganarsu da Salim a jiya, and if she guess it right Salim ne bakon kenan, domin Captain ya fada mata alakarsa da shi. Uhmmmm wahalalle Wa...? A tsawace Momy ta tambaya tana mata wani kallo sakaka. And that's was the moment da ta yi realize bata fayyace ko waye ba. Wani tunanin nake yi dabam ba Momy ba Captain ba, na isa? Haba ko hauka nake ai ba zan fara ce masa haka ba Good Sai a lokacin Momy ta numfasa kamin ta bi miyar da Inna Shatu ke zubawa a karamin kula. Wa kike zubawa miya Shatu? Ko kun fara satar nin har da abinci kuma? Subhanallahi, Wallahi ban taba ba, Hurriya ce idan zan zuba abinci na zuba mata nata dabam Saboda me? Toh Hajiya yanzu kuma ni na ce wani abu? Sai dai ki tambaye ta Karki sake raba abincin mu da ita, salon da saka mana wani abu a abinci ko kuma saboda ita ta fi wani neda za a ware mata abinci, ban da ma rainin wayo idan Hurriya ta fada miki abu sai ki yi? Waya dauke ku aiki? Babu sisin mahaifinta a cikin biyan masu aikin gidana, juye miyar nan tun wuri Toh Hajiya Ta juye miyar ta aje kular ta fice. Anan ne Namra take bata labarin abun da ya faru tsakaninta da Hurriya. HURRIYA POV. Yadda ta yi spending Night and Morning dinta a dakinta haka ta zauna a dakinta har la'asar, saboda tana gudun ta sake fitowa ta sake yin arba da wani abun bakinciki, kukan kan ta sha shi kamar shi ne last hope dinta. Ta rumgume yunwa, bakiniki kuma yayi mata rumfa a zuciya, bata ji zata iya fita ba har sai da yunwa ta yi ta kawo mata farmaki ta hana ta shakat ta hana ta zaman lafiya balle kwanciyar gado lafiya. Sai da ta hada da karfin hali sannan ta iya Sallah la'asar saboda jikin nata babu kwari ko kadan, tana sallamewa ta dauko kur'ane ta karanta suratul Kahafi ta yi addu'a ta maida kur'anen a muhallinsa sannan ta dawo gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, fuskarta har ta yi rama saboda azumin dole da ya kamata tun jiya har yau da yamma. Siraran hawayen da suka zubo mata ta share sannan ta dauko hoto ta shafa a fuskarsa saboda boye abokin rayuwarta wato kuka, sannan ta ta shafa man lebe kadan, ta tashi ta dauko dankwalinta ta daura daidai yadda zai tsaya akanta ta karya karin dankwalin da kyau irin daurin Zarah Buhari, ta sako gashin kanta data daure ya sauko a gadon bayanta hakan kuma ba karamin karawa daurin nata kyau yayi ba, ta gyara gilashinta, ba dan komai ta yi haka ba sai dan karawa kanta courage, and tana jin she deserves to live a happy life kamar sauran sa'aninta balle kuma a yau da yake rana ta musamman wato jumma'ah even though zuciyarta na cike da damuwa da kunci, kuma kwalliyarta zata boye kukan da ta yi. Bata saka talkamin da suka saba sakawa idan za su saka kasa ba a haka ta nufi kofar dakinta ta bude idonta cike da tsoron arba da Momy ko Namra, ba dan tana jin yunwa sosai ba ba zata sauko ba sai dai bata da wani zabi da ya wuce ta bawa cikinta da jikinta abun da suke bukata. Ta dan rika skirt dinta ta dage shi kadan saboda ta samu sauka stairs din cikin jindadi, hakan kuwa sai ya bawa kyawawan kafafuwanta kuma farare fes damar bayyana. Tana hango falon da mutane gabanta ya buga da karfi, maza ne biyu da bata ga fuskokinsu ba, sai Momy da Namra dake falon, ganin babu sarki sai Allah ya saka ta cigaba da takawar without making any sound domin babu talkamin a kafarta, hakan kuma sai ya taimaka mata babu wanda ya lura da saukowarta har sai da ya rage sauran taku biyar ta sauka. Kusan a tare Captain da Salim suka dago suka kalli stairs din dake hagu da inda suke zaune, sai dai sun samu tsabanin aje idonuwansu a mabanbanta muhalli a jikin Hurriya, Salim ya tafi kai tsaye gurin fuskarta, yayinda Captain ya fara sauko idonsa a kan zarazaran yastun kafarta sirara masu matukar kyau zuwa leg dinta slowly ya bi kasanta da kallo zuwa gurin da Salim ya dade da yada zango wato fuskarta, Subhanallahi ba zai ce be taba ganin mata masu kyau ba a duniya but Hurriya is different tana da wani sirritacce kyau mai jam hankali maza zuwa gareta, wato kwarjini yana fisgar zuciyar wanda duk yayi arba da Innocent face dinta,
Chapter 76 · 0% Book details