← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 143

Sashe 54

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lonely, komai baya min dadi yanzu i miss those old days da zan zauna na yi hira da Appana yana dariya, na yi marmari jin muryar Amma, na yi marmarin ganinmu a inuwa daya, na yi marmarin Hamad fadan da muke ma na yi marmarinsa, Husna kowa yana da uwa a gidan yana da abokin hira ni kuma ba ni da shi, idan suna bukatar abu kowa zai je gurin mahaifiyarsa ta yi masa ko Appa ni kuma ba ni da uwa a gidan, idan kuma na kusanci gurin da Appa yake sai ya rufe ni da fada, baya ma son ganina Husna ta dafa kafarta tana jin tausayinta. Ki yi hakuri Hurriya, wata rana komai zai wuce ya zama tarihi Hurriya ta kalleta hawaye na mata sallama. Hakan na nufin Appa ba zai sake so na kamar da ba kenan? Hamad ba zai dawo ba? Ba haka nake nufi ba, ina nufin wata rana rayuwar farinciki zata dawo komai zai wuce, dazun ma sai da muka yi hirarki da Umma ita ma take tambayata maganar karatunki, tace kina bata tausayi sosai saboda halin da kike ciki Husna ina cikin kunci ina jin rashin sakewa sai na ji kamar a wani guri nake rabe ba a gidan mahaifina ba Komai zai wuce Hurriya, ki yi hakuri, me Amma zata yi da wannan kudin? Ta share hawayenta. Gwaggo ta fada min an kai Amma gurin magani kuma mutumen yace sai an bashi 150k shi ne dazun da Yaya Namra zata siya min abu na ce bana so ta ba ni kudin kawai zan bawa Amma, saboda Gwaggo ta ce basu da kudi yanzu duk sun kashe kudin da ya rage musu gidan da suke ciki za a siyar ni kuma bana son a siyar da gidan, kuma ban isa na tunkari Appa na ce ina son kudi ba, sai ya fara min fada ni tsoron ganinsa ma nake yanzu Innalillahi Abun har ya kai haka? Wallahi duk wanda ya raba ki da mahaifinki ya ci amanarki Hurriya, da a baya ne ko miliyan kika ce kina so Appa zai baki. Ya Allah ka dubi Amma ka bata lafiya, zan fadawa Umma in Shaa Allah zata cika kudin Hurriya ta rumgume ta da sauri. Na gode Husna, na gode Allah ya saka miki da alheri Ba komai, Allah ya kawo miki sauki Ameen, zan tafi kar a fara nema bana kusa Okay muje ki gaishe da Umma sai na raka ki Sun tashi a tare Husna ta saka Hijab dinta suka fito daga dakin, Husna ce ta yi mata jagora zuwa dakin Ummanta not because of gidan yana bakonta sai dan zata fi sakewa idan Husna ta shiga gaba. Mahaifiyar Husna ta amsa da far'a tana sakawa Hurriya Albarka sannan ta kara ja mata kunne akan addu'a da kuma hakuri. Karki yi wasa da addu'a kina ganin yadda aka maida mahaifiyarki bayan an cireta a gidan ubanki, ke ma kuma an shata muku layi, ki yi ta fadawa Allah matsalarki, sannan ki kara hakuri ki yi da hakuri Hurriya komai zai wuce In Shaa Allahu Umma na gode Ta tashi ta fito, suka jero da Husna a harabar gidan suna tafi suna hira, sam bata lura da Yayan Husna dake tsaye can gefe dare da Abokinsa yana hira ba har sai da abokin ya kirata. Hey Young Lady... A tare suka juya suna hada ido sai ya sakar mata mata murmushi ita ma ta dan yi masa murmushinta mai tsada kadan ta gaishe su. Ina wuninku Mutumen ya tako ta karaso gurin da suke tsaye tare da Yayan Husna, still tufafin da ta fara ganinshi da su ne sanye a jikinsa wato wando sojoji da bakar rigarsu T-shirt. Kin gane ni Ta daga kai kadan sai yayi murmushi. Ina kawarki? Yayata ce Amma fa ta iya driving, kun ba ni wahala dazun fa, but still i enjoyed it, it was fantastic Bata ce masa komai ba har ya sake wata tambayar. Nan unguwar kuke Nan ma bata amsa masa ba, Yayan Husna ya tambaye shi. Ka santa ne Ethiopian? Yeah i meet them today at Sarauta's Mall Ta juya zata fara tafiya. Please ki kirata mu gaisa idan kusa ne, or invite me na je na gaishe da Yayarmu Zan fada mata Ta fada ba tare da ta juyo ba. Okay ina nan ina jira As always bata ce masa uffan ba, sai kallon juna da suka yi da Husna, sannan ta shiga fadawa Husna yadda suka hadu... 08036126660 Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660 Har bakin gate din gidansu Husna ta rakota sannan suka yi sallama ta shigo ciki Husna kuma ta juya ta koma. Hanayenta nade cikin hijab ta shiga falon Momy, Namra na zaune a gurin da ta barta tana operating wayarta, Momy kuma na zaune gefenta a dayar kujerar tana cin abinci. Hurriya ta fara isa gurin Momy ta risina ta gaisheta. Momy sannu da gida Ina kika fito Namra ta yi karaf ta ce Ta fada min da zata fita Momy ta dauke kai ba tare da ta saks cewa komai ba. Hurriya ta tashi ta nufi gurin da Namra take zaune ta kai bakinta saitin kunnenta. Yaya Namra wannan mutumen da muka gani dazun yayi tsere da ke har kika karbi katinsa, na ganshi yanzu a gidansu Husna tare da Yayanta kuma ya ce a kira ki ku gaisa Namra ta wara ido tana kallonta da dan mamaki. Like really. Hurriya ta daga mata kai. Yace ba zai tafi yana can yana jiranki sai kin zo Ya akayi ya ganeki? Namra ta tambaya kadan kadan tana dan murmushi, Hurriya ta daga kafadunta alamar bata sani ba. Okay zan je Hurriya ta yi murmushi tana amsa mata da kai sannan ta daga ta nufi dakinta. After ta maida kofar ta rufe ta cire hijab dinta ta zauna bakin gadonta ta dauko Qur'anen ta bude tana karatu, bata daga ba sai da aka kira sallah Isha'i sannan ta aje ta dauki hijab din ta saka ta gabatar da Sallah Isha'i. Tana sallamewa Namra ta turo kofar dakin ta shigo tana murmushi. Na je mun gaisa, amman ya tambaya wai ko ni na hana mi dawowa Hurriya ta yi murmushi tana karanta addu'o'in sallame sallah. Namra ta zauna bakin gadon Hurriya. Yana da ban dariya, he's nice na yi mamaki yadda ya gane ki Hurriya ta shafa addu'ar da take ta mike tsaye tana kallon Namra irin duban nan na tuhuma (Zargi) Yaya Namra.... What? Nonono please daga haduwa da mutum? Don't please Ta tashi da sauri ta fice tana dariya, Namra ma dariyar ta yi ta hau saman gadonta ta kwanta, zuciyarta cike da farinciki alkwarin da Husna ta yi mata domin ta san zata cika. Washe gari da yamma Husna ta dawo mata da martanin cewar ta fadawa Ummarta kuma ta cika kudin and the most beautiful thing is ta tafi ta kaiwa Gwaggo kudin har suna saka mata albarka suna godewa Umma. Hurriya ta rumgume ta da sauri tana murna. Na gode sosai Husna Ba komai tarenmu y wuce haka, and Umma ma na ji tana magana akan makarantarki domin ta nuna damuwarta sosai akai gaskiya Ni ma abun yana damuna, ina son na yi ma Yayana magana shi zai iya magana da Appa ko Allah zai saka ya tuna da ni ya saka ni Hurriya da neman magana waya ce miki Appa ya manta da ke? Ta yi dariya. Haka dai nake gani kin ga bari na tashi ke ma haka kike da kin zo gidanmu baki wani dadewa sai ki fara cewa zaki tafi Laaaa ai to ni kin san yadda gidanmu yake ba ni da freedom ne, amman ke ba a miki tsananin da ake min, dan Allah ki zauna Husna na jidadin zuwanki Ba zan zauna ba, muje ki rakani Idan naje zan sake dadewa Naki wayon zan tafi idan ba zaki rakani ba Hurriya ta tashi da sauri ta dauki Hijab dinta ta saka, sannan ta bi bayan kawarta da tuni ta fice daga dakin, a tare suka daga kai suna kallon Ruma dake isar da sakon Hajiya Kaltume ga Hurriya. Ni kuma? Me na yi to Hajiya take nema na? Sako aka kawo miki Gaban Hurriya ya fadi ita da Husna suka kalli juna kamin su kalli Ruma da tuni ta wuce abunta ta barsu a stairs din tsaye. Kin yi da wani za'a kawo miki sako? Aa Wallahi ni wa nake da shi da zai kawo min sako? Kuma idan za a kawo sako da sanina ai ba za a kai bangaren Hajiya ba sai dai nan da nake zaune ko? Haka ne kuma, to sakon miye Ban sani ba Allah yasa ba wani sherin aka kulla miki ba Amin, bari na tafi kar na dade na yi laifi Husna ta dafata. Na rakaki? Aa dan Allah ki tafi, idan Hajiya ta lura da yawan zuwan da kike zata iya bata alakarmu, ni kuma bana son haka Shi ke nan Tare suka sauko Masu aikin Momy suka gaishe da bakuwar Hurriya duk da kasancewar ta yarinya ta amsa cikin Ladabi domin bata hadu da su lokacin da ta shigo falon ba, sai yanzu da zata fita. A karamin gate suka rabu Husna ta nufi babban gate din fita gidan, Hurriya kuma ta nufi bangaren Hajiya Kaltume gabanta na faduwa domin ta san ita kullum mai laifi ce a gurin Hajiya. Cikin tsoro da fargaba ta shiga falon kana kallon idanuwanta dake cikin gilashi zaka san babu kwanciyar hankali a tare da ita. Nesa da Hajiya Kaltume ta tsaya ta risina Hajiya ga ni Sako ne aka aiko miki, wannan dan iskan yaron da mahaifinki ya rabaki da shi wato baki ji ba ko? Ta girgiza kai da sauri. Wallahi na kyale shi Hajiya, daman ni ban san shi ba sai a bikin Yaya Khairi Amman mai gadin daya karbo sakon ai cewa yayi yace ga sakon da yace zai aiko miki nan Ban yi da shi zai
Chapter 54 · 0% Book details