Sashe 83
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Warahamatullah Ta sallame sallah magariba ta karo da azkar din sallah, sannan ta daga hannunta ta yi addu'a kusan rabin kowace addu'arta Amma ce, burinta Allah ya bata lafiya ta tare kamar da, sauran addu'o'in bukatu na rayuwa suna biyo baya ne bayan ta yi ma mahaifinta. Daf da zata shafa addu'ar Namra ta shigo dakin, saman gadonta ta jefa mata ledar dake hannunta kana ganinta kasan Hurriya ta shigar mata hanci da yawa. Na gaji da ajiyar wayar nan, idan ma baki bukata ki jefar ko ki kyautar, bana bukatar wani abu naki ko na Salim Ta juya tana jan kofar dakin da karfe Kamar zata ballata. Hurriya ta juya ta kalli ledar sannan ta mike tsaye ta nade carpet din ta zauna a bakin gadonta ta dauki ledar tana dubawa. Babbar waya ce har da sabon line da chocolate sai turare mai kamshi. Komai sai da ta bude ta gani musamman ma wayar da take jin kamar ta yi amfani da ita, sai dai tana tsoron kar Yayanta yayi magana domin bata taba rike waya ba, kuma kowa zai tambaye ta ina ta samu, idan ta amsa da cewar Salim ya bata za a tambaye ta miye alakarta da shi, to me zata ce? Wannan tunanin ne ya saka ta maida wayar a ledar ta cire chocolate din da turare ta janyo kwalin da Adam ya bata ta saka wayar a ciki, turaren kuma ta dora a mirror tare da sauran turarukanta da suke gurin. Sannan ta hau gado ta dauki chocolate ta fasa ta fara ci tana lumshe ido, daman ta san dadinsa domin Appa na siya mata lokacin da Amma take gidan, Amma ma da kanta takan siya mata ko ta bata kudi ta siya wani lokacin amman ban da wannan lokacin da komai ya canja. Knocked din kofar dakin aka yi, ta tashi da sauri tana cin chocolate din, kamar zata tambaya ta ce waye sai kuma wata zuciyar tace tashi ki duba mana, ta sauka saman gadon ta nufi kofar ta bude, Khairy ce tsaye tana lasa wayarta suna hada ido ta sakar mata murmushi ta kunno kai cikin dakin. Hurriya ruwa be saka ki zazzabi ba? Ta juyo tana amsa mata. Khairy ta kalli bakinta da hannunta. Me kike ci? Chocolate Eyyyy yar gayu, wannan mutumen da na gani a falo ya kawo miki? Tambayarta take irin tambayar nan mai halshen damo, tana wani murmushi ta kalailaye ido ita ga mai wayo. Ita kam Hurriya sai ta ji cewar ta samu mafita ai daman bata san ya amsawa mata ga wanda ya bata ba dan haka ta amsa mata da. Eh shi ya ba ni Khairy ta kama hannunta suka zauna bakin gado. Ba ni labari shi ma sonki yake? Aa ni aa To ai kin san ke din mai kyau ce ga farinjini, tsaraba ce? Haka na n dai ya ba mu Hurriya ta amsa tana jin kanta guilty saboda ta yi karya, abun da ba halinta ba. Dan'uwan Momy ne ko, ina yawan ganinshi ai ance dan yayanta ne Ta amsa tana daukar dayan chocolate din ta mika mata, a nan Khairy ta juya ta kalli bayanta, Chocolate ta gani ba daya ba ba biyu ba uku ba zai kai 12 kala dabam dabam kuma duk masu tsada. Kin ce ba sonki yake ba, amman ya kawo miki chocolate haka, maybe dai baki son na sani ne ko? Haba Hurriya ki dauke ni kamar kawarki mana, ko da yake dai be kamata na takuraki ba Ta mike tsaye. Daman Hajiya ce ta ce na kiraki Ni kuma? Me na yi to? Sai kin yi laifi za a kiraki? Haba Hurriya karki ma Hajiya wannan kallon mana Hurriya ta hade yawu tare da sauran chocolate din dake makoshinta, gabanta ya shiga faduwa ita dai ta san alheri baya sakawa Hajiya Kaltume ta kirata, sai da ta wuce gaba sannan Hurriya ta bi bayanta gaba daya ta saka mata tunani cewar Hajiya Kaltume tana nemanta sai ta fara tunanin ko fitar da suka yi ne a dazun, ko dai wani abun aka shirya mata? Ko Hajiya Binta ta sake yi ma Hajiya Kaltume wata maganar ne? Da tambayoyi kala kala ta sauko stairs din, a daidai lokacin da Captain yake hada takardunsa Namra na saka masa laptop din a jakarta. Sai da ta fara kallon Khairy kamin ya kalli Hurriya dake biye da ita a baya, a shi da alaka ta Hurriya dan haka ba shi da hurumin tambayar ta ina zata je ko kuma da waye take tare. Sai da suka fice sannan ya kalli Namra ya ce. Amman wannan yarinyar tana shaye shaye ko? Me ka gani? Fada min kika yi? Ya jefa mata bakar magana kamar yadda ya saba. Allah ya baka hakuri, tambaya ce kawai Ni m amsa na bayar, ke ma idan kika fara yi zan gane Namra ta yi murmushi tana mamakin yadda yayi saurin ganewa bayan kuma bata fada masa ba. Amman ba a tabbatar ba, haka dai ake zargi saboda friends dinta wasu daga ciki suna yi Be ce mata komai ba ya daga kansa ya kalli Momy ya kalli agogonta. Tun dazun ake ta kirana Momy sai gobe idan na dawo Zaka dawo Ta tambaya daga inda ta tsaya ganin kamar yana sauri, ya daga mata kai. Kullum zaku rika ganina har na gama watannin da zan yi In Shaa Allah Haka nake so, Allah ya taimaka ya maka albarka Jameel Ameen Ya amsa suna hada baki da Namra, sannan ya karbi Laptop dinsa. Dauko min wasu kayan da suke dakin Musib Okay Ya fita Momy na binsa da kallo, Namra kuma ta nufi stairs domin dauko masa sauran kayansa. Dan lokaci da ta bata kamin ta kawo masa jakarsa da ipod da agogon daya cire a dazun, har ya fusace ransa gaba daya bace, tana bude kofar falon ya ja motarsa ya barta nan tsaye rike da kayan tana kallonsa. Kuma har ka yi fushi? Ta juya ta koma cikin falon. Be karba ba? Momy ta tambaya tana operating remote ganinta da rike da jakar ga kuma fuska na bayyana labarin zuciya. Wata kila cewa zai yi na bata lokaci, wai har yayi fushi Ya kamata ki saba, ki lura da duk wasu abubuwan da baya so ki rika kiyayewa, kin ga yanzu hankalinsa ya dawo gidan nan wata kila ma saboda ke ne, kuma kin san halin Captain ba sai an fada miki ba shi da fushi da zuciya da saurin kai hannu ba su da maraba Amman Momy wani lokacin abun sa ya kan yi yawa, dauko kaya kawai sai ya zama laifi? Toh haka Allah yayi dan'uwanki ya zaki yi? Je ki aje kayan amman make sure kin kira shi a waya kin bashi hakuri Ta lumshe ido ta bude alamar damuwa. Shiyasa ya kasa zama da budurwa, komai aka yi masa bacin rai ne Momy bata bi ta kanta ba ta cigaba da kallon tv ba. Namra ta yi wuce da kayan ta fara taka stairs. HURRIYA POV. Da tsoro ta shiga bangaren na Hajiya Kaltume, da farko ta ji tsoro ganin Yayanta da Salma a falon sai ta yi zaton za ace ta yi wani abun ne, cikin karfin hali ta gaishe shi ta gaishe da Salma, yanayin yadda ya amsa mata ya fahimtar da ita bata da laifi a gurinsa. Khairy ta zauna kusa da shi. Wai yau na gaji da yawa, ina yin Sallah Ishan'i zan sha magani na kwanata Yasir ya dubeta Maganin me? Aikin me kika yi kika gaji? Pain killer nake son cewa, zan shafa a kafa driving na yi yau mun yi yawa sosai Good shiyasa na yi ta shigowa ina ganin kowa ban da ke, ke kawai kin fi son rayuwar waje, ki je yi ta abubuwan da kike so babu mai ce miki uffan, kawaye ma idan an rabaki da wannan gobe da wata za'a ganki? Khairy abun da kike yi fa ba shi da kyau, kuma ina miki fada ne ki gyara ba dan ni kadai ba sai dan ke kanki da future dinki, idan kika dauko wani abun magana ko, mutane za su zageki kuma kimar gidan nan zata zube, amman ke da Hajiya kun kasa gane haka Salma ta ce. An kusa aurar da ita Yaya ka kusa hutawa Mtscheeeeee Tsaki Khairy ta yi ta mike tsaye, ita dai har yanzu ba wani son auren take ba, ganin take gana cikin cin lokacin ta ne za a yanke mata, ko da wani ne balle Fadeel da ke da mata kuma da dukan alamu ba zai dauki irin rayuwar nan ta barin mace ta yi wasu abubuwan da suka tsabawa dokar Musulimci da al'adar Malam Bahaushe ba. Hurriya shiga ciki Hajiya na kiranki Hurriya ta nufi stairs din tana jin cewar idan dai ba mahaifinta zata tarar a dakin ba irin wacan karon da aka koreta, to komai mai sauki ne domin zagi da wulakanci na Hajiya Kaltume ta saba da shi dan haka be daga mata hankali. Sai da Hurriya ta haye sama sannan Khairy ta kalli Yayanta cikin sifar magiya da lalama ta ce. Yaya dan Allah ka daina irin fadan nan a gaban Hurriya Hurriyar bakuwarki ce? Ko kuma ita wata bare ce da ba zan miki fada a gabanta ba? Kuma da kin zama yadda nake so zan miki magana ne? And Salma was right idan an miki aure dole ai ki tsanu, and wannan ya zama na karshe da zaki fita ba tare da kowa ya san gun da zaki tafi ba! Dazun na tambayi Hajiya tace min baki fada mata gurin waye zaki je ba, ki daina wannan dabi'ar tun a yanzu Zan daina Yaya ba zan sake fita ba tare da na fada Ya fi miki, ai saboda kun samu Appa yana musu sauki ne yanzu, ace kamar baya ne da yake daukar zafi baku isa duk ku yi wannan ba, kuma ko. Yanzu idan kika sake irin haka sai na fasa miki jiki Ya mike tsaye. Yaya, ka yi hakuri dan Allah ba zan sake ba, ko dazun ma fa ba ni kadai na fita ba, tare muka fita da Hurriya ita tace gidan so boring shiyasa muka dan fita