Sashe 82
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya kamata mu yi ma aikin ba ita ba, kuma yanzu komai ya daidaita Hajiya Kaltume ta yi wani sukuku tana kallonta kamar wata mai tunani. Hajiya Fatee ta dafa kafardarta. Ki kwantar da hankalin, wannan mutumen amintacce ne, ni Wallahi na yarda da shi dari bisa dari, yanzu haka akwai kudin da na damka masa, zai siya min gona a kauye, wata shekara ni ma zan fara noma, yace min babbar gona ce zan yi mamakin abun da za a girba idan aka yi noma a gurin! Yanzu amincinki da mutumen nan ya kai har ki dauki kudi mai yawa ko bashi ya siya miki gona? Kuma da alama ma baki je kin ga gonar ba? Na yarda da shi ne fa Yarda? Mutumen da ba danki ba ba dan'uwanki ba? Kuma ba dan cikin gari ba? Anya kina cikin hayyacinki kuwa Hajiya Fatee? Mutumen nan fa abun da ke tsakaninmu da shi mu bashi kudi yayi mana aiki A wani yanayi na rashin jindadi da kuma gamsuwa da maganar da Hajiya Kaltume take, Hajiya Fatee ta gyara tsayinta ta ce. Yarda ta kawo haka? Idan babu yarda ai ba zamu bada kudin aikin ba ma, kuma ke ma da baki jidadin aikin da yayi miki ba a akan Hurriya da Iyami da baki kai shi makka ba, kuma ni ina ganin babu laifi a cikin shawara, shawara ce yayi min na abun da yake ganin ya dace ke kanki da kika kawata baki min irin wannan shawarar ba, kuma da babu yarda ba zan kira shi ya shigo har cikin gidana ba Duk wani abun da zamu masa a babin kyautata ba laifi ba ne, amman kulla kasuwanci ko fada masa sirrinki har ya san nawa ke ganinki wannan abu ne na sirri da be kamata ki yi ba, dan Allah Hajiya Fatee ki farka daga wannan bachin da kika fara Hmmm ba zaki fahimta ba Hajiya Kaltume, ke dai tafi kawai sai kin natsu zamu yi magana Tana maganar tana girgiza kai tana mamakin yadda kawar tata ta kasa fahimtarta a yau. Shikena zan kira a waya Hajiya Kaltume ta nufi motarsa ta bude ta shiga, direbanta dake zaune yana jiranta. Hajiya Fatee kuma ta juya ta koma gida. Ita dai har ta isa gida mamakin amince da yarda da kawarta ta dauka ta bawa Malamin da za a iya kira da boka, ita da bata da saurin yarda da mutane, ko da tsoronsa take ne. Can kuma wata zuciyar ta tuna mata da abin da ta manta. Ai ya kwanta da ita, wata kila ta nan ya samu sa'ar mallakarta da wannan mallaka ce kawai Ai ka ji matsalar, ba kwanciyar ba mallaka, da babu mallaka ma ai da sauki Ta fada a fili, har direbanta ya juyo da sauri yana amsawa. Na'am Hajiya Ba da kai nake magana ba, kawai ka yi aikin gabanka Toh Hajiya Ya cigaba da tukinsa. Suna isa ana sako ruwan sama Hajiya Kaltume ta fita motar ta shige bangarenta, a bude ta samu kofar falon babu kowa a ciki sai tv da ke kunne baturiyar dake screen din tana ta watsa labairai. Waye ya bar kofar a bude kuma? Ya maida kofar ta rufe sannan ta nufi hanyar stairs, kamar jira ake ta kawo kofar dakinta, tana bude kofar sai ta tafi kamar an turata ta fadi kasa jibisssss. Irin faduwar da ta taba yi har ta ji ciwo a kafa, ita ta sake yi a yau kuma ta sake jin ciwon a kafa kuma ta fadi a daidai gurin. Wayyo..... Innalillahi Subhanallahi Ta fada tare da tashi zaune da sauri tana yarfar da hannu saboda zafin da ta ji, idonta kamar za su fado saboda zarosu da take. Anya dai... Anya dai... Tana ta fada, ta matsa can gaba da sauri tana kallon gurin, kamin ta hankare zanen lace din dake jikinta ta duba kafar, ba ruwa ta taka ba balle ta ce tsantsin tile din ne ya kwasheta ta fadi, haka ma ba kofar dakin ba ce, and this is the second time da ta ji haka bayan faduwar farko da ta yi a lokacin da Maama ta samu matsala da mijinta har ta dawo gida. Mai kishiya fa baya mutuwar Allah, anya dai? Faduwa irin haka har kana jin kamar an turo ka? Da a stairs na fadi yaya kenan? Ta tambaye kanta kamin ta amsawa kanta. Ai zaka iya karyewa ma! Ta murgina ta rarrafa ta isa gurin gadonta ta cira daker ta hau saman gadon tana taba kafar dake mata mugun ciwo. Anya ba karaya na yi ba? Wannan bala'in zafin? Ina da makiya da yawa fa a yanzu, ita kanta Iyami waya sani ko ta ji sauki ma zata iya bibiyata ga Nafisa ma, ga wannan sabuwar matar da Alhaji ya dauko maganar, tun da fata suke su shigo gida su mallake komai, ga wannan malamin ma yanzu idan ya fahimci bana son aikinsa zai iya bibiyata fa... Khairy ce ta leko dakin ita kam nata jikin a sanyi ruwa, alamar ruwan sama ya fara dukanta kamin ta dawo gidan. Hajiya magana kike yi? Kofar dakinki na gani a bude da na matso kuma sai na ji kamar kina magana Hajiya ta kalleta ta sauke ajiyar zuciya. Shigo Ta shigo kamar yadda mahaifiyarta ta bukata. Ina kika je tun dazu? Gaba daya yau ba gida kika wuni ba, Yayanki ya shigo dazun yana ta min masifa wai ina barin kina fita any how ba tare da na san inda zaki je ba Dan Allah ki daina biyewa Yaya Hajiya, shi fa gaba daya rayuwarsa matsala ce, irin yadda yake son ya rika mana an wuce wannan yanzu how old I'm da zai ce a rika saka min irin dokokin nan! Kuma ma gidansu Habiba na tafi tare da Hurriya Hurriya kuma? Kika tafi da ita ko kuma ya? Da ita na tafi, yanzu muka dawo na ajeta a bangaren Momy Ni fa ban gane miki ba Khairy, wani sabon kawance ko kauna ce kika dauka kina yi ma Hurriya yanzu? Yarinyarda ita da uwarta bana da makiya kamar su? Ko kin manta halin da uwarta ta saka ni? Oh hudubar yayanki ce kika dauka kika bar tawa ko? Aa Wallahi Hajiya, ba dan wani abu ba da sai na ce miki na fiki tsanar Hurriya da mahaifiyarta fiye da ke ma, amman ya kamata komai zamu yi, mu yi shi cikin hikima da wayo, ta haka ne ma zamu rika sanin wasu abubuwan Karki kuskura ki ce zaki nuna min kin fini wayo, daga haka ban san iya abun da zai biyo baya ba, ga yayanki nan ya dauko zancen auren Rukayya gaba daya su kuke ku haukata ni na ga alama Aureta kuma? Khairy ta tofar da yawu. Wallahi ba zamu tana yarda Yaya ya dauko mana wannan bakin jini ya kawo mana ba, tab....! An gama da yayarta ita kuma a dora da ita, ga yarta ma ba a gama da ita ba? Kara ma Amma da wannan Rukayyar kana ganinta kaga marar kunya, wato ba su hankaltu ba da har za su dauko wasu Rukayya su aurawa Yaya? Mai kwadayi kuma? Suna ganin sun samu a gurin Iyami ita ma ai suna saka ran samu a gurinta ne Amman shi Yaya har idonsa yayi rufewar da zai rasa matar aure sai Rukayya? Kamar be san alakarta da Iyami ba? Ai ni da Iyami daya yake kallonmu, amman matukar ina raye, wannan abun ba zai taba faruwa ba, gashi nan duk saboda Iyami abubuwan sun zo min ta yadda ban zata ba, dan kyaun nan ke janzu ba komai ba Shi ne fa, gaskiya ko kin kyale ni ba zan kyale ba Wallahi Maganar take tana cika da batsewa gaba daya maganar ma ta bata mata rai. Allah kadai ya san sherin da suke bibiyata da shi, ko dan ma a samu sa'a ta ai zata iya aura masa ita, a mallake shi a juya shi yadda ake so, idan aka gama ruwan nan ki shiga ki kira min Hurriya Toh, amman Hajiya ki ja masa kunne gaskiya ba zai auri Rukayya ba Sha kurumin ki, idan kin shiga kiranta ma ki faki idon Nafisa ki kira min Kulu Ta latsa kafarta tana runtse. Ciwo kika ji? Ture ni aka yi Wallahi Turewa kuma? Eh mana, ai ba faduwa ce haka nan ba, wannan ne karo na biyu, nan gaba ban san ina aka dosa ba kuma Ikon Allah Hajiya ta amsa mata. Ikon gaskiya, na fi karfin kowa nan gani nan bari sai gani sai hange, kowaye ba zai iya da ni ba Wallahi Khairy ta dan yi dariya yadda Hajiya take maganar da fada kamar wanda yayi mata hakan yana gabanta. Kamin ta mike tsaye ta fice daga dakin. Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... HURRIYA POV. Assalamu Alaikum Warahamatullah Assalamu Alaikum