← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 143

Sashe 65

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660 Yau Namra ce a gidan na mu Hajiya ta fada tana kallonta, cikin karfin hali Namra ta yi murmushi ta nemi guri ta zauna. This is the first time da ta ji bata sha'awar hada ido da Hurriya. Hajiya barka da dare Barka, yau na ci arzikin Hurriya kin zo gidan nan kenan Haba Hajiya daman can na kan zo na duba ki fa, karki ce saboda Hurriya na zo To ssboda wa kika zo tsakaninki da Allah? Sabosa Hurriya Cewar Namra tana dariya, Hurriya kuma dadi ya cika ranta jin cewar yar'uwarta ta biyo sawunta, sai dai abun da bata sani ba shi ne ba tafiyace ta zuwa gurinta kai tsaye ba tafiya ce ta Salim ba dan ita ba. Yaya Namra ina wuni Lafiya Kalau Hurriya Ta amsa tana murmushin da ya fi kama da an mata dole. Ato ke dai kin kyauta da kika biyo sawu, daman ke kin fita dabam ba da yan'uwanki, amman Nafisa kam da Kaltume rayuwarsu tana ba ni mamaki, yanzu Hurriya ta gama karanta min abun da ya faru, ashe abun har ya kai a laka mata sata Namra? Namra ta kalli Hurriya ba tare da tace komai ba ta dauke ido. Ban yi zaton zamu yi ma yarinyar nan haka ba, saboda kawai bata da uwa cikin gida sai ta zama abar wulakantawa, ban jidadi ba, yanzu ko korar nan da aka yi mata da ke ce ko Khairy ai babu wanda uwarta zata yarda ta bar gidan, da bata da ni ya rayuwa zata zame mata? Ke kuma ya kamata ace kuna nunawa iyayenku wasu abubuwa be kamata su yi ba, wani abun ba za su lura ba sai an lurar da su Hurriya dai kanta na kasa tana jin kamar ta rufe bakin Hajiya Binta. A kokarin Namra na kawar da maganar ta kalli Hurriya tana jin wani abu a zuciyarta game da Hurriya ta ce. Da bako nake fa, kuma ke yake jira magana ya zo yi da ke? Hurriya ta dago ta kalleta. Hajiya kuma ta tambaya. Wane bako kuma? Ita tasan wa nake nufi, ya zo ne yayi magana da ita sai mu tafi Waye ne ban san waye ba? Salim Sarauta... Yana waje Namra ta amsawa Hurriya kai tsaye kamar yadda ta bukata. Hajiya Binta kuma ta kalli Hurriya ta ce. Saurayinki ne? Aa Saurayin Yaya Namra ne, yana yawan tambaya ne, maybe ko yana son mu gaisa ne To tashi ki tafi, idan kun gaisa sai ki dawo Ta amsa umarni, Hajiya ta tashi ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka sannan ta fito ta fice daga falon. Tana fita Hajiya Binta ta fara karantawa Namra sakon da zata bawa Momy da Hajiya Kaltume. Cikin natsuwa Hurriya ta fita harabar gidan, sai da ta gama kallon ko'ina sannan ta nufo gate domin bata ga bakuwar mota a gidan ba bayan motocin da Appa ya ajewa Hajiyarsa guda biyu. Sai da ta fita gate din gaba daya sannan ta yi arba da motar dake fake gefen gate din gidan, tun kamin ta fito zuciyarta ta raya mata a waje ya aje motar ganin babu bakuwar mota a harabar gidan Hajiya Binta. Kamin ta karaso ya bude motar ya fito yana taba wayar hannunsa, da alama wani abun yake typing amman idonsa yana kanta har ta iso, cikin far'a da sakin fuska ta yi masa sallama da muryarsa mai dadin sauraro. Wa'alaikissalam Young Lady Sannu da zuwa barka da dare Barka dai, fatar na same ki lafiya Lafiya Kalau Maa Shaa Allah Ya fada yana raba ido, ko za su samu gurin da za su zauna. Ko zamu iya rabawa daga can kar na aje ki yi ta tsayuwa, saboda ina da tarin maganganu buhu buhu Allah yasa ba laifi na yi ba, Yaya Namra tace min zamu gaisa ne Laifi kika babba kuwa, kusa kisan kai ma Ta zaro ido hankalinta ya fara tashi. Ni... Ke fa, amman yanzu mu fara zama tukuna Nan ma ya isa ka fada min laifina ni hankalina har ya tashi Yadda take da kin sakin jiki zuciyarsa ta raya masa idan ya bukaci su shiga motar su zauna ba zata yarda ba, ba kuma zai iya forcing dinta suje cikin gidan su zauna ba. Dan haka ya bude mata mota ta gefen da yake ya matsa baya. Zauna nan, ni sai na tsaya zan yi magana da ke ne Bata son ta musa masa a karo na uku, haka kuma sanin cewar shi din masoyin Namra ne yasa bata son ta aikata abun da zai fusata yar'uwarta. Juyawa ta yi ta kalli gate din gidan. Kamar ya san abun da take sakawa a ranta kamin ta juyo ta tsinkaye shi yana fadar. Karki damu, babu wanda zai fito har sai mun gama maganar da zamu yi Ni fa zan iya tsayuwa ko na awa nawa ne Shiyasa Namra ta kasa shawo min kanki, da alama dai kina da kafiya Hurriya kamar zan sha wahala, please ki zauna zaki fi fahimtar magana ta idan kina zauna Ta taka ta zauna cikin motar kafafuwanta da fuskarta duka suna waje suna fuskar gurin da Salim yake tsaye. Wayar dake hannunsa ya duba sai ya amsa kira da sauri. Ka iso? Ya juya bayansa. Oh na ganka Ya fada tana daga hannu ya tare fuskarsa daga haske motar dake haske fuskarsa. Sauke wayar yayi ya saka aljihunsa. Ina zuwa Young Lady bari na mikawa wani, sako Ya zagaya da sauri dayan side din, hakan ya bawa motar mai tsananin haske haske fuskar Hurriya har sai da ta saka hannu ta tare idonta da ba lafiyayyen ba. Gammm ta ji an rufe mota sai dai ba zata iya fadar motar da aka rufe ba, ta Salim ce dake neman sako kamar yadda ya fada mata ko kuma ta wanda za a bawa sakon ne? Ganin Hasken dake hasketa ya dauke yasa ta janye hannunta daga idonta sai ta yi arba da mutum tsaye a gabanta nesa kadan da gurin da Salim ya tsaya a dazun, kasansa ta fara kallo har ta daga kanta sama ta kalli fuskarsa, akwai hasken wutar gidan dake haska ko'ina ta bawa kowa damar ganin abun da yake wakana a harabar, sai dai hasken be kai ya tantance mata fuskar waye tsaye a gabanta ba, saboda lafiyar idonta, sai dai tabbas zata iya shaidar wani abu da ba zata kira da shi tsoro ba, kuma ba fargaba ba ce, wani abu ne da ya cika idonta ya aikawa zuciyarta da sako ta fara bugawa da karfi, a rashin zato da tsammani ta samu kanta a tsaye gabansa numfashinta na kokarin sarkewa. Me kike yi a nan? Muryarta ta daki dodon kunnensa, a nan ta gane duk wani abu da ta ji gabanin fitar sautin muryarsa shimfida ce. Ka santa ne? Salim ya tambaya yana rufe motar ta dayan bagaren sannan ya zagoyo. Ba nan ne gidansu ba, me take yi a nan? Ta daga kai da zimmar tantance waye tsaye a gabanta jin furta cewar ba nan ne gidansu ba, wannan abun dai irin na dazun ya sake tare idonta daga kallon fuskarsa idanuwanta suka shammaceta ta sauke su a fadaddan kirjinsa mai matukar fadi da yalwatacce damtse, cikin wani yanayi da yafi kama da sihiri jikinta ya fara kyarma kadan ta kasa tsayar da idanuwanta guri daya. Ba magana nake miki ba? Muryarsa bata yi kama da muryar da ta taba ji ba, idan ma ta taba to ta manta, balle kuma fuskarsa da kwarjinsa be bari ta kalleta da kyau ba balle ta tantance waye shi. Ni na sallamota magana zan yi da ita Salim ya fada yana kallon Saurayin dake gabansa da ba zai wuce sa'ansa ba. I said ba nan ne gidansu ba Eh amman ta dawo nan a yadda na ji Namra ta fada? Mutumen ya kalleshi da kamar mamaki. Namra? Ita ma ka santa kenan? Cousin dita ce Wow baka taba fada min ba Dole ne sai na fada maka alakata da kowa? Ina tarkadun? Shikenan kuma ka dawo ba zama lafiya, sai bakar magana kamar dan kishiya, ga su Ya mika masa takardun dake hannunsa. Tun da ka dawo ba mu samu zama ba, gashi ni kuma an min transfer Be ce da shi komai ba har ya gama duba takardun sannan ya juya. Salim ya bishi da kallo yana fadin. Ajiyarka ta nan Captain, he's living healthy amman... Ya juyo da karfi ya kalleshi fuska babu annuri. Ban tambaye ka wani abu game da haka ba, idan ina bukatar sani wani abu game da haka ni zan tuntuba watch your mouth Ethiopian... Akwai maganar da nake son mu yi ne, akwai abun da ya kamata ka sani Ba a nan ba Ya nuna gurin da ya tsansa, sai da ya kalli Hurriya sannan ya dauke idonsa ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Hurriya ta daga hannunta da sauri saboda haske motar da ya dawo yana haska idonta, sai da ya ja motarsa ya bar gurin sannan Hurriya ta sauke hannunta. Sorry na bata miki lokaci, wasu takardun ne na bashi na aikin mu Ita dai bata ce uffan ba sai mamakin inda ya santa take. Ashe ya sanki, he's very good friend of mine, yana da kirki sosai sai dai akwai zuciya abu kadan ya bata masa rai, yana gaba da ni a aiki amman dai abokina ne sosai Ta dauke idonta daga dayan gefen ta kalli kasa. Zauna please Ta girgiza masa kai alamar ba zata zauna
Chapter 65 · 0% Book details