← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 143

Sashe 130

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dauki hijabinta dake gefen kujera ta saka ta fice daga falon. Sama da haura zuwa dakin da Captain yake, tana tura kofar dakin ta ji karar unkurin aman da yake daga bandakin dake bude, tsantsar soyayya da kulawa irin na uwa sai ta karasa gurin da sauri hankalinta a tashe. Da gaske baka da lafiya ashe Ta taba wuyansa zuwa kansa ta ji shi da zafi sosai, da kanta ta kunna lap ta wanke masa baki kamar wani karamin yaro. Mu je asibiti yanzu Zan iya kira likita ya zo gida ya duba ni Aa asibiti zamu tafi Ta cikin tsananin razani da tsoron kar wani abu ya samu danta. Sakinsa ta yi ta fice daga bandaki da sauri. Tawul ya dauka ya goge fuskarsa idonsa har wani ja suka yi alamar jikinsa ya saki saboda Fever, haka ya fito bandakin yana jin aman kamar be gama yi ba, kofar bandakin ya rike yana jin yawun bakinsa na tsinkewa. Sai ga Ammy ta shigo tare da Momy Ikilima Mu tafi ga direba can a waje Ammy ba wani ciwo ba ne da zaka daga hankalinki ba Ban taba baka umarni ka aikata a take ba tare da ka yi min musu ba, haka last time na ce maka zamu tafi England a duba lafiyarka baka yarda Ammy kamar zata fashe da kuka take maganar. Ganin haka ya saka shi nufar gurin da ya aje wayarsa ya nufi wayar ya dauka. Mu tafi Gaba ta saka shi, kamar wanda zai gudu sannan ta bi bayansa ita da kanwar mijin nata. Zan iya tuki ba ni key Ya mikama Direban hannu, direban ya kalli Ammy. Sai ta girgiza masa kai. Ka bari ya kai mu ina zaka iya tuki yadda jikinka yake da zafi nan Ammy ciwon nan be kai yadda kike tunani ba, zan iya tukin nan da kaina Ya rufe baki yana karkata dubansa ga motar Salim da ya faka kusa da wata motar gidan. Captain ya bude motar zai shiga Salim yayi hanzarin bude tasa motar ya fito. Captain... Be amsa shi ba kuma be fasa shiga motar ba. Ammy ta kalli Salim din ta kalli anta. Salim ne Na san shi ne Ammy mu tafi Salim na isowa gurin ya gaishe da Ammy da yar kunyarsa kunshe a aljihu. Lafiya Kalau Salim Fita zaku yi? Eh Captain za mu kai asibiti Ba shi da lafiya ne? Salim ya kalli Captain din da baya son kallon gurin da Salim din yake tsaye ya mika masa hannu. Captain ya kalli hannunsa ya kalli fuskarsa, sai ya amsa masa ba tare da ya mika masa hannun ba. Come on mu bar abun da ya faru ya wuce mana, ba yara ba ne mu, mun samu rashin fahimta kuma mun hau dokin zuciya, amman ba zan bari wannan abun ya lalata alakarmu ba, we're friends for more than 15yrs now wannan dan karamin abun ba zai bata alakarmu ba, na san na yi ba daidai ba a wani gurin kai ma kuma ka zafafa I'm sorry Salim ya sake mika masa hannunsa a karo na biyu, sai dai wannan karon na neman kawarda fadan dake tsakaninsu ne, ba irin na dazun ba da yake na gaisuwa. Wannan karon ma sai da Captain ya dade yana kallonsa hannunsa sannan ya mika masa nashi hannun ba tare da yace komai ba. Ammy ta yi murmushi. Ko ku fa, amman ace mace zata shiga tsakaninku kamar ba maza ba? Ban jidadin abun da ya faru ba kuma daman ina da kudirin na shirya tsakaninku Still Captain be ce komai ba, Ammy ta bude baya ta shiga tare da Momy Ikilima dake yaba yadda Salim ya fi karfin shaidan ya kawar da girma kai ya kawo kansa. Direban ya ja motarsu zuwa asibiti Salim kuma ya shiga motarsa ya bi bayansu. Sai da aka fara diban jininsa aka auna bayan likitan yayi masa tambayoyi sannan ya ba shi gado domin har yanzu akwai gajiya a tare da shi kuma yanayin jikinsa ya tsananta sosai. A take aka saka masa drip Ammy ta tare a dakin tareda Salim hankalinta a tashe ta fita dakin tana sanar da Daddy. Momy Ikilima kuma ta koma gida dare da direba domin sanar musu halin da ake ciki da kuma dauko wasu abubuwa da ake bukata. Sai dakin ya zama daga Salim sai Captain da idonsa yake rufe hannunsa kuma yake sanye da cannula. I'm so sorry akan abun da ya faru, gaskiya ta bayyana yanzu kuma za a yadawa duniya cewar Hurriya bata aikata ba Matsalata da kai ba akan Hurriya ta aikata ko bata aikata ba ne, so please sunanta ya fita daga bakinka, matsalar sa muka samu saboda na karya hannun Adam ne so mu yi magana akan haka kawai Salim yayi ya dan tabe baki. That's right... Adam yayi abun da kake bukata an turawa mahaifinka video kai ma kuma na turo maka ka duba whatsapp dinka Captain ya bude idonsa ya kai hannunsa na hagu ya ciro wayarsa ya bude whatsapp dinsa, suna ganin Salim ya fara budewa kamin ya sauke video kiran Daddy ya shigo wayarsa ta whatsapp video. Daddy Hi Jamal... Yanzu Ammynka take fada an baka gado a asibiti, haka ne... Eh amman da sauki ba yadda take daga hankalinta ba ne... Salim ya juya ya fice daga dakin, yana rufe kofar dakin Ammy na kawowa bakin kofar dakin, ganin Salim sai ta fasa shiga ciki. Ina son magana da kai Salim Okay Ammy, zamu iya yi a nan ko sai mun tsada Idan muka matsa zai fi Ya fara takawa ita ma ta taka sai suka jera suna tafiya. Amman ina son na sake yaba maka ne akan kokarin da ka y na kawar da komai a ranka, kuma ka bawa Captain hakuri duk da kasancewar ta wani bangaren ka fi shi gaskiya, na jidadin haka domin idan baka yi ba na san Captain ba zai taba iya aikata abun da ka aikata ba, ka san halin abokinka Salim yayi murmushi. Nasan halin kayana Ammy ba sai kin fada min ba, shiyasa ai na bada hakurin da kaina, ni kuma na fahimci ban kyauta ba ta wani bangaren and be kamata na bar yarinyar kamar Hurriya ta raba ni da Captain Good na jidadin dawowarka sosai, daman ina neman wanda zai taya ni fadan nan domin ni kadai nake yakin nan a gidana, Engr yana goyon bayan Captain yan'uwansa kuma basa son fada masa gaskiya saboda Engr, yau ma Hajiya Nene fada ta yi min tana ganin kamar kishi nake da yarinyar nan ni kuma ba kishi nake da ita ba i just can't find any reason da zai saka na so ta, i know da cousin dinka aka aikata abun nan amman ko da ba gaskiya ba ne ai wannan abun ba zai shafe a idon duniya ba Ya tsaya daga tafiyar da yake. Why are you telling me this Ammy? Bari na tambaye ka tsakaninka da Allah... Shin zaka iya auren yarinyar nan a lokacin nan? Ba zan iya ba, ko a gaba balle a yanzu na jinjinawa Captain yayi kokari kuma yayi jihadin da ba kowa sai iya ba To me yasa ba zaka taya ni fada masa gaskiya ba? Ka lurar da shi ta wani gurin da kurakurai suke mana Idan na yi hakan zai bata alakarmu da shi ne akwai, ba zai fahimta ba kuma sai yi tunanin na zo ne saboda na daga masa hankali na hana shi zaman lafiya da Hurriya ko sonta yadda ya dace Cikin Hikima zaka yi Salim, wannan taimako a gareni da kuma shi kansa abokinka, Wallahi bana son auren Amman an riga an daura ai Ammy meyasa baki hana ba kamin a daura Babu wanda ya sanar min da cewar za'a daura, mahaifinsa ya shigo gida ne kamar haka ya sanar mana sun je jaje kuma yin nemi aurenta an ba su har an daura, yarinyar da bata gani ma amman idonsa ya rufe ya rantsa sai ya zauna da ita Salim ya sauke ajiyar zuciya ya saka hannayensa aljihu. Yarinyar nan bata cancanci Captain ba ko kadan ko da kuwa bata aikata ba, ya kamata ya lura da yadda duniya take kallonta a yanzu, amman kin san Captain ba a masa daidai, kawai dai mu saka masa ido zai fi Kai ma dai ba zaka iya ba kenan...! Babu wanda yake iya fahimtata Ta cige baki tana kallon wani ward din dake facing dinsu, Salim ma gurin yake kallo sai dai kowa da kalar tunaninsa. After Salim ya fice Captain ya tashi zaune Ina fatan dai ba wata matsala ta ja rashin lafiyarka ba? Aa rashin lafiya ne kawai babu wata matsala Daddy Ma Sha Allah, daman ina da niyar kira na maka albishir sai kuma Ammynka ta sanar da ni ciwonka a take tawun giwa ya take na rakumi Akan Adam ne? Ka ga video ne? Aa zan sauke kenan ka kira ni, amman Salim ya fada min Adam din ya aikata abun da ake bukarta ya aikata Ya aikata yayi kamar yadda muke bukata, mahaifinsa ya turo min da video, domin ya kara kira bayan ya tafi gurin mahaifin yarinyar be yi nasara saboda na yi waya da shi na fada masa duk irin magiyar da za su masa kar ya aminta da su, sai kuma ya dawo ni ma yana rokona sai dai ban bashi wata amsa ba bayan wanda ka bashi, kuma na tabbatar masa a jibi Monday za a shiga kotu, sai gashi yau ya turo min da video Na jidadin hakan Daddy thank you very much, da goyon bayanka ne na samu wannan nasarar, zan yada video, na san hakan zai wanke yarinyar nan ko da ba gaba daya ba, zata yi farinciki idan ta ji i wish ni zan fada sanar mata ma saboda na mata wannan alkawarin Daddy yayi murmushi. Yaron ma abun tausayi, kaddarori ne kawai da rashin tunani irin na yaran yanzu, jiya ma na yi waya da Hajiya nake tambayarta zuwa yaushe ne ya kamata ace Hurriya ta tare saboda damuwa a yanzu matsalar idonta ne, ina son ta dawo karkashin ikonmu ne gaba daya sai a nema mata maganin hakan zai fi armashi da ace tana gidansu
Chapter 130 · 0% Book details