Sashe 40
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... Page 7 Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660 Two days later... Hindu ta ciro gorar ruwa dake cike da rubutu ta aje a gaban Amma. Yace wannan ki sha shi a tsaye kuma ki shafa zaki yi haka har kwana 7, na karya sihiri ne da tsari sosai Amma ta kai hannu ta dauka tana juya rubutun. Rabawa zan yi har bakwai kenan Eh wannan kuma na hayaki ne, wato matar nan ba karamin asiri ta yi miki ba na shiga tsakaninki da Alhaji, kuma yanzu haka tana nan tana shirin yin wani akan Hurriya Shi ma dai tsafin yake kenan? Aa ba tsafi yake ba, kawai dai yana duba ne da kasa, ke ya dubo mana abubuwa da yawa fa, Wallahi ya ce yanzu haka ta yi miki jifa kuma tana daf da samun idan kuma ta same ki rayuwarki zata canja sai kin zama abar tausayi, ya ce idan baki tashi tsaye an yi yanka ba an maida mata da jefarta to zaki koma kwance ne, kuma ya tabbatar min idan aka yi haka ba jefarta ko asirin da ta yi sai ya karye Amma ta aje rubutun da sauri. Subhanallahi, Subhanallahi Hindu kin ji abun da nake gudu, wannan ai shirka ne Wane irin shirka kuma? Ke fa matsala ne da ke, mu da muke neman warware sihiri? Ba fa sheri zamu yi ba warware ne Amma ta girgiza kai. Hmm hmm Hindu ba zan taba komai nasa ba, ba zan iya kauce hanya saboda duniya ba, komai mukaddari ne daga Allah Hindu ta rike baki. Toh ke ma dai ba a banza ta barki ba, wato sai da ta kwantar da ke ta yadda ba zaki iya yin komai ba Ko ma dai minene ni dai ba zan yi yanka ba, ba zan aikata wani abun da zai hana ni kwanciyar kabari lafiya ba, saboda rayuwar duniya mai karewa, ni dai na bar komai ga Allah shi zai isar min, Allah ka isar min ga duk wanda yayi min cuta, ga duk wanda ya hana ni zama da mijina, ga duk wanda ya raba tsakanin Uba da Yarsa, Hindu Wallahi ba zan iya shirka ba, ki yi hakuri dan Allah zan baki kudin da kika kashe Ba sai kin biya ba, ai na san mai kudi kika aura Hajiya Iyami, ni dai ban tafi gurin wani na ce yayi min tsafi ba, kuma dai ina sane ba zan yi shirka ba, amman na miki alkawari daga yau ba zaki sake jin bakina akan neman taimako ba kin yi da yar halak Ta fara tattara kayan tana sakawa a jakar, Amma na kokarin fahimtar da ita amman bata saurareta ba ta fice daga gidan cikin bacin rai. A gurin Amma aikata irin abubuwan nan shirka ne, neman taimakon wani wanda ba Allah ba shirka ne, Hindu kuma tana ganin matukar ba shari suka je nema ba, kuma ba wata ibada suka yi da Allah kadai ake yi ma ba, to ba su aikata shirka ba, fahimta ta sha banban sai aka samu sabanin ra'ayi kowa ya kasa fuskantar inda dan'uwansa ya dosa. Gwaggo ce ta fito daga dakinta ta zauna falon cikin yanayi na rashin jindadin abun da ya faru domin tana jin komai dake faruwa. Ai da baki mata haka ba, da sai ki karba ki aje ba dole sai kin yi amfani ba, kuma abun da be tsabawa addinin ba, ba a hanawa kai aikatawa Iyami, ke kanki kin san ruwa baya tsami banza kuma na tsorata da lamarin matar nan domin bata da imani Gwaggo idan na karba kamar na yarda ne, kuma idan Kaltume bata da imani ta aikata tsafi mu ma sai mu biyeta mu aikata? Saboda namiji? Namijin da ko babu asiri zai iya cewa ya gaji da zama da ni, namijin da zan iya faduwa na mutu yau da dare ya sadu da abokiyar zamana? Ni kam ba zan yarda na zama daya daga cikin matan da Annabi ya ce mafi yawansu suna wuta ba, domin farkon abun da ke shigar da bawa a wuta tsabawa Allah ne da kin bin dokokinsa Duk da haka dai, Iyami ki nemi tsarin jiki kuma ki nemi na karya sihiri ban ce ki yi tsafi ba, amman ki yi tunani Gwaggo ta tashi ta fice daga falon zuwa harabar gida. Amma ta girgiza kai. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, wai duk saboda kishi zai saka Kaltume ta aikata min haka kuma ta aikatawa yarana? Duk saboda namiji? Ka bata lahirarka? Appan Hurriya dama ban aureka ba, ina ma ban je gidan aiki ba Tana maganar hawaye na sauko mata. Ta dora duka hannayenta a kai tana jin kamar ta bude bakinta ta saka kara ba tare da an mata komai ba, gaba daya duniyar ta rikice mata kashe ya hade ta rasa ina zata sa kanta ta ji sanyi ina zata saka rayuwarta ta ji sassauci. (Ni kan na ce anya akwai irin su Iyami kuwa Kuka ta yi sosai har sa da ta gode Allah, sannan ta tashi ta nufi dakin Gwaggo ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta nufi dakinta dake wajen falon, kamin ta karasa ta soma jin gabanta na faduwa irin faduwar da bata saba ji ba. A take ta fara ambaton Allah har ta shiga dakin. Tana taka kafarta sai ta ji kamar ta taka kaya da sauri ta daga kafarta ta duba sai ta ji a dayar da sauri ta koma baya ta fita daga dakin. Ta sake saka kafarta sai ta sake jin kamar tana taka kaya ta sake fita, sai da ta yi haka sau uku har ta juya kamar ta kira Gwaggo sai kuma ta fasa gudun kar ta daga musu hankali. Rukayya Na'am Rukayya ta amsa daga dayan dakin sannan ta fito Gani Dan Allah shiga ki dauko min twins Okay Amma ta juya ta koma dakin Gwaggo ta zauna, a dakin Rukayya ta kawo mata su, ta shimfida su a saman gadon Gwaggo, Amma ta dauki Hamid ta bashi nono sai da ya koshi sannan ta bawa Hamad shi ma, ta kwantar da su ta kwanta gefensu ta kai hannu ta shafa Hamad tana murmushi sai hawaye suka zubo mata. A ranar Amma ta kwana cikin tunani kala kala. Misalin karfe uku na dare ta ji kamar an tashe ta sai ta bude ido, ga mamakinta arba ta yi da rana ta haska sosai kamar karfe biyun rana. Da sauri ta sauko saman gadon tana mamakin wane irin bachi ta yi haka bata farka ba har rana, kuma wani be tashe ta ba. Gwaggo Gwaggo Gwaggo Ta shiga tashin Gwaggo. Gwaggo ta tashi zaune tana murza ido. Lafiya Iyami? Gwaggo rana ta yi kalle fa Gwaggo ta juya ta kalli dakin har zuwa windows ita dai dare take gani, Gwaggo ta tashi ta nufi makunnin wutar dakin ta kunna, sai haske ya baibaiye dakin, a take ranar ta bace a idon Amma. Karfe ukun dare ne fa yanzu Iyami, lafiya kike kuwa? Gwaggo ta fada bayan ta duba agogo falon. Sai dai Amma bata ji da ganin komai sai muryar mutum hudu da fuska daya, mace ce mai manyan idonawa kamar girman kwai, ga bakin gashi da aka birkita ya yamutse, da bakin tufafi, wannan na nuna mata Yamma tana cewa ki bi nan. Wannan na nuna mata gabas tana cewa ki bi nan, wannan na nuna arewa dayar na nuna kudu, kowa kuma cewa yake ki bi nan bi nan. Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Shi ne abun da ta yi ta maimaitawa ta sai dayar dake hadu ta miko hannu ta buge mata baki. Amma ta yi baya ta fada kan twins dinta har sai da Gwaggo ta dagota daker ta janye yaran sannan ta fara tofa mata addu'a, kamin ta fita ta kira Bappa da Rukayya. Haka suka zo suka rufe tana suna ta tofa mata addu'a sannan Rukayya ta dauko alkur'ane ta fara karanta mata, daman daga iya sai Iyamin ne suka yi sauka, Rukayya sai ta maida hankalinta bangaren boko bayan saukar Iyami kuma bata cigaba ba bayan Primary domin a lokacin babu hali, sai kawai ta saka ga aiki a gaba da kuma karatun addini. Har safe Iyami bata motsa ba har lokacin kuma idonta a rufe yake. Gwaggo ce ta fara bada shawarar a nemi masu maganin hausa, Bappa kuma ya karkata bangaren Asibiti. Wane irin asibiti kuma rana fa ta fara gani kamin komai ya faru kuma na fada maka, karfe uku na dare amman tana ce min rana ta yi Toh tun da kun fi sha'awar na hausar sai ayi, amman dai da mun fara kaita asibiti, wata kila ma damuwa ce ta yi mata yawa damuwa babu abun da bata sakawa Shi ke nan Malam mu tafi asibitin Ba dan ranta ya so ba aka dauki Amma zuwa asibiti, suna zuwa kuwa aka bata gado likitoci suka hau dubawa. It take them a week ba su gano komai dake damunta ba, daga lokacin aka dawo gida aka fara yin na hausa shiga nan fita nan babu wani canji ko'ina kuma da abun da ake fada, wasu su ce kishiya ce wasu su ce karo ta yi wasu kuma su ce gidan ke da aljannu. Kowa da abun da yake fada, withing 5 Months Amma ta zama abar tausayi domin bata iya komai sai an mata a kwantar a tayar bakinta kuma bata iya cewa komai sai dai ta yi ta kallon mutane