Sashe 69
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai na yafe miki, ni dai ina neman mafita ne acikin lamarin nan, domin Hurriya ba ni kadai ta sako a gaba ba har da ke.. Da kuma mahaifinta, wata kila nan gaba kadan idan tana zaune a gidan Hajiya zata iya sakawa ta tsine mana gaba daya, ko kuma ta cilastawa Alhaji rabuwa da mu Appa yayi karaf ya ce. Aa Hajiya ai tana da hankali da tunani, ba zata yi haka ba Baka da tabbaci kai kanka idan aka fada maka Hurriya zata aikata abun da zai saka ka koreta a gidan nan zaka yarda? Amman da yake butuluce kamar uwarta ai gashi nan ta je ta zage ka a wani gurin ta saka makota suna maka kallon azzalumi, nan gaba kadan kuma baka san abun da zai biyo daga gurin Hajiya ba, kasan dai yadda take son Hurriya take daukar shawararta Sai a lokacin Momy ta kai zaune, bayan Hajiya Kaltume ta gama rattaba bayannanta. Ni abun da nake gani kawai ka yi hakuri ka dawo da ita gidan nan, idan ba haka ba ma zata iya lalacewa Momy ta dubi Hajiya Kaltume ta ce. To miye amfanin korarta da Alhaji yayi? Ai sai ta dawo ta cigaba daga inda ta tsaya tana hada mutane To ai mun san halinta yanzu, ko da ta fada ba zamu yarda kuma dole a ja mata kunne To sai dai idan bangarenki zata zauna, ni dai na gaji da zamanta a gurina, balle kuma yanzu Aa ni da take kallon a matsayin makiyiyarta, ta ina ma zata yarda ta zauna a gurina Appa ya gyara zama ya kallesu one after the other ya ce Kar wanda ya sake bani shawara ko zabin gurin da Hurriya zata zauna, idan har zan dawo da ita cikin gidan nan a inda nake son ta zauna zata zauna, daga gidan har ku da yayanku a karkashin ikona kuke, musamman ke Nafisa na lura da bakinki ba shi da linzami akan irin wannan maganar, kai tsaye kike furtawa, na yi miki kashedi amman baki ji ba, wata kila sai kin ga zahiri... Da mamaki Momy ta kalleshi bakinta a sake ta ce. Allah da iko yake, in ba dan ana son a maida laifi gareni ni da aka raina ba, ai Kaltume ma ta yi maganar ba zata zauna a bangarenta ba, amman sai ni kake yi ma radda wato ga ni itace mai dadin hawa, to Allah ya baka hakuri ta zo ta zauna, daman korar ai ba ta Allah da Annabi ba ce, tun da ga shi har kuna son a dawo da ita Appa ya dakawa Momy tsawa domin ita kadai ce yake yi ma fada a yanzu, Hajiya Kaltume kuma an saka masa tsoronta ko da ta yi ba daidai ba ba zai iya magana ba, and ba zai iya bijirewa umarninta ba. Nafisa... Akan yayana zaki iya janyo wa kanki masifar da zata daukeki daga gidana, bana son ana aibanta min yaya dukansu, ki sani Hurriya ko kisan kai ta aikata Hurriya Haruna Mai Yadi haka za a kirata babu wanda ya isa ya kankare wannan, kin fara kai min hanci kuma ina daf da fyatoki, idan baki rike rike girmaki ba, baki dauke idonki akan Yayana ba za ki sha mamaki Hajiya Kaltume dake murmushi cikin rai, ta kalli Appa da ciki wani yanayi dake nuna da gaske take yi ta ce Haba Alhaji yanzu saboda Hurriya sai ka ce zaka fadi wani abu marar dadi akan Nafisa, adai yi hakuri shekara nawa ana tare, yanzu ga yaya sun girma ana zancen aure kuma zaka bari shaidan yayi tasiri akanka? Kara dai ayi hakuri duniyar ma duka duka nawa take? Ni ko Iyami ban jidadin rabuwa da ita ba, tun da ga yaya biyu ko da yake yanzu Hurriya ce kadai ta rage, amman dai ba dadi ai, da yanzu tana nan da duk ba zamu samu wannan tsabanin ba, tun da yarta taba hannunta Cikin fushi Appa ya ce Ko yanzu ai zan iya kai mata ita, ba dole sai ta zauna nan gidan ba Aa kara dai ta dawo nan din, can ga uwa tana jinya abun ai sai ya taru ya zama biyu, wahalar ta yi musu yawa, kana ganin wannan halin da hurriya ta fara idan ba a nan take ba ai kara baci zata yi, ni da kaina zan shirya mu tafi tare a daukota daga gidan Hajiya, ko yanzu ai ta horu Momy dai bata sake cewa komai ba, domin bata son Appa ya sake furta mata wata maganar marar dadi a gaban Hajiya Kaltume. Ni zan tafi bangarena sai da safe... Appa ya mike tsaye ya nufi dakinsa, kama yadda Hajiya Kaltume ma ta fice daga falon bayan ta yi musu sallama. Duk wani damuwa da tunanin tonuwar asirinta ya gushe a zuciyarta saboda farincikin ganin fadan Appa da Momy. Da murmushi ta shigo bangarenta tana maida kofar dakin ta rufe Kulu ta mike tsaye hannunta biyu a hade tana murzawa. Hajiya an fito, na ga ita ma Momyn ta fita shiyasa na zo da sauri, sai kuma aka ce min kin shiga bangaren Alhaji shi ne na ce bari na jiraki Hajiya Kaltume ta dan yamutsa fuska yayinda ta kawo gurin da Kulu take tsaye da daurin zanenta irin na masu siyar da ganye. Zuwanki ai ba shi da wani amfani kulu, kullum babu wani abun da kike kawo wa, tun lokacin da na saka binciken dakin Hurriya baki kawo min komai ba Kulu ta shiga rantsuwa. Wallahi Hajiya na bincike dakin Hurriya kaf har kayanta sai da na duba amman ban samu komai ba, kin ga kuma dole na fada miki gaskiya ba zan miki karya ba To yanzu me ya kawo ki? Dazun ne ina cikin Kitchen ina wanke kayan da suka ci abinci, kin san Momy bata son a bar kaya ya kwana ba a wanke ba, to ina cikin wankewa sai ga wani bakon Momyn ya shigo, yana ta masifar wai an kori Hurriya Momy bata yi komai ba, har umarni yake bata wai ta dawo da ita, ita kanta Namra da ta saka baki a maganar sai da yayi kamar zai mareta To waye shi? Ina tunanin dan yayanta domin can da yana zuwa gidan sosai kuma danta take kiransa tana nuna masa so sosai, haka suke ce masa kefin Miye alakarsa da Hurriya? Toh nima shi ne ya ba ni mamaki ai, na ce ko sonta yake yi, ya ma daina zuwa an fi shekara uku yanzu sai yanzu ya dawo, amman ita ma kanta Momy da Namra ina jin suna tsinewa Hurriyar suna cewa bata da albarka Ai dole, tun da ta fara hada munafurci, amman duk da haka ni da kaina zan tafi na dawo da ita gobe, sai na nuna mata hankalin Babba dabam dana yaro, kuma idan za a asake korarta sai daia yi nata korar da zata tafi nesa da garin nan gaba daya, ba wai ta tsaya a kusa da Hajiya ta hada mu ko kuma Appanta ba Shi ke nan Hajiya, daman na ce bari na fada miki ne abun da na ji Kin kyauta kuma ina son cigaba da abun da kike yi, da zarar kin ji kyas ki zo ki fada min, tun daga kan Hurriya har Nafisa da kasuwancinta Toh Hajiya na gode mu kwana lafiya Hajiya Kaltume ta daga mata kai, sannan ta bita da kallo tana tauna maganar da ta fada mata a ranta. Waye yaje yana masifar a dawo da Hurriya? Sonta yake ko kuma me? Waya sani ma ko kanta take bashi ko yake neman samu saboda ta zama marar aji yanzu, tun da uwarta ta bar gidan, kuma gashi har wani dan iskan ma Adam ya ce yana sonta. Hajiya... Ta juyo ta kalli Yasir dake saukowa yana sanye da jallabiyar da ya siye a Khadeeja Candy Store, sai shinning take kamar an zuba mata mai. Yasir ka dawo? Eh, na shigo ai baki dakinki Khairy tace kin tafi bangaren Appa Eh na je na yi magana da shi ne akan Hurriya, kasan kai baka son laifinta shiyasa ban fada maka abun da ta yi ba Kararta kika kai gurin Appa kuma? Haba Hajiya? Duk bayan wannan abun? Aa ba kararta na kai ba, sako Hajiya ta aiko mana wai muna takurawa Hurriya magana dai babu dadi ji, ni kuma na je na samu Appanku na bashi shawarar dawowa da Hurriya a gidan nan zai fi, ka ga mun guje bacin ran Hajiya kuma mun shirya ta da mahaifinta Yasir yayi murmushi dake fitowa har daga zuciyarsa. Haka na ke son ki zama Hajiya, kuma na ji dadin haka Allah ya saka miki da alheri Amin Ta kalleshi sama da kasa. Yau ka dawo da wuri baka tafi gurin hirar ba ne Ya dan yi murmushin kunya ya shafa kansa, tare da cira kafa ya nufi dinning, Hajiya ta bishi da kallo na kauna da alfahari. Wai ni kam wace yarinya ce wannan mai tsada, har yau baka kawo min ita mun gaisa ba, kamar fa baka daukar komai naka da muhimmanci, ni bana son Miwan da Musib su rigaka aure, ka san kuwa suna dawowa kasar nan babu abun da za su yi sai aure Kai ya rankwafar alamar damuwa kadan na bayyana a fuskarsa. Hajiya, su dabam ni dabam idan ma sun riga ni aure miye a ciki? Komai fa lokaci ne, ni ma kuma yanzu yarinyar da nake jira ta kare karatu kuma ina son na maida hankali gurin gini na da hada kayan lefe, sai dai ni da ita muna tsoron yadda iyayenmu za su karbi abun ne, musamman ma ta bangaren iyayenta Hajiya ta Kaltume ta nufi gurin da yake Miye abun tsoro, ka tafi kanka tsaye ka fada musu waye ubanka a garin nan, dole a karba maka uwarka ma nan gaba kadan za a fara sakawa da ita cikin manya mata yan kasuwa na garin nan ko ma na ce na arewa gaba daya Ta karasa yayinda ta dora hannunta a kan kujerar da yake zaune. Juyowa yayi ya kalleta da murmushi a fuskarsa. Kasuwanci zaki fara Hajiya Sosai kuwa, ina son na bude shagunan tufafi masu kyau da tsada, kuma zan bude