Sashe 25
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai ka dauki motata ku tafi da ita, idan an gyara wannan Musib zai kai maka ita gida Jameel ya juyo ya nufo hanyar falon, sai duk suka dugunzuma suka biyo bayansa, ban da Hajiya Turai da bata matsa daga inda take tsaye ba tun bayan da suka fito daga falon. Cikin natsuwa da kamala ya shiga falon, sai ka rantse ba shi ne ya gama bacin rai a waje ba, zaunawa yayi ya hade hannayensa ya sadda kai kasa ya rufe ido yana motsa bakinsa a hankali, kokari yake na ganin be bar bacin ransa ya ninku a zuciyarsa ba... [10/20, 6:25 PM] Nana 1: ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy Namra ta dago ta dubi kofar shigowa falon tana amsa sallama, sai ta mike tsaye da sauri tana kallon Captain da mamaki, zuwansa a yanzu ya bata mamaki tsabanin baya da bata mamakin zuwansa domin ya saba zuwa gidan a duk lokacin aiki ya kawo shi ko ziya, tana mamakin zuwansa ne kasa da wata uku da faruwar abun da ya fusata shi, wato fasa masa tayun mota da Hamad yayi suke zaton Hajiya Kaltume ce ta saka aka aikata haka. Ba kasafai yake sake zuwa gurin da aka bata masa rai ba, idan ma zai sake komawa a gurin sai ya dauki lokaci mai tsawo har an manta da shi yake sake zuwa, wannan ya saka duk wani makusancinsa da yake son alaka da shi ta daure ko da iyayensa yake kokarin kiyaye duk wani abu da zai batawa dan gatan Ammy kuma a daya tilo ga Alhaji Aliyu Turaki. Wata kila haduwar jinin da Allah ya saka tsakanin Momy da an Yayanta ya wuce yayi mata haka. Fuska ba yabo ba fallasa ya shigo falon hannayensa duka biyu suna bayansa. Sannu da zuwa Ya... Captain Tunawa da ta yi baya son ace masa Yaya ya saka ta kasa karasa sai ta kiranshi da sunan da kowa yake kiransa. Yauwa hutawa kike? Eh bari na kira Momy tana ciki Tana juyawa ya dakatar da ita. No Wait... Ina yarinyar nan take Namra? Ta juyo tana wara alamar bata fahimce wadda yake tambaya ba. Wata fara haka mai dan tsayi marar jiki, mai saka glasses Oh Hurriya, tana bangaren Hajiya a kirata Ya daga mata kai, sai ta aje remote din hannunta ta nufi kofar fitar ta fice da sauri, da mamaki da tunanin dalilin kiran Hurriya ta isa bangaren Hajiya Kaltume, sai ta ci karo da Hurriya tana rike da tiyo tana watsawa motar Yasir ruwa, Hamad kuma na ta kada kumfa. Hurriya Uhmm Ta juyo ta kalleta. Wai ki zo ana kiranki Captain... Waye Captain...? Ina wani wadda na ganku tsaye a bakin kofar Momy har na dauko miki glashinki da ya fashe? Kin tuna Hurriya ta yi shiru ta dan bata fuska, kuma ta kasa amsawa Namra da ta tuna ko ba ta tuna ba. Wanda ya mareki? Hamad ya tambaya, Hurriya ta daga masa kai Namra ta zaro ido domin bata saka ran marinta yayi ba, ta san dai akwai abun da yake faruwa. Au daman marinki yayi? Ikon Allah me kika masa? Wucewa na zo yi ban gani ba muka yi karo shi ne ya mare ni har gilashina ya fashe Ni kuma na fasa masa tayun mota duk biyu da wuka Namra ta rufe baki with mamaki. Hurriya ma masa kallon rashin jindadi fadar da yayi a yanzu. Daman kai ka fasa tayun nan? An kusan yaki a gidan nan fa saboda an fasa tayun Captain, Allah ya tsare ka Momy bata sani ba, da sai ka zama abun tausayi Ni ina ruwana Ya fada yana turo baki. Captain akwai zafin zuciya ko shi zai iya maka hukunci babu ruwansa da alakarka a gidan nan, to yanzu dai shi ya ce a kiraki Hurriya ta ake tiyon kasa ta nufi fanfon ta kashe sannan ta bi bayan Namra, Hamad kuma ya cire hannayensa daga cikin kumfan da yake kadawa ya bi bayan Hurriya. Ita dai bata san ta masa laifi a yanzu ba balle ta yi zaton mari ne ko cin mutumci, sai idan kuma cewa za'ayi ta haifar masa da ciwon kirji saboda kanta ya bugi kirjinsa. Namra ce ta fara shiga sannan Hurriya sai kuma Hamad dake bayanta. Yana tsaye a gurin da Namra ta barshi sai dai wannan karon gefen kujerar da Namra ta tashi yake kallo ma'ana kofar falon ta koma gefensa na dama sabanin dazun da ya bata baya. Gata nan Namra ta fada, sannan ta zauna Hurriya ta karaso inda yake ta tsaya gabansa ta kalleshi sau daya ta sauke kai kasa, Hamad kuma yake tsaye kusa da kofar falon yana kallon ya ga abun da za'ayi ma yar'uwarsa. Captain ya maido ta hannayensa gaba ya mika mata box din da ke hannunsa da hannunsa na dama ba tare da ya ce komai ba. Ko be fada mata ba, ta san box din glasse ne domin shi dabam yake ta ka ganshi kana ganewa balle kuma ita da take 5&6 da glass. A hankali ta dago ta kalli fuskarsa bayan ta kalli gilashin sannan ta kalli Hamad ya watsa mata harara duk ya bi ya bata rai, domin har yanzu haushi Captain din yake ba shi, daman kuma shi be iya tsana ba idan ya tsane ka sai Allah ke kasa ku sake shiri da shi. Captain ya karkarata da kansa kadan ya kalli Hamad da sai a lokacin da ya san da shi tsaye a gurin sai kuma ya kalli Hurriya. Ita ma ta kalleshi ta dauke kai ta nufi kofar fita daga falon ba tare da ta ce masa Komai ba balle kuma har ta karba, sai da ta fara ficewa sannan Hamad ya bi bayanta yaja kofar falon ya rufe. Captain ya matse box din gilashin dake hannunsa da mugun karfi ya daga kansa sama ya rufe ido. Allah ya sassauta min kar na kashe yarinyar nan.... Tab ka kasheta Wallahi kai ma sai an kashe ta dan gata be fi gata ba, ita ma yar gatan banbanta ce Namra ta fada a ranta a fili kuma sai ta ce. Glasse ne? Ya sauke kan ya kalleta. Wuka ce Gilashin da Appa yake siya mata mai kyau ne daga waje ake kawo mata Ta fada a zahiri a badini kuma sai ta ce. Captain dai kamar ka fi kowa iya bakar magana Kamar ta san zai kara mata. Wannan a bula na dauko shi Tambaya ce kawai, daman ai na san Hamad ba zai bari ta karba ba, amman ka ba ni zan bata hakuri sai na bata daga baya Ya kai dayan hannunsa yana zagayen gilashin da shi. Waye Hamad? Kanenta ne wanda ka ga ya tsaya jikin kofa har ta kalleshi, shi ne ya fasa maka tayun mota saboda ka mareta, ni ma ban sani ba sai yanzu yake fada Murmushi yayi mai sauti, ya dago ya kalleta ya sake yin murmushi mai cike da mamaki. Wow... Nice... Haka ya kamata dan'uwa ya zama, mai kokarin kare yan'uwansa i like him Ya fada after yayi taking few seconds yana kallon wani bangare na falon, because he know yayi missing wani part na shi da be taba samu ba, wato yan'uwa da suka hada uwa ko uba ko ma uwa da uban gaba daya. Amman haka ba zai hana a hukunta shi ba, they have to pay for what they did Ya juya ya fice daga falon ba tare da ya nemi a kira masa Momy ba, daman kuma ba dan ita ya zo ba wannan karon, ya zo ne domin baya Hurriya gilashin da ya siyo Saudiya saboda ya fasa nata, and that slap da yayi mata ya tsaya masa after ya bar gidan saboda lura da yayi da bata gani sai da gilashin kamar yadda Namra ta tabbatar masa tun a wacan ranar. Namra ta san me yake nufi they instead of he, wato Hurriya saboda ta ki karbar gilashin Hamad kuma saboda ya fasa masa tayun mota. Sai da ta leka ta ga tashin motarsa sannan ta saki curtains din tana fadin. Ban da kai Captain ana kyauta dole ne, ko ni ce ai ba zan karba ba, ka yi zafin hannu ba wani uzuri da an maka abu sai zafin zuciya Ta nufi upstairs, sai da ta fara leka dakin Momy ta ga har lokacin bachi take sai ta ja mata kofar a hankali ta nufi dakinta. HAJIYA KALTUME POV. Yanzu kina da number Salame? Eh ina da ita, ai ko shekaran jiya ta zo gidan nan, har take min zancen Malamin ni dai ban tanka ta ba, domin damuwata ta isheni kar na yi abun kunya Kunya Hajiya fatee? Tofar da yawu, har abada ba zamu taba kunyar duniya ba lahirar ma muna fatan nasara, saka number ki kirata ki ce ta turo miki number Malamin ko kuma idan ta samu lokaci ta shigo sai ku yi magana Hajiya Kaltume na rufe baki Hajja Fatee ta dauki waya ta shiga laleben number Salame. Knocking aka yi har sau biyu sannan Hajiya Fatee ta amsa. Waye? Hajiya Yaron nan ne ya sake dawowa fa, kuma mai Baba mai gadi ya ce yayi yayi da shi amman ya ki tafiya shi sai ya ganki Hajiya Fatee ta hanye wayar ta rafka tagumi. Oh wannan fitinanne yaro ba zai bar ni da abun da ya ishe ni ba Waye haka? Wallahi wani yaro ne na dauka aikin ba fulawa ruwa, ashe barawo, ni ban sani ba, irin yaran nan yan sare sare, wata rana suka zo nemansa har da fasa mana gida aka ayi, tun daga lokacin sai na sallame shi, amman yaron nan ya ki ya rabu da ni, duk lokacin da wani abun ya same shi sai ya zo ya fada ko mai dadi ko marar dadi, ko kuma ya ce ya zo gaishe ni, yanzu ya bi ya fitine ni yau sati biyu kullum sai ya zo wai mahaifiyarsa bata da lafiya ni yake son gani Ikon Allah toh ke Hajiya irin wadannan yaran ai suna da amfani wata rana Hmmm baki san yadda suke fitinar mutum ba ne, ga su da shegen na ci idan sun ga samu Bari na yi magana da shi,