Sashe 127
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya ma sunan addu'ar nan da ake idan za a bar gida, wanda aka ce idan ka karanta babu abun da zai same ka har ka je ka dawo? Hajiya Fatee ta yi shiru alamar nazari tana kokarin tunanin addu'ar amman ta kasa. Akwai dai Bismillah a ciki, Bismilah da wani abu a ciki ni ma fa na manta addu'a Kin ga da kin rike ai da mun karanta yanzu, mu tafi cikin kwanciyar hankali Duk abun da za'ayi fa ba zan samu kwanciyar hankali ba, domin ba mu da shi a yanzu, tafiyar nan dai ta zame mana dole ne kawai, domin ni ma ina son na san lafiyar Malam To kin gani, dole a haka zamu daure mu tafi, Allah dai ya kaimu lafiya, amman tashin hankali da nake ciki a yanzu ai ya fi na yan kidnapping Babu wanda ya di wani, fatan dai Allah ya kaimu lafiya Cikin tsoro suka shiga motar ta suka dauki shatarta tun daga tasha direban ya zo gidan Hajiya Fatee ya dauke su. Hajiya Fatee ce mai rike carbi tana ja tana leka lake waje, Hajiya Kaltume kuma shiru take sai da suka iss cikin garin sannan hankalinsu ya kwananta Hajiya Fatee ce ta yi ta nuna ma direban hanyar gidan Malam be sauke su ko'ina ba sai a kofar gidan da yayi baki kirin har wani bangare na ginin ya zube. Hajiya Kaltume ta kalli kawarta. Anya akwai lafiya a gidan nan kuwa? Ina lafiya kina kallon gida kamar an yi gobara Ni ma abun da ya daure min kai kenan, amman dai bari mu shiga cikin gidan mu ji Hajiya Kaltume ta zagoyo ta gefen da Hajiya Fatee take suka jera suka nufi gidan da kusan ma za'a iya cewa ya zama kango. Ke yaushe rabonki da nan? Wai ni? Ai tun zuwan da muka yi tare da ke van sake zuwa ba, to me zai kawo ni irin wannan gurin ma sai dole Yanzu wai da gaske kike filaye da gonakin da kika ce mutumen nan ya siya miki duk baki ga ko daya ba? Ai yarda ce ta kawo haka, ni na yarda da ko ban zo na duba ba na san ba zai cuceni ba A bakin kofar gidan da aka zagaye da aya suka tsaya suna kallon yadda gaba daya gidan yake kone kuma babu alamar ana rayuwa a cikinsa. Hajiya wannan gidan da kike gani gobara aka yi, kuma kina kallon gidan ya zan kango babu kowa a ciki Amman Hajiya Fatee ni da ke a nan muka san matan malam suna rayuwa? Bari mu tambaya, ba mamaki ma ace ya tashi tun da yanzu linkafa ta yi gaba Juyowa suka yi suka fito daga zauren gidan suka yar tafiya sannan suka isa gida daman makotansa suka yi sallama. Hajiya Fatee ta shiga ciki Kaltume kuma ta tsaya daga waje tana waige waige kamar wanda bata yarda da garin ba. Sannu ina kwananku? Sannu dai muna lafiya Alhamdulillah dan Allah Malam muke tambaya ko ya tashi a nan ne shi da Iyalansa? Mun shiga gidan babu kowa a ciki na ga kamar ma ginin ya fadi Ayyah wai Malam? Malam ai yau kwanansa tara da kwanta dama, Malam ai lokaci yayi Hajiya Fatee ta dora hannunta akan tulun kirjinta ido a waje kamar za su yi magana. Malam kike nufin ya rasu? Malam ya rasu lokaci yayi, gobara yayi cikin dare wutar ta ci shi ta cinye yaransa biyu kuma bata bar komai da yake gidan ba, amman sauran yaransa da matansa sun fita da rai suna nan lafiya kalau Hajiya Fatee ta kai zaune tana dafe da kirji. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, na shiga goma na lalace yau kashi na ya bushe, Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Wayyo Allah na ni.... Kuka da ambaton Allah da take ne ya saka Hajiya Kaltume shigowa, sai kuma ta shigo a sa'a, domin ta shigo ne a daidai lokacin da matar take kara radawa Hajiya Fatee cewar. Matansa sunan na yamma da mu kadan, a sabon gidansa suke takaba, ai Malam ya kowa ya ji mutuwarsa duk wanda ya zo nan kuma yake mana Mutuwa? Malam din ne ya Mutu? Hajiya Kaltume ta amsa a razane da karfi tana kallon matar dake rike da tabarya tana surfe. Yau kwana tara kuwa, gobara aka yi a gidan, komai ya kone, zane wannan na daura sai da aka taimakawa matansa da shi a lokacin da lamarin ya faru Shi nan na shiga uku, ni kam ta kare min.... Al'amurra sai kara rinchabe min suke.... Yanzu Malam be tashi tafiya ba sai da wahala ta tunkaro ni gaba da yamma, na shiga uku na lalace Ba ke kika shiga uku ba Kaltume ni na shiga uku, wayyo Allah wayyo ni kaina Sai hakuri haka mutane suke ta kuka idan suka zo, ai mutuwar Malam ta taba kowa musamman customers dinsa Hajiya Kaltume ma ta kai kasa ta zauna kusa da kawarta suna kuka kowa da dalilin kukansa kuma da abun da yake yi ma fargaba. Tun matar na ba su magana har ta gaji ta zuba musu ido, domin ko da matansa ne iyakar kuka da bakinciki da za su yi kenan. Ku yi hakuri bayin Allah mutuwa ai ta gaji haka shiyasa kullum ake son a shirya mata, Salmanu tashi ka kai su gidan matan Malam Ta fadawa babban anta, domin kukan da suke ya fara yi mata yawa har makota na lekowa ta katanga wasu kuma na shigo suna kallonsu. Hajiya Fatee ta mike tsaye rike da jakarka ta tana kuka, taku daya ta yi kamin ta yi na biyu wani hudun zuciya da ido ya rufeta ta saki jakar ta fado kan Hajiya Kaltume da ko alamar tashi bata yi ba, domin jikinta ya mutu kamar an mata allurar kasala. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un idan kika mutar min a yanzu ai sai abun ya taru yayi min yawa ku taimaka min jama'a Matan dake kofar gidan suka karasa shigowa suka rika Hajiya Fatee suka daga ta daga jikin Kaltume, suka shimfidata a kasa wasu suka fara mata fifita matar idan kuma ta tashi da gudunta ta debo ruwa aka kwarawa Hajiya Fatee. Sai gata ta farko tana hakki. Malam ya mutu, Malam me yasa ka mutu a yanzu? Asirin an tonu na shiga uku wayyo Allah, Malam ya mutu ya bar ni da wahala wayyo Allah na.... Wani irin shidewa ta yi luuuuuuu jikinta ya sake saki, har sai da matan suka jin tsoron wannan suman nata na biyu, Hajiya Kaltume kuma tana zaune a gurin ta kasa aikata komai sai kuka take kamar ita kadai ta rasa Malam. Ruwan aka sake zuba mata sannan ta farfado tana kallon matan karkarrar dake juya mata tana jin sannun da suke mata kamar a mafarki, fada mata da matar ta yi cewar Malam ya rasu ma sai ta ji abun shi ma kamar mafarki ne ba gaske ba. Abun da zai fi akaisu gidan Matan Malam ko kuma a kaita asiri Wata daga cikin matan dake rike da ita ta fada, Hajiya Kaltume ta kalleta da jajayen idanuwanta ta ce. Ina ne gidan Daga nan ne yamma kusa da kuka uku, Sslmanu wuce gaba ka kaisu Yaron da aka kira da Salmanu ya dauki tayarsa da karen kada tayar ya wuce gaba yana zumuncin nuna musu hanya, ganin mutanen daga birni suka zo. Ba dan taimakon Allah da rahmarsa ga bayinsa ba da Hajiya Kaltume bata kai kanta gurin motar da suka shigo ba, domin gaba daya kafafuwan rike mata suka yi, Hajiya Fatee kam sai da aka riko aka saka ta motar idonta sai juyawa yake kamar bata san inda take ba. Yaron ne ya wuce gaba da tayarda yana turawa su kuma suna cikin motar zaune a baya, Hajiya Kaltume ce kadai ke iya kuka a yanzu Hajiya Fatee kam kai kawai take juyawa kamar mai kokarin fita daga hayyacinta, direbansu na biye da su har suka isa katon gidan ginar bolu kana ganin gidan da ba'ayi ma filista ba ka san ba duk kauye ba, ko a kauna sai wanda ya tsaya da kafafuwansa. Wai yanzu da gaske Malam ya mutu Hajiya Kaltume? Shikenan Malam yayi tafiyar da babu dawowa? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, shi ke nan ta kare min dari ta hade min da dubu, Wallahi ganin nake kamar ba gaske ko dai mafarki nake Kaltume? Hajiya Kaltume kam kaddara ta riga fata, bata iya cewa Hajiya Fatee komai a yanzu domin ita ma bata da wannan kwarin guiwar. Hajiya Fatee ta unkura zata fita ta kasa saboda jiki yayi nauyi a zaunen da take ma jiri ke debanta yana zubarwa. Dukiyata.... Cikin nan..... Ga Afrah... Indai Malam ya mutu a yanzu Malam be kyau min ba Direban motar ya juyo ya kalli Hajiya Fatee dake sabbatu tana wani mashalo kamar mashayiya. Cikin gidan Hajiya Kaltume ta shiga babu ko sallama sai tafiya take a gajiye, daga a tsakar gidan ta fadi zaune tana kallon matansa dake zaune da kayaransa. Daga tsohon gidanku muke aka fada Malam ya rasu, dan Allah ku ce mana ba gaskiya ba ne Karamar ta sauke kai kasa idonta na cika da kwalla, mai karfin halin ce fa amsawa Hajiya Kaltume. Malam kam rai yayi halinsa ya riga mu gidan gaskiya, sai dai mu bishi da addu'a, ba Malam kadai ba har da yara biyu Hajiya Kaltume ta rushe da kuka tana dora hannu akai tana ihu kamar zata tara musu mutane. Kashi na ya bushe a yau, ashe shiyasa komai yaki daidai, na zuba kudi ina duban Malam yana nan yana aiki ashe Malam yana barzahu, na kira waya shiru ashe babu Malam Matan suka taso suka rika Hajiya Kaltume suna kuka domin ta tsikaro musu bakincikin rasa mijinsu da suka yi. Hakuri suka rika bata sannan suka rikata suka zaunar da ita a ciki barandar gidan (Balcony) dayar ta debo mata fridge ta aje mata sannan ta zauna tana bata labarin abun da ya faru tana kuka. Kin ga gidan nan be dade da gama shi ba, ya saka komai a ciki tv da fridge irin na yan birni ya saka mana, kayan daki ma masu kyau ya zuba mana, na dubu 70k, duk kauyen nan sai labarin gidan nan yake ashe