← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 143

Sashe 84

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta samu ta sake ita ma Ki dai koya mata fitar kike so, shekara nawa tana zaune a gida bata gidan so boring sai a yanzu, ita ma ta fara raina wayon mutane, wata fadawa da zata fita? Ita ai bangaren Momy take laifin ba na Hajiya ba ne Shiyasa kullum Rukayya ke fadar na kula mata da Hurriya, wani lokacin sai a rasa ta ina ma za'a fara controlling dinku Mtscheeeeee Ya karasa yana jan saki, Khairy da Salma suka kalli juna a gurin da Yasir yake ambatar sunan Rukayya. Sai dai babu wanda ta isa tace wani abu domin sun san halin yayan na su. Sai da ya fice sannan ya Khairy ta koma kusa da yar'uwarta suka tasa gulmarsa da na Rukkayya. HURRIYA POV. Ta shiga dakin na Hajiya da Sallama ta zauna a kasa tana gaisheta, Hajiya Kaltume ta amsa irin amsawar nan kamar ta dole fuska babu yabo ba fallasa, idan ta kalli Hurriya wani kololin bakinciki ke taso mata saboda tuna Iyami da take yi. Lafiya Kalau, ya jikin Iyami? Ta ji sauki Ta daure ta kirkiro murmushin ya Maa Shaa Allah, haka ake so ai, Allah ya kara rikawa yanzu tana tafiya ko? Aa bata tafiya Ah ah kuma kika ce ta ji sauki? Hurriya ta yi shiru idonta da kanta a kasa kana ganinta ka ga natsantsiyar yarinya. Tana iya tashi zaune da kanta? Huriyya ta yi shiru na dakiku kamin ta girgiza kai. Ashha dai, Allah yasa jinya ta zama kaffara, ni fa ina son naje na dubata amman ina gudun ka ce na ce, idan kin je dai ki gaisheta Toh Hajiya Hajiya Kaltume ta dauko wayarta ta bude Gallary ta kama hoton wani farin lace ta mikawa Hurriya wayar. Duba ki gani, daman wani Lace ne nake son na siya muku Bata yarda ta karbi wayar ba, a madadin haka ma sai ta bi Hajiya da wani kalami. Aa Hajiya na gode Toh har da kyautar Iyami ta hanaki karba? Aa Hajiya ai Amma bata iya magana, bata ce min kar na ki karbar kyautar kowa ba, ni ce dai ban karba a karan kaina Toh tashi ki kara gaba, daman duk yadda aka muku mutuncin sai kun ce ba ayi ba, an riga an gado bakin hali, daman ni ai ba so na zaku yi har abada Hajiya Kaltume kamar wanda ta zare haka ta rika fadawa Hurriya kalamai marar dadi, Hurriya dai bata dauki ko daya a nan gurin da ta fada mata su a nan ta bar su, ta fice daga dakin. Fitar Hurriya da kamar minti goma Kulu ta shigo dakin ta zube kasa tana dagawa Hajiya hannu kamar wata sarauniya ko matar sarki. Ranki ya dade gani, Khairiya ta fada mjn ina nema ma na fito har na kusa sai na hango ta doso nan tare da Hurriya shiyasa na koma Hajiya Kaltume ta yi kamar bata ji ba ta shiga wani bangaren na wayarta, kamin ta kara wayar a kunnenta. Yasir kana kusa? Yasir ya amsa a dayan bangaren. Eh ina nan waje, muna tare da Kamal ne Asibiti nake son mu tafi idan ka gama Waye ba lafiya Ni ce, amman dai da sauki, ka bari sai ka gama ni ma akwai abun da zan yi yanzu Ta sauke wayar ta kalli Kulu, sai a lokacin take amsa mata maganar da ta yi. Ai kara da kika yi haka, saboda kaucewa ido Duk wani abun da zai saka Momy ta ji ko ta gane akwai alaka a tsakaninmu ina kokarin ganin na gujewa haka Kin kyauta, dabam na ce a kira min ke ne, saboda mu yi wata magana da ke, kamin nan tashi ki tura kofar dakin Kulu ta kike tsaye ta nufi kofa da ta bari a bude ta rufe, sannan ta dawo ta zauna ta natsu sosai tana sauraren matar da ta fi tsoronta a yanzu fiye da uwar dakinta. Aminci ne ya saka na nake tambayarki abu ko na saka ki yi, na san ba dan kin dauki sarka da kudi ba, wata kila ba zamu san juna ba, amman bana son kina kallon wannan a yanzu, ni daman tuni na tattara wannan abun na aje a gefe daya Hajiya ai ba dan karki ce na yi karya ba, nikam da nace satar nan ta zame min alheri domin sanadinta na hadu dake Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya ta marairaice fuska. Kulu ke da yar'uwata duk daya a yanzu, shiyasa har na kira ki nake son na fada miki damuwata, kuma neman samun mafita a gareki Hajiya tafi kanki tsaye, duk wani abun da kike so zan miki shi, yadda kika rufa min ba ni da kamar ke a duniyar nan Dogon numfashi Hajiya Kaltume taja ta sauke sannan ta furta. Kulu ina cikin damuwa da matsala kala kala, amman wanda ta fi min yawa, ita ce ciwon kafar nan dake damuna, yanzu haka kiran da kika ga nayi ma Yasir ita zan kai asibiti, na dade ina ciwon nan amman har yanzu babu sauki babu alamarsa, tun ina barin ciwon a cikina abun ya fara min yawa, to yanzu kuma sai abin da biyo har da mafarkai da ba su dace ba, kuma ciwon nan sai cigaba yake, abun ya ba ni tsoro, ga maganin asibitin nan yi ake amman a banza Kulu ta dukufa a tunani har wani kada ido take tana jinjina kai. Hajiya ba zaki gwada na hausa ba? Ko Allah zai saka a dace? Kamar an yi ma Hajiya Kaltume albishir haka ta ji, saboda Kulu ta sosa mata gurin dake mata kaikaiyi. Shiyasa na kiraki ai, kin san ku ne mutanen kauye, kun fi sanin irin abubuwan nan, wata kila ba zaki rasa sanin masu irin aikin ba Akwai su Hajiya kala kala, akwai wata mai aljannu tana bada taimako sosai, kuma akwai namiji ma yana yi Yauwa namijin dai zai fi, ni ban cika son mata masu aljanu ba, na fi son inda zan tafi a fada min ko minene, jifa ce ko kuma ciwo ne ko iska ne Aiko kina tafi gurin Malam na gangare zai fada miki ko menene, domin shi baya son ma ka fada masa abin da ya kawo ka shi zai baki labarin komai, har abun da baki sani ba, da madubi yake aikinsa yana kallo madubi ya fadi magana ta tabbata, kuma ko minene a take zai rabaki da shi, idan jifa aka yi miki ko turbuda a take ma zai ciro shi Hajiya Kaltume ta dauki filo ta dora a cinyarta ta kwantar da hannayenta akai tana gyada kai. Yauwa irin su nake so masu aiki kamar yankan wuka masu zafi To idan kika kai gareshi magana ta kare, domin shi ko mutum kika ce ya kashe miki zai kashe Irinsa ya dace, kin ga ko minene a take zai fada maka kuma ya karya shi, a ina hake Kulu? A kauye uku yake, dake nan cikin bungu Babu nisa sai dai ban san yanayin hanyar ba? Hanya lafiya kalau take, ai garin mu babu irin bata gari, su kansu suna tsoron mutanen yankin Maa Sha Allahu, sai dai kuma tafiyarmu kamar ba zata yi a tare ba, saboda uwar dakinki Nafisa ba zata bari ba nake gani Wannan ba matsala ba ne Hajiya, kina shiga garin Bungu u ki dauke hanyar kauye uku, da kin isa ki ce gidan Malam Ashiru mai Yasin da Allon karfe kike nema, ko karamin yaron zai kai ki, idan kuma kina jin ba zaki iya haka ba ke nemi gidan su Kulu taroro kina shiga gidan ki ce ni na aiko ki gurin Malam Ashiru za a kai ki, zaki iya ma kira na yi magana da su Allah dai ya saka miki da alheri Kulu, ina ganin ma ba zan tafi asibitin nan ba, gobe ina gama karyawa zan kama hanyar garin, zan iya tafiya da direba na ma ya kai ni garin Daman Hajiya tafiya da daren ba ai ya fi sirrin da sauki Haka zan yi, zan fara zuwa gidan na ku sai na kira na ba su ku gaisa idan ya so sai kun iso gurin Malamin zai fi sauki Toh Hajiya, Allah ya bada lafiya Amin Hajiya Kaltume ta mike tsaye daker tana cige baki kafar kuma kamar zata yi gurmanta da ita haka ta taka ta isa gurin kayanta ta bude wardrobe ta dauko wani lace da ba a dinka ba ta jefawa Kulu. Ahhhhh Kai Hajiya duk ni kadai? Alhamdulillah Hajiya na gode na gode, Allah ya kara rufa asiri ya biya bukata, Allah ya kara lafiya ya tsare ki daga duk wani sheri Amin, wani abun kulu ai sai na samu lafiya ma, da yardar Allah idan bukata ta biya zan kyautata miki, ta shi ki tafi kamin Yasir ya shigo Toh Hajiya, amman zan bar leshin a nan saboda idon mutane, sai idan na ga sarari zan zo na karba Dadina da ke wayo Kulu kin iya sirri Gidan na mu ne Hajiya sai da haka, kamin a fara fadar ana ganina bangarenki Hajiya Kaltume ta yi murmushi. Ita kuma ta mike tsaye ta yi mata sallama. Mu kwana lafiya Kamin ta isa kofar dakin ta bude Yasir ya bude sai dai be shigo ba ya bata hanya ta fita yana amsa gaisuwar da take masa. Me ta zo yi nan? Hajiya ta nuna masa lace din dake kasa Nafisa ta aiko min da lace? Ke kuma? Ya tambaya kamar mai shakku, Hajiya dai bata sake ce masa komai ba ta nufi gurin da ta tashi ta zauna da tafiyar nan nata kamar zata yi dingishi. A kafa kike jin ciwon ne? Eh gurin da na taba jin ciwo kwanan baya, a nan na sake jin ciwo haka nan kawai sai na ji kamar an tureni na fadi kasa Ko santsin gurinki ne ke janki Ya soma duba kafar da ta dan dago masa tana jin kamar ana yanka gurin sai sululi yake mata kamar an watsa ruwan zafi. Aa ba wani tsantsi shekara nawa ina gidan nan da can tsantsin be ja ni ba sai yanzu? Turo ni ake yi fa To wa yake turoki Hajiya Yo ina zan sani tun da abu ne na aljanu,
Chapter 84 · 0% Book details