Sashe 36
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya kin daukar kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660 Hurriya first lost her sight a jikin Gwaggon, before ta yi going blank aka kwasheta ita da Amma sai Asibiti. Amma aka wuce da ita dakin haihuwa Hurriya kuma aka kaita Emergency. After 49hours of labor Amma ta haihu tagwayenta biyu duka maza. A madadin ta yi murnar ta haihu ta samu yan biyu sai murnar ta koma mata ciki saboda tunanin Hamad bata da wani kuka sai na Hamad. The following day aka sallamo ta daga asibitin bayan sun mata dinki kuma sun dorata akan maganin da zata rika sha na hawan jini sannan suka hana ta wankan ruwan zafi domin jinin nata ya hau sosai irin hawan da ba dan Allah ya kawo sauki ba, da abu ne mai wahala ta fita lafiya. Har lokacin Hurriya tana asibitin Hajiya Binta na jinyar tare da taimakon Rukayya, kwananta biyu bata san inda kanta yake ba a asibitin, kamin ta farfado sai kuma ta zama so weak sai da ta sha drip da manyan allurar sannan ta samu sauki, the following day ita ma aka sallame ta two days after an sallami Amma. Wani abun da ya bawa kowa mamaki ciki har da Momy kuma ya daurewa Amma da Hajiya Binta kai shi ne, kin lekawar Alhaji Haruna a asibiti ko gida da sunan duba Amma ko kuma duba yaran da ta haifa masa, yan'uwansa na nesa da na kusa duk sun je duba twins din kuma sun je duba Hurriya wasu ma ba su samu labarin abun da ya faru ba sai a da suka je barkar twins. Sai dai Appa be bar rashin zuwa duba yaran da kowa ke musu lale da zuwa duniya, ya hana shi kyautata musu ba, duk wata hidima ta ya kamata uba yayi ma yayansa Appa yayi tun daga kan tufafin mai jego Amma har na jaririnsa, sai dai Amma bata yi taron suna ba, duk kuwa da kasancewar ba ayi taron gaisuwa a gidanta ba, an yi zaman makoki a gidan Appa kuma an masa sallatul ga'if wato sallar da ake yi ma gawar da bata kusa. Ta ko'ina Appa ya karbi gaisuwar mutane ana ta jajanta masa. All those days, hour's Hurriya a daki take rayuwa, domin bata son ganin kowa, idan zata yi alwala sai ta shiga bathroom ta yi idan ta yi sallah ta kwanta, bata son ayi mata gaisuwar Hamad, bata fitowa idan mutane suka tambayi ina take, idan kuma aka shigo sai ta rufe kunnuwanta bata sauraren kowa, she's the only one da ta kasa yardar Hamad ya mutu, ranar sunan yaran ma sai da ta saka kowa kuka, domin ihu take ta yi me yasa Amma ta sakawa little one din Hamad yayan kuma Hamid. Amma da baki saka Hamad din ba, Wallahi Hamad be mutu ba, karya suke yi Amma dan Allah ki cire, ki saka masa wani sunan ba Hamad ba Tana kuka tana rokon Amma a canjawa jaririn suna, Amma ta aje Little Hamad ta kama Hurriya ta rumgume. Hurriya dole mu karbi wannan gaskiyar, tana da daci amman dole ne mu karbi kaddara, duk yadda kike son Hamad na fi ki sonsa domin ni na yi nakudarsa na haife shi, una jin fiye da yadda kike ji To me yasa kika sama Amma? Why? Why? Amma ta girgita da karfi tana kuka. Saboda ya mutu Hurriya, baki daya Allah ya karba ya bamu biyu ba? Toh sai mu gode masa, yadda ya so haka yake aikatawa, Hamad ya tafi tafiya ta har abada ya kamata ki karbi wannan, wannan shekarar haka ta zo mana Hurriya ta saki jikinta sai ta lankwasa ta yi baya Amma ta sake ta ta fadi kasan carpet din. Ita kam ta kasa yarda dan'uwanta ya tafi ya barta, fadan da suke yawan yi yake damunta a yanzu, why take ramawa idan yayi mata abun? Ko wane motsi yana tuna mata da dan'uwanta ne, bata taba sanin tana kaunarsa ba sai a yanzu da baya kusa da ita, ina ma ita aka dauka ba shi ba haka take yawan ayyana a ranta. Kusan kowa a gidan sai da yayi kuka kuma aka kasa wanda zai rarrasheta sai Yayanta Yasir, domin shi kadai ya fahimci manufarta kuma ya mara mata baya cewar Hamad be mutu ba, domin karbar gaskiyar cewar ya mutum shi ne arya a zuciyarta. **** **** **** **** Hajiya ki yi ha uri dan Allah, bana son ina musa miki akan abubuwa, amman yaran nan da Iyami ta haifa nawa ne, idan ina bu atar ganinsu ba sai na jira wani ya ba ni shawara ba, ayukan ne sun min yawa a yanzu amman da zarar na samu lokaci zan je na duba su, idan suka yi wari ma aka yayensu auko su zan yi na dawo da su gidana domin zuciyata ta fi amintuwa da haka Hajiya Binta ta kalleshi tana mamakin yadda yake ita bude baki ya musa mata a duk lokacin da ta yi masa maganar zuwa duba Twins din da Amma ta haifa. Tsoho me yake damunka? Wani lokaci ne baka da shi akan iyalinka? Hajiya kin san kasuwanci ba daya ba, kuma idan ina son ganin yaran nan ni zan je da kai na, ina cw dai na sauke duk wani hakki na uba? Toh baka bukatar ganinsu kenan? Haka kake nufi? Toh ni da nake bukatar ganinsu zan tafi, ko miye ya rufe maka ido ka kasa taka kafarka gidan Iyami Allah ya yaye maka shi tsoho, yau sati daya da haifa maka yan biyu kyautar Allah amman ka kasa taka kafarka ka duba yayanka A gaishe su, Hajiya zan leko in Shaa Allah, kuma idan kin tafi ki fada mata next week Hurriya zata dawo zan aiko da mota a dauke ta saboda makaranta Yana maganar yana mikewa tsaye abun da be saba yi ba, ko magana Hajiya Binta take masa baya iya daga kai ya kalleta tsabar biyaya amman a yanzu duk ya canja mata, abun da be yi mata da kurciya ba a yanzu da girma ya kama shi yake canjawa. Baki saki Hajiya Binta ta fi danta da kallo har ya fice sannan ta girgiza kai hawaye na cika idonta. Allah ka shirya bawan nan naka, Allah ka karya duk wani abu da aka yi masa Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Ta rafka uban tagumi tana kokarim ganin bata bar hawayenta sun zubo ba, domin ta san illar zubar hawayen uwa ga anta. Appa har ya isa gida bw daina ganin laifin Hajiya ba, ganin yake tana kusa masa cikin al'amurran da be kamata ta saka kanta ba, shi dai aka haifawa yara to damuwa kuma na me tun da har be ce ba yayansa ba ne, kuma yayi musu duk wata hidima da ya dace uba yayi ma ansa. Ba ta inda ya ji sayin kamar ta gurin da Hajiya Kaltume take taba masa ita ma tana dorawa Hajiya Binta laifi, tana bashi gaskiya na kin son zuwan da yake. Gaskiya Hajiya ba a haka, ai sai ta saka maka ido ta gani, ina laifin bayan duk wata hidima, kuma yara idan suka yi wayo ai sai ka dawo da su nan gurin Momy ta cigaba da kula da su, tun da tana da masu aiki ba daya ba za su rika musu komai Ni ma haka na gani, amman ta kasa fahimtata sai laifina take gani, gaba daya ta rufe ni da fada Toh ya ka ayi, sai hakuri ka san bata hada Iyami da kowa ba a gidan nan, duk dai abun da yayi dalili ya raba amman dai Hajiya bata dauki kowa sukarta ba sai Iyami, wai ni yaushe Hurriya zata dawo ne Alhaji Tana maganar ya aje kofin ruwan dake hannunsa ya amsa mata. Next week, na fadawa Hajiya idan ta je ta fadawa Iyami zan aiko da mota a daukota saboda makaranta Hajiya Kaltume ta dan tabe baki tana shafa zanen atamfar dake jikinta. Makaranta ma ai bata jira Alhaji, yanzu kan sai dai a canja mata makaranta a maida ita Government School, ko ba komai ta dan rage kewar Hamad dan na san abun zai yi da damunta, amman idan ta koma wata makarantar sai ta samu sabin kawaye kewar zata dan ragu, kuma ka ga yanzu private school ai duk an yi nisa da karatu sai dai ta Gwafnati ita ce za su karbe ta ko dan lalurarta Appa yayi shiru kamar mai nazari, idea Hajiya Kaltume na cewa a saka ta wata makarantar ta government be masa ba, sai dai ba zai iya nuna mata haka ba. Ko kuma a kaita wata makaranta, amman makaranta government bata cika kyau ba, bayan kuma ga duka yan'uwanta a private suke, kuma kudin biya makaranta ai akwai shi ba babu ba Ba shi zaka duba ba, yadda Hurriya take da kokari a makaranta ko'ina zata iya karantu, kuma zata gane kamar sauran yan'uwanta daman kuma ta fi su basira, ni dai gaskiya shawarar da nake baka Alhaji a kaita government schools kuma bana son ka musa min akan haka, kai fa ka san Hurriya kamar a take a gurina, yadda ba zan so abun da zai cutar da Ruma ko Khairi ba ita ma ba zan so abun da zai cutar da ita ba Shi ke nan, tun da haka kike so, za'ayi, Allah ya tabbatar mana da alheri Fuskar Hajiya Kaltume ta fadada da murmushi. Amin Alhaji na, Allah