← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 143

Sashe 49

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

kamar ta bugu motar dake gabansu sai kuma ta danne zuciyarta. Mai motar nan lafiya yake kuwa? Ko yayi shaye shaye Maybe Namra ta rage gudun motar shi ma sai ya rage, the second thing she did was laugh irin abun yanzu kuma ya zama out of sence. Ta dan gwada kara gudun shi ma sai ya kara, ta sake raguwa sai ya rage. Tana samun sa'a ta yi overtaking ta wuce da gudu, shi ma sai ya danna a guje ya wuce, wannan karon har da Hurriya sai da ta yi dariya, Namra ta sake yin gaba ta wuce shi sai ta sauya hanya, ga mamakinta sai ya biyota a baya ya wuce, daga lokacin ne suka fara tseren gudu ita da shi ba dan sun san waye a motar ba. Ita dai daman gilashin motarta a bude yake daga ita har Hurriya ana kallon yadda suke shakar dariya su ne basa iya ganin wanda ke cikin motar. Da gangan Namra ta sake sauya hanya tana dariya tana kallon nearby mirror bata ga ya biyo ba, sai da suka kusa isa karshen Titi sai gashi ya bullo ta gabansu. Mun shiga uku Hurriya waye mutumen nan? Hurriya dariya kawai take ta kasa cewa komai, domin a gurinta abun is so funny ita bata tsorata kamar yadda Namra ta fara tsorata yanzu ba. Namra ta rage gudun motarta ta sauka gefen titi shi ma sai ya rage gudun ya sauka gefen titi ya faka gabansu. Ki daina dariya what if he want to kidnap us? Ko kuma wannan saurayin ne na dazu? Hurriya ta ji gabanta ya fadi a take ta daina dariyar, A daidai lokacin da aka bude motar wani matashin saurayi ya fito sanye da black T-shirt da wandon soja haka ma kafarsa na sanye da black shoes. Murmushin da suka gani a fuskarsa ne ya dan sanyaya musu zuciya domin alama da yanayin jikinsa be yi kama da masu aikata mummunan aiki ba. Ya iso gurinta ya duko yana kallon fuskokinsu ko wannensu da tsoro a idonsa. Nice race Namra ta dan yi murmushin karfin yana kallonsa, daga fuskarsa har hasken fatarsa be yi kama da dan nigeria ba rigar soja dake jikinsa da kuma wandon. Sai dai kafarta na kan burki jiran kawai take ta ga wani abu ba daidai ba ta taka burkin da karfi. Na zo na bi ku har gida sai kuma na yi gudun kar na tsorata ku Yanzu ma a tsorace muke Yayi murmushi sosai ya shafa kansa. Na gani ai a idon wannan Ya nuna Hurriya. But i like it, tun da kuka fito Mall nake binku shiyasa na so na bi ku har gida in case of na yi mussing race sai na biyo na kwankwasa muku Namra ta yi murmushi, Hurriya kam har lokacin a tsorace take. Hannu ya saka Aljihu ya ciro karamin kati ya aje mata. Here is my cart duk lokacin da kika yi marmarin race just give me a call I'm Salim Sarauta aka Ethiopian nice to meet you All Still idonsa ya kan Hurriya da tsoro ya gama bayyana a fuskarta, ya juya ta nufi gurin motarsa ya shiga ya yi reverse ya hau titi, sai da ya kawo saiti mn gurin da Hurriya take sannan ya danna horn sau biyu. Namra ta danna ta masa sau daya murmushi yayi ya dauke kai yaja motarsa, Namra ta bi motar da kallo ta mirror ta kai hannu ta dauki katin tana dubawa kamin ta kai babban yatsanta ta shafa. It take her some minutes tana kallon katin sannan ta ja motar suka cigaba da tafiya, bata yarda baya binsu ba sai da suka isa ta faka motarta. Yaya Namra na fada miki account din a yanzu Bari sai mun shiga ciki na huta Ta bude motar ta fita tare da ledar da suka yi siyayya, har ta isa bakin kofar falon ta tura ta shiga Namra na zaune a motar bata zare key ba sai kallon katin take, har yanzu zuciyarta bata gama yarda mutumen kwarai ne ko na banza ba, and ta kasa zaba mata tsakanin jefar da katin da kuma barinsa...
Chapter 49 · 0% Book details