← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 143

Sashe 136

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Appa Sannu Sapna surfe kike yi? Ta yi shiru tana kallon kasa, bata son yace bata gode da abun da yake mata ba. Appa abun da kake aiko mana ne baya wadatar da mu, kasan yanzu Iyali sun karu ba kamar da ba, yanzu ba ni kadai nake ba ya kara aure ya aje can gumawa, gashi ba wata sana'a yake a yanzu ba, shagon da yake tsaro mutumen ya rufe shagon, kuma barayi sun hana noma, daman da shi ne muke samu muna karawa, shiyasa nake surfen dab abun da na samu sai na hada da abun da ya ba ni mu ci ni da yara... Appa ya sauke kansa kasa yana jin rashin dadi ta rashin adalci. Me yasa baki fada min ba Sapna? Kina da wani wanda ya fi ni ne? Ta girgiza kai. Ba ni da shi Appa kai ne uwata kai ne ubana ba ni da gata sai na Allah sai kai To me yasa baki fada min ba? Damuwar ta bayyana a fuskar Appa har ta saka idonsa cika da kwalla, irinta ce a fuskar Sapna ita nata kwallar suna zuba. Gani na yi kamar ba a son zuwana gidan, bana jin dadin yadda ake banbanta ni ko dan ni ina kauye su suna birni ban sani ba, kuma idan na bukaci abu wani lokacin har sai na manta kake yi min Appa, duk da haka kana kokari da mu na aiko mana sa abinci duk wata, gashi ni ba ni da halin da zan maka komai, kuma ba ni uwar da zata maka godiya, wani lokacin ina kunyar bijiro maka da bukata nauyin ai sai yayi maka yawa Appa ya dube ta da kyau ya jinjina kai. Gaskiya ne.... Ke din nan ke da Hurriya da Yasir bana da kamar ku a a Allah ya muku albarka... Kuma da tsananin biyaya da tausayi a gareni Amin... Ya amsa tana share hawayenta, Aliyu ya shigo tare da kanensa su shi da a falon suna ta murnar ganin Appa yau a gidansu, daman rabonsa da garin tun kamin a haifi Hamad... Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 49 https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx Appa ya maida ludayin furar ya matsar da shi gefensa ya gyara zamansa yana sauraren Hajiya Binta. Na muku addu'a sosai daga kai har anka, kuma zan cigaba da yi har zuwa ranar da za dawo da yardar Allah Na gode sosai Hajiya, Allah ya karbi ibada yasa ayi Umara karbabbiya Ameen, ina wajen su Hurriya Amarya? Suna lafiya Hajiya, na bawa mahaifiyarta kudi mai yawa da bake kyautata zaton za su wadace ta siye mata duk wani nau'i na kayan Kitchen, Furnitures kuma ni zan siye mata da kai ne Ka kyauta, haka nake son ji sai dai su ma kayan dakin da dama ai iyayen mata ka barwa su zaba mata za su kyau, ko kuma mahaifiyarta idan da hali Mahaifiyarta har yanzu bata son ganina Hajiya, kudin nan ma Gwaggo da Bappa na hannatawa ita bata da son saurare ma Fushi ta yi da yawa, sai ka sha wahala kamin ta sauko, kuma ina fatan idan ta sauko abubuwa za su daidaita ko dan yaya Daya daga cikin dalilin da ya saka nake son kyautata mata a yanzu fiye da kenan, kuma ina tunanin jingine lamarin auren yarinyar nan ya kamata na kimtsa gidana tukuna, Sapna ma ina ta shirye shiryen dawowa da ita a garin nan kusa da ni, domin halin da na same ta last week da na je garin nan ban jidadi ba Wannan ma wani abu ne da ya kamata ka yi tuntuni, ni har mantawa nake da kana sa ya a kauye saboda dadewar da take bata zo ba, kuma mu ma ba ma zuwa amman idan a nan ne ka ga tana kusa da mu, na jidadin kudurinka Tsoho Allah ya maka albarka ya kara yaye damuwa ya haskaka rayuwa Ameen Hajiya Sai ka cigaba da rike addu'a, kuma idan da hali ita ma Kaltume ka dawo da ita cikin yayanta, ta ci albarkacinsu Ajiyar zuciya Appa ya sauke yana jin kamar Hajiya Binta na matso masa da mutuwa kusa. Wato Hajiya da dai za a kara daga min kafa wata kila a gaba zuciya ta raya min haka, amman a halin yanzu matar nan bata gabana ko kadan, da ina tunanin idan ta cika idda zan fada mata ta koma gidanta ko Family House dinsu, domin bana bukatar zamanta a gidan nan da sunan zaman Yayanta Ba saboda ita zaka yi ba Tsoho saboda yayanka zaka duba, Yasir da Ruma domin ba zan saka da Khairy ba Idan umarni ne Hajiya zan bi idan kuma shawara ce zan duba Shawara ce, Iyami ma da take kyautata min nake kaunarta cilasta maka maida ita ba balle Kaltume da ba dan darajar Yayanta ba da ko kallonta ba zan yi ba, babu kalar cin mutuncin da bata yi min ba, amman shi babba ba ya zama kamar yaro kuma abun da duk ka aikata mai kyau ko marar kyau zaka girbe shi a kusa ko a nesa, wannan fadin Allah ne Haka ne, Kuskuren kuma daga ni ne Hajiya ban tsaya na duba background din ba kamin na dauko, kaddara ta riga fata Wannan ma zai wuce tsoho, ka kyautata zamanka da Iyalinka gwargwadon yadda zaka iya, kuma ka kwatanta adalci a tsakanin anka ita soyayya an sani Allah yake sakata, amman sai mutum ya bar abun a zuciyarsa ba sai ya bayyana ba domin bayyana ko nuna fifiko akan wani shi ke bude kofar abubuwa da yawa da baka yi tsammani ba In Shaa Allahu Hajiya Allah yayi taimako ya hada kan Iyalinka Amin Ya amsa sannan suka yi sallama ya sauke wayar ya kalli ragowar furar da Sapna ta daka masa da kanta ta aiko masa bayan dawowar daga kasar Maradum. A yanzu jin kansa yake a free kamar wanda ya fito daga wani kangi ya samu yanci haka yake jin a ransa, nishadinsa na da yadda tsarin rayuwarsa na baya a yanzu jinsa yake a normal a yadda ya saba yi. A yanzu din ne yake jin marmarin abokiyar rayuwarsa fiye da koyaushe be taba bakincikin rabuwa da ita ba sai a yan kwanakin nan gaba daya ta shige masa a rai wani sabon kaunar Amma yake ji a ransa, be tabbatar da ya tabka babban kuskure na sakinta ba tare da ta yi masa laifi ba sai a yanzu bata kusa da shi, gashi idan ya tuna da yaransa Hamad Hurriya da yan biyun da ta haifa masa sai ya ji tausayinta ya kara kama shi. Lokuta da dama ya kan nutsa a duniyar tunanin dalilin sakin nata sai ya rasa, gaba rayuwar baya ta zame masa kamar mafarki yayi wasu abubuwan da yayi ma Amma da Hurriya da kuma iyayenta idan ta tuna sai ya ji babu dadi, kuma ya rasa dalilin haka, kamar yadda a yanzu ma ya rasa dalilin tsanar da yayi ma Hajiya Kaltume, macen a da ko tari ta yi jikinsa rawa yake ya amsa mata, a yau ita ce yake jin baya bukatar zamanta a gidansa ita ce a yau yake fatan ta gama zaman idda ta bar masa gidansa, a yau ita ce macen da baya son kallon bangarenta idan zai fita. Zancen da Hajiya Binta ta yi masa cewar mata ne suka dace da siyayyar kayan dakin Hurriya ya saka shi kiran Number Amma, kamar wani yaro haka ya aje wayar a gabansa ya dauke hannayensa yana kallon number tare da fatan Amma ta daga kiran amman bata daga ba har kiran ya katse, ya sake gwada kiran a karo na biyu sai kuwa ta dauka hannunsa ya kai ya taba speaker dake jikin wayar, sallamarta kadai nishadi take kasa shi tana tuna masa da rayuwarsa da suka yi a baya. Wa'alaikissalam...Hajiya an wuni lafiya? Alhamdulillahi Maa Shaa Allah, Ina yarana duka suna lafiya Lafiya kalau Ta amsa a takaice domin bata son wata maganar da ta wuce sha'anin yara ko gaisuwa ya wuce tsakaninsu. Shiru ya dan yi na lokaci kamin ya ce. Yanzu na gama magana da Hajiya nake fada mata yadda muka yi da ke na siyayyar wasu abubuwan na Hurriya, nake fada mata ina son siyayyar kayan dakinta da kaina kamar yadda nake yi ma sauran Yaya Sapna da Maama, wai take cewa su ma siyen kayan daki ai na uwa ne, iyaye mata ya kamata su yi Haka ne Shi ne na ce idan babu damuwa sai ki shirya tare da mutanenki mu tafi Kano a duba mata kaya masu kyau wadanda hankalinku ya kwanta da su, da ice ita din babu lalura a tare da ita da sai mu tafi tare da ita ta zaba da kanta kamar yadda sauran yan'uwanta suka yi Already mun yi order kayan Kitchen gurin Khadeeja Candy, zata saka a kawo mana daga Kano har gida, kuma
Chapter 136 · 0% Book details