← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 143

Sashe 23

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fara ci kamin ta ci na kowa wani lokacin ma bata taba abincinsu sai ta ce ta koshi. Bayan sallah la'asar Yasir ya iso gidan daukar Hajiya Binta kamar yadda mahaifinsa ya umarce shi, cikin gidan ya shigo suka gaisa da sannan ya fito tare da su Hurriya a daidai lokacin da Rukayya ta sallami bakonta ta nufo karamar kofar shiga tsakar gidan da suka fito. Yasir ya gida Ya sake mika masa gaisuwa a karo na biyu bayan gaisuwar farko da suka yi a lokacin da ya shigo. Mutumen da na gani saurayinki ne? Wani kallo ta yi masa jin yadda yayi mata tambayar kai tsaye kamar da zolaya kuma kamar gaske, domin murmushin dake fuskarsa ya hanata fahimtar komai. Dan makarantar mu Dan makarantarku har cikin gida? Lallai yana da matsayi da alama Murmushi kawai ta yi ta maida dubanta gurin Hajiya da Amma ta rakota suna tafiya suna hira. Allah ya kiyaye hanya, Hurriya sai kun dawo uhmmm za a shiga a cigaba da karatun ko? Ko last time da na zo har na fita baki sani ba tsabar karatun littafan soyayya, to aje a karasa kar a manta page din da ake Ta girgiza kai still tana murmushi. Yasir ka cika shiga min hanci fa... Haka kemin idan na je gidanku ko zama na yi sai ka ce ba daidai na zauna ba Toh ki fyato ni mana idan kin isa A nan ma murmushi ta yi ta shige ciki, shi ma ya bita da kallo yana murmushi Hurriya da Hamad kam tuni sun kai cikin mota, inda sabo sun saba da ganin tsokanar yayansu akan kanwar Mamansu ba sabon abu ba ne a gurinsu Amma ma ta saba gani balle kuma su. Amma da kanta ta budewa Hajiya mota ta shiga ta rufe sannan ta juya ta koma ciki Yasir ya shiga ya fara jan motar. Yasir na ce ko a fara sabunta kayan dakina ne na kusa samun kishiya? Hurriya ta saka dariya Hamad kuma yayi murmushi tare da cewa Hajiya yanzu kuma kin fasa aurena? Eh ga babba me zan yi da yaro! Yasir ya ishe ni gashi har yana nema min kishiya, ko da yake Kaltume ai ba zata yarda ka dauki wannan ba sai dai wata Ke tsohuwa waya fada miki har yanzu ana irin zamaninku da ake yi ma mutane auren dole? Ni zan zabo wadda nake so na yi aurena To Allah ya nuna mana, kuma ya bada ta gari Ameen Ya amsa yana cigaba da jan motar. Sai da ya fara isa gidan Hajiya ya sauketa sannan ya juyo ya kama hanyar gidansu, a harabar Hajiya Kaltume ya faka motarsa ya bude ya fito Hamad ma ya fito tare da Hurriya gaba dayansu suka nufi hanyar falon Hajiya Kaltume. Hurriya me ya samu gilashinki? Yasir ya tambaya domin tun zuwansa daukarsu ya lura da fashewar gilashin nata. Ta kai hannu ta taba gilashin. Faduwa na yi Karaf Hamad yayi ya ce. Karya take wani bakon Momy ne ya mareta ni kuma ya na fasa masa tayun mota gaba daya Daga Huriyyar har Yasir tsayawa suka yi kallonsa da mamakin furucinsa. How? Wuka na saka wukar Momy ta yanka ashi na yi ta cakawa ina yanka har da sai da na fashe duka tayun Maganar yake yana nuna yadda yana yana cize baki alamar eta. Cikin mamaki Yasir yayi dariya ya bugo kan Hamad. Baka da kyau yaron nan bura'uba Hurriya ta yi murmushi for the second time ta sake jin Hamad ya burge ta a yau, bayan da ya fadi cewar zai zama likita saboda yayi mata aikin ido yanzu kuma ya fasa tayun wani saboda ya mareta, ita dai ta san bata jituwa da Hamad suna yawan yin fada da samun tsabanin amman kuma yana nuna damuwarsa da kulawa a duk wani abu da ya shafeta, idan wani ya taba ta yana jin zafi fiye da yadda shi idan aka masa yake ji. Yasir ya shiga tambayar me ta yi ma bakon yayi mata marin da ya saka gilashinta fashewa. By Misteke na fito... Shi kansa be ji dadin jin karami dalili da be taka kara ya karya ba ya saka bakon marinta marin kuma mai zafi. Mutane ba su da hakuri kuma ba su da hakuri... Ya rufe baki yayinda yake tura kofar falon ya shiga. Toh Wallahi ba zan dauka ba, wannan wulakanci da rainin wayon da Nafisa take min yayi yawa Me ya faru? Yasir ya tambaya domin shi kadai ne be san wainar da ake toyawa ba. A take ta amaye masa cikinta tana wani cika domin ba karamin cin mutunci ne a gareta ba Momy ta zargeta da haka duk kuwa da irin rashin zama lafiyar da suke. Yasir ya kalli Hamad, Hurriya ma ta kalli Hamad Hamad ya kalleta kowa yayi shiru, shi dai Hamad ba zai yi laifi yace shi yayi ba, kuma idan an gano shi yayi hakan ba zai dame shi ba, Hurriya kuma ba zata tonawa dan'uwanta asiri ba, balle kuma Yasir da ko da yaushe yake kashe wutar fitina. Toh Hajiya Ki yi hakuri, dan Allah ku daina wannan fadan, bana jin dadi haka Appa ma ba dadi yake ji ba, kuma dai ba yara kuke ba be kamata ace kuna biye zuciya ba Hajiya ta daki cinyarta Wallahi ba zan hakura ba, sai ta dandana kudarta, kuma Wallahi na fi karfinta bokanta yayi karya Wallahi, Iyami ma ta kara da ni ta bar ni balle ita bukkar banza, mai karyar arziki sai ka ce kanta farau arziki duk ta fi ta cikawa mutane gida da bakin kuri da iyayi ita diyar mai kudi, mun ji karuna duk arzikin ubanta be kai karuna ba, ni kuwa sai na zame mata fir'auna a cikin gidan nan Subhanallahi Hajiya dan Allah ki daina irin maganar nan haba Yasir ya fada cike da damuwa, domin baya jin yadda matan ubansa suke samun tsabani a gidan. Babu ruwanka babu ruwanka idan ba zaka taya ni yaki ba karka sake shiga tsakanina da kowa, dan iya. Ke kuma yar gadon munafurci bace min da gani Ta karasa tana watsawa Hurriya dake tsaye tare da Hamad harara, babu bata lokaci Hurriya ta juya ta fice daga falon, Hamad kuma ya tsaya a gurin kamar ba zai tafi ba, irin yadda yara masu fama da rashin kunya suke yi, sannan ya fice yana wani tukuki saboda saka sunan uwarsa a fadan da Hajiya Kaltume ta yi kuma ta kira Hurriya da yar gadon munafurci. ____________________ Masu karatun suna hango abun da nake hangowa? Akwai Bomb fa ba karami ba? Fatan dai kun shiryawa tafiyar? Idan kun karanta ku yi sharing [10/18, 6:16 PM] Nana 1: Hello Habibaties Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy Hanya Hurriya ta hadu da Hamad ya zo zai kirata domin ita Hajiya Binta ta fara tambaya daga isowarta gidan. Me ya same ki? Hajiya na kiranki tana bangaren Appa Ya tambaya kamar irin hankalinsa be tashi ba dan ya ga hawayenta. Momy ce ta yi baki shi ne namijin ya mare ni Me kika masa? Ban masa komai ba, kawai saboda na je fitowa da sauri shi kuma zai shiga na buge shi, shi kuma ya mare ni gilashina har ya fashe, da jikinki kamar itace mugu kawai Ta farasa tana kuka ita ma kanta ciwo yake an karon da suka yi, balle kuma shi da bata san yadda ya ji ba. Ina yake? Yana bangaren Momy Ta bashi amsa ta bar shi a gurin tsaye yana kallon apartment din Momy kamar mai tunani tafiya, ita dai ta yi gaba abinta, har Namra ma ta zo ta wuce Hamad na tsaye a gurin yana kallon part din. Hurriya na shiga bangaren Mahaifinta ta rungume Hajiya ta fashe da kuka. Hajiya Binta da tsayi ke neman gagararta sakamakon rikon da Hurriya ta yi mata kalli Alhaji Haruna. Kalli abun da ka yi Appa ya sauke kansa kasa ba tare da ya ce komai ba. Allah ya kyauta Hajiya Binta ta fada sannan ta taka a haka ta isa gurin kujera ta zauna Hurriya na rike da ita, har jikokinta da matar anta Momy suka shigo suka gaisheta, suka fita Hurriya bata dago daga jikinta domin ji take kamar Amman ce ta rumgume, wani gatan ma da kakanin suke mata Hajiya Binta da Gwaggo Amma bata mata irinshi. Kullum idan na zo gidan nan bangaren Iyami nake sauka, amman yau ka raba wannan a dole na sauka a nan, mace mai hankali da girmamawa, wannan matar ta san kimata, har abada ba zaka taba samu mace mai irin tarbiyarta ba tsoho Appa ya sauke ajiyar zuciya domin ya san gaskiya Hajiyarsa take fada, iri irin Iyami masu son iyayen miji da girmamasu kadan ne a duniya ba su da yawa. Hajiya ga abinci ki bari na zuba miki Aa Hurriya zata zuba sai mu ci tare ai kasan da ita na saba cin abinci idan na zo Appa yayi murmushi. Hurriya dago haka Hajiya ta ci abinci mana Hurriya ta dago ta bude kulolin ta dauki plate ta fara zubawa. Sai a lokacin Appa ya lura da fashewar da gilashinta yayi. Me ya sami gilashinki Hurriya? Faduwa na yi Ta yi karya kai tsaye. Hajiya ta kalli Hurriya sannan ta kalli Appa ta ce Kana da dai jin abun da Hamad ya fada min a mota, idan ba zaka dauki mataki ba ni zan zo da kaina na dauke yaran nan na maida su gidana, domin ba zan bari a rika wulakanta kamar wasu bare ba Appa ya shiga mata rantsuwa domin kare kansa. Wallahi Hajiya, ban san da duk wannan ba, ai kin san idan na sani ba zan bari ba, ni kaina sai a yanzu nake ji a gurin Hamad din, kuma In Shaa Allahu zan dauki mataki, Hurriya me yasa baki fada min abubuwan da suke faruwa ba? Hurriya ta kalli Appanta ta sauke kai ta cigaba da zuba abinci, daman ta sani ko da Hamad be yi ikirari ba zai iya fada balle ma har yayi. Wallahi ban sani ba, amman zan dauki mataki yanzu da yardar Allah Na dai fada maka, dan ba zaka saki uwarsu ba, kuma ka barsu ana
Chapter 23 · 0% Book details