Sashe 88
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kasa dake a gidan nan Shi dai wannan mutum suna jinsa kamar wani sarki Ta fada a ransa a zahiri kuma sai ta amsa da toh, ta nemi guri ta zauna har sai da direban ya iso, sannan mai aikin ta daukar mata kayan aka saka a motarsa. Mutumen da ya bude mata gidan baya ta shiga Soja ne dake sanye da uniform dinsa Complete, tana zaune cikin motar shiru tana kallon titi har suka isa. Tun a bakin gate din gabanta ya fara faduwa sakamakon arba da ta da fara da soldiers rike da makamansu, tafiya suka yi sosai ciki sannan suka isa wani bangere da aka ware dabam da sauran bangarori, daman gurin part part ne, a gurin da take ma part part ne. Fitowa yayi ya bude mata motar after ya faka, ta sauko kafafuwanta ta fito ta dauki kwandon shi kuma ya rika coolers din ya wuce gaba ta bi bayansa, gabanta sai faduwa yake saboda tsaron dake gurin, kusan wannan shi ne karo na farko da ta taba arba da sojoji da yawa haka. Wani gurin ya zagaya da ita dake bayan wasu manyan gine gine dake gurin suka isa wani part da aka kawata da furannin daga gaba. A nan din ma akwai masu tsaron wasu kuma suna ta aikin da takardu wasu da system. Can ciki aka wuce da ita ya lasa wani gurin kofa ta bude sannan ya matsa baya yayi mata alama da ta shiga. Captain ne zaune a kujera cikin katon office din yana mikawa wani files din dake hannunsa. Mutumen ya karba ya tsare masa sannan ya juya ya fice, shi ma wanda ya riko mata cooler sai da ya tsare masa sannan ya aje, da zai fita kuma ya sake sare masa, yana fita kofar ta rufe kansa. Hurriya ta dago idonta kadan ta kalleshi sai ta yi sa'a ita yake kallo daga inda yake zaune sanye da uniform dinsa complete abun da bata taba gani ba, ita bata ma taba sanin soja ne ba sai yau. Da sauri ta maida idon har da dan rufesu kwarjininsa na yau ya fi na kullum wata kila saboda yau yana sanye da kakin na soja ne, dake karawa ko wane namiji kawarjini balle shi da Allah ya wadata da six-packs. Baki iya sallama ba? Baki iya gaisuwa ba? Assalamu Alaikum ina wuni Ta hade sallamar da gaisuwar a lokaci daya ta fada da sauri, har lokacin tana rike da basket din ne tun da be bukaci ta aje ba. Ya aje pen din hannunsa ya mike tsaye ya zagaya ya fito daga gurin table din ya nufi wasu kujeru da suke can gefe visitors chair ya ware daya ya ja baya. Zo nan ki zauna ki ci Ta fara tafiya tana rike da basket din, ta ci? Ita? Ko kuma dai bata ji daidai ba? Maybe nufin yake ta aje. Dan haka da ta aje basket din ta ta dauko coolers din ta kai gurin ta aje. Na kai Ta fada, ba tare da bari sun hada ido ba. Ya mata banza ya cigaba da aikin da yake. A nan ta soma fahimtar manufar. Ni fa na ci abinci Ta fada kamar a shagwabe. Saboda ke na saka a kawo abinci nan, ina nan aikin ya min yawa kowa aiki yake yau, amman my mind was telling me kina can baki ci abinci ba you must eat...! Ya karasa a tsawace domin tana kokarin bata masa rai ne kawai, matsawa ta yi baya a zarane ta dan saci kallonsa tana bata fuska ita dai ta san yana neman ja mata matsala ne kawai a gurin Momy, kamar zata yi kuka ta ce. Na ci abinci fa Ya tsaya cak daga aikin da yake, ya dubeta. Kamin ya saka hannunsa aljihu ya ciro pistol dinsa ya aje kan table. Bana maimaita magana, kina cikin headquarter soliders ne you should be careful... Yana aje bindigar ya mike tsaye ita kuma ta fadi zaune jikinta na rawa kamar mazari, ta bude cooler ta fara zuba abincin wani na zubewa saboda tsoro. Ficewa yayi daga office din ya barta daga ita sai bindigarsa dake kan teburin aikinsa. Ta daga plate din ta dora a cinyarsa tana ci tana kallon bindigar, daman tana jin ana fadar soja basu da imani yau ta tabbatar. Captain be dawo Office din ba sai da ya dauki lokacin da yake kyautata zaton ta isa cinye abincin. Ta mike tsaye da sauri. Na cinye Ya kalli plate din sannan ya kalleta. Yanayinta so innocent da raunin dake tattare cikin kyawawan idanuwanta, suka saukar masa da tausayinta, fiye da wanda ya ji a lokacin da ya mareta Namra ta fada masa makauniya, fiye da wanda ya ji a lokacin da aka dauke dan'uwanta, fiye da wanda ya ji a lokacin da ya same ta tana cin abinci a kitchen din Momy irin cin yan yunwa tana kuka, fiye da tausayinta da ya ji a lokacin da ya ji maganar Momy da Namra akanta. Dauke kai yayi ya nufi teburinsa ya bude wani guri daga kasa ya dauko box din gilashin da ya taba bata a lokacin da ya fasa na ta, a yanzu yana son ya bata gilashin ne da ya siya da hard earned money, da hannunsa a England, as an apology na marin da yayi mata a lokacin da yayi zaton tana sane ta bugu kirjinsa. Cire gilashin idonki Cikin wata muryar data fi kama da shagwaba da kuka ta ce Idan na cire hudu zan gani, bana gani komai sai da shi Kansa ya daga sama, yana addu'a a zuciya, na neman Allah ya kara masa hakuri da juriyar iya controlling kansa, domin babu abun da ya tsana a duniyar nan kamar musu. Hannunta ta kai ta cire gilashin ganin kamar zata bata masa rai a rashin aikata hakan, bayan kuma Momy ta gargadeta, a take kuwa ta ganin komai da kyau hudun da take tsoro ya mamaye idonta, da can tana ganin dishe-dishe idan ta cire gilashin sai dai bayan tafiyar da dan'uwanta daya tilo yayi ya barta sai idanuwan suka kara lalacewa saboda kukan da ta sha, da kunnuwanta take auna sautin takunsa har kwakwalwarta ta sanar mata yana tsaye a gabanta. Tsakiyar cikin kwayar idonta yake kallo, ya sani ko da zai saka wuka ya barka cikinta, ko ya dora mata bindigar da take tsoro a kai ko yayi mata dariya ba zata shaidar abun da ta gani ba, domin ita ta rasa wannan ni'imar. Kansa ya sauke kasa ya busar da iska bakinsa a hankali. Alhamdulillah Ya furta da nuryar da shi kadai sai muhallinsa za su ji, domin shi ya samu abun da Hurriya ta rasa, daman kuma hausawa sun ce mutum dan tara ne be cika goma ba, Allah ya mata gomai ya rage da ido, shi ne kadai tawaya a gurinta. Kamar an kunna wuta haka jijiyoyin idanuwanta suka sanar da kwakwalwarta dake raba sako, ta karbi sakon hoton fuskar Captain dake tsaye a gabanta hannayensa kuma suka zagaye tsakanin dama da hagu na kyakkyawar fuskarta. Dauke hannunsa yayi bayan ya saka mata gilashin sannan ya karbi na hannunta a lokacin da hawaye suka sauko a idonta irin saukowar da wanda yayi arba da su a fuskarta zai tausaya mata. Ya nade gilashin ya dora a kan teburinsa ba tare da ya kalli hawayen da suka zubo mata ba. Direba yana waje yana jiranki Daga haka be kara cewa komai ba ya fice daga office din, gafen hijabinta ta saka ta share hawayenta, sannan ta nufi gilashinta ta dauka ta cire wanda ya saka mata ta maida nata sannan ta nufi kofar ta bude. Taku daya biyu kamin ta yi na uku wanda ya kawo ta ya nuna mata hanyar da za su ba, ba wanda suka zo dazun ba. Ba musu ta bi bayansa har suka isa gurin motar ya bude mata ta shiga ta zauna, shi kuma ya shiga mazaunin tuki yayi ma motar key, amman shiru shiru ta ji yaja motar sun kama hanya ba, bata ankaro ba aka bude back seat inda take zaune, Captain ne ya shigo cikin motar ya zauna, tana kallonsa ta yi saurin maida idonta kasa, sai ya kai hannu ya dago fuskarta ya cire gilashin idonta ya saka masa nasan data cire ta aje masa a office, sannan ya bude motar ya fita da nata ya rufe motar. Damdamdam.. Ya buga bayan motar sai sojan yaja motar suka fara tafiya. Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 29 Sai da suka wuce sannan ya dawo office dinsa, yana shiga ya aje gilashin na Hurriya a saman teburinsa ya zagaya ya zauna ya cigaba da aikin da yake. Few minutes Namra ta kira wayarsa dake gaban teburin sai ya amsa ta bluetooth din dake kunnensa yana duba wasu takardun. Ni fa na zagaye garin nan kaf