Sashe 93
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... Cikin tsananin tashin hankali aka kwashi Salma zuwa asibitin, duk kuwa da kasancewar alamun tafiyar da babu dawowa ya bayyana a jikinta amman Hajiya Kaltume bata yarda yarta ta mutu ba sai da likitoci suka tabbatar da haka. Tun a asibitin Hajiya Kaltume take kirewa tana faduwa ta tashi tana kuka irin na tashin hankalin da ba a saka masa rana, Appa ma duk juriyarsa sai da ya zubar da hawaye a cikin asibitin, dominta abun tausayi ne, yarinyar data kare makaranta few weeks ta dawo gida cikin aminci da koshin lafiya, babu ciwo babu komai an wayi gari babu ita a yau. Hauka ne kawai Hajiya Kaltume bata yi ba a lokacin da aka iso da gawar yarta gida, Khairy ma idonta har ya canja kala, Ruma ma da kuka ta baro makaranta ta dawo gida, Namra da Hurriya ma duk sai da suka zubar da hawaye na tashin hankali da mamakin mutuwarta, abun ya taba kowa balle kuma Yasir da ya dauke ya kaita asibiti. Da azahar aka yi mata sallah, a lokacin gidan na cike da jama'a domin wannan ne karo na biyu da Appa yayi rashi mai girma bayan na Hamad. Hankalin Hurriya ya tashi sosai a lokacin da ta yi arba da gawar Salma da aka daga aka saka a mota, kuma aka ja motar aka fita da ita wasu jama'ar na yi mata rakiya a cikin har da mahaifinta da dan'uwanta da kuma wasu daga cikin familynta na kusa da na nesa, ta tabbatar a yanzu Salma ta yi bankwana da kowa kenan har abada, lallai mutuwa akwai tashin hankali da bakinciki da kuma ban tsoro. Ana tafiya da ita sai ta dawo daki ta zauna gaba daya tsoro ya kamata kusan wannan ne karo na farko da ta yi arba da gawa ganin idonta. Ganin da ta yi mata jiya da dare a lokacin da ta shiga ta yi magana da Yasir kawai take tunawa. Misalin karfe biyu da mintuna tana dakinta kwance Inna Shatu ta shigo kiranta, sai a lokacin ta taso ta fito duk hayaniyar mutane da take ji na yan'uwan Momy wandanda suke kusa suna zuwa yi ma Appa da Hajiya Kaltume gaisuwa ba saka Hurriya lekowa ta ga ko su waye ba. Tana fara saukowa stairs din ta hango Mama Rukayya sai idonta ya cika da hawaye bata kula da kowa ba sai bayan da ta fada jikin uwar tata tana kuka domin mutuwar ta taba matuka. Mama Rukayya kin ji Yaya Salma ta rasu Gaisuwarta na zo, kowa baya wuce lokacinsa Hurriya, yanzu tsakaninku da ita sai addu'a Tana fada tana sharewa Hurriya hawayenta. Sai a lokacin Hurriya ta lura da wasu daga cikin yan'uwan Momy da suke falon, ba kowa ta sani ba amman haka ta bisu daya bayan daya tana gaida su, wasu su amsa mata kai tsaye wasu kuma sai sun gama yanga saboda sun san wacece ita da matsayinta a gurin Momy. Ina wuni Ta fada a lokacin da kai gurin Captain dake zaune kusa da wata matar mai kama da Momy sai dai ita yarinya ce sosai da bata kai ace ta haife shi. Da kai ya amsa yana kallon idonta dake cikin gilashi Hurriya ta juya gurin Rukayya. Mama Rukayya mu tafi daki Muje ki rakani gaisuwa tukuna Rukayya dake fada ta mike tsaye suka jera da Hurriya suka fice daga falon. Sai da suka kusa fita harabar gidan sannan Rukayya ta kama hannun Hurriya ta tsayar da ita daga tafiyar da suke. Ni fa ban so zuwa gaisuwar nan ba Saboda me? Saboda Hajiya Kaltume kin san matar nan ba wani kirki ne da ita ba, zata ma iya cewa dadi muka ji, Yasir ne ya takura sai na zo, na fada masa bana son Hajiya Kaltume ta yi wata magana yace min babu abun da zai faru Ba zata yi komai ba, Mama Rukayya baki ga yadda ta yi kuka ba idonta ya kumbura sosai ni tausayi ma take ba ni Ke kiji tausayin kanki, ita ma ta dandana yadda muka ji lokacin da Hamad ya rasu, ni da na sani ma wata zan janyo ta rakoni ko ma na saka mask, ina gudun Gwaggo ta sani ne shiyasa na janyo twins na ce mata gidan kawata zan tafi, ba su san da maganar mutuwar ba, da Yasir ya fada min ban fada musu ba, saboda na san Gwaggo zata iya hanani zuwa amman ita ta zo, kuma Yasir ba zai jidadi ba idan ban zo ba, sai na koma na fada musu Hurriya ta fara waige waige. Ina twins din suke? Suna can tare da Yasir, suna ganinshi suka bishi, muje ki raka ni na yi gaisuwar na koma Hurriya ta bita suka taka har bangaren Hajiya Kaltume dake cike da mutane ta ko'ina domin wannan ne karo na farko da aka yi mata mutuwa mai nauyi, yan'uwa har nasa sun zo saboda sun san mai hali take aure kowa binta yake sau da kafa a familynsu. Hurriya bata san Hajiya Binta ta zo ba sai da ta shiga bangaren na Hajiya Kaltume, da sauri Hurriya ta karasa kusa da ita ta zauna tana gaisheta. Hajiya ta amsa da dan murmushi kadan. Hurriya tun dazun nake dubawa ban ganki, na ce kina can kin boya ko sarkin tsoron mutane Hurriya ta share hawayen da suka zubo mata ta ce. Hajiya Salma ta tafi To ya aka iya, sai hakuri haka rayuwarma zata kare, shiyasa ake son mutum ya ji tsoron Allah ya bawa kansa lafiya, duniya ba gurin zama ba Yan'uwan Appa dake kusa da ita suka amsa da cewar haka ne, suna dorawa da nasu sannan suka yi ma Hurriya ya hakuri ta amsa tana kuka kai kace Salma wani kaunarta take. Rukkayya ma ta gaishe da Hajiya Binta sannan suka haura sama tare da Hurriya suka shiga har cikin dakin Hajiya Kaltume, zaune suka sameta kan karamin Carpet Khairy na kwance a cinyarta, kallo daya zaka yi mata ka san mutuwar nan ta taba ba, ba karamin tabawa ba, domin ta fada a take ga ido ya kumbura kamar ya silala, har bata iya daga ta duba mutane da kyau, Khairy ma nata idon ba baya ba domin ta sha kukan da bata taba yi ba, Maama na zaune kan gadon Hajiya Kaltume ita ma kana ganin nata idon zaka san an yi rashi a familyn. Rukayyah ta mika gaisuwa aka rasa mai amsa mata daga Hajiyar har Maama da Khairy, sai wasu yan'uwan Hajiyar ne suka amsa ta fara gaisuwa tana Allah ya jikanta suna amsawa da Ameen. Hajiya Kaltume ta dago wasu hawayen na zubo mata bakincikin rasa yarta na dawo mata farko, ganin Rukayya da ta yi, da yanzu su ne da kuka ba ita ba, amman gashi nan reshe ya juye da mujiya. Rukkaya karki sake shigowa gidan nan, munafurci ya kawo ki saboda ki zo ki ga zan yi tun da na rasa yata, kun jidadi ko? Azzaluman mutane, tun da Iyami ta auri Alhaji ba ni da kwanciyar hankali, kum bi kun hanani zaman lafiya, kuma Wallahi babu ke babu dana, ko mata sun kare a duniya Yasir ba zai auri karuwa yar iska irinki ba, kuma Wallahi ke da yayarki sai mugun abun ku ya koma kanku, sai kum ga abun da ba ku so, Allah ya isa A nan jama'a suka shiga bata hakuri, Hajiya Fatee na fitowa daga bandaki ta dorawa Rukkaya da nata. Daman ban da iskanci da tsaurin ido, ke har kin isa ki taso tsugudi dake wai kin zo gaisuwa, wato ke yar iska yar daukar rahoto, to sai kije ki fada musu yadda kika tararda mu, mutuwa dai ta san gidan kowa Wata yayar Hajiya Kaltume ta shiga yi musu fada tana tsawarta a matsayinta na babbar duk kuwa da bata san me yake faruwa ba amman zata iya auna wasu abubuwan a kalaman da Hajiya Kaltume ta fada cewar ko mata sun kare ba zai auri Rukayya ba, a lokacin ne suka gane cewar ita din kanwar Iyami ce. A fusace Rukkaya ta mike tsaye Ni ma zan tabbatar miki da wani abu yau, ko maza sun yi karamci a duniya ba zan auri Yasir ba, amman gida kam idan kika ga na daina shigowa, to babu Hurriya a cikinsa Tana kawai ta juya, Maama da Khairy suka taso zasu yi kanta, sai da aka rike su. Hurriya ta kasa cewa komai ita dai sai mamakin yadda Hajiya Kaltume take tsanar mahaifiyarta da duk wani abu dake da alaka da mahaifiyarta take, me ye laifin Rukayya dan ta zo gaisuwa, wanda aka yi ma rasuwa da ya kamata ace ya natsu ya koma ga Allah shi ne suke haka, kamar Rukkaya ce ta yi sanadin mutuwarta. Ko da ta fito daga dakin ta sauko kasa har Rukkayya ta fice daga gidan gaba daya. A lokacin da ta fito ta duba ko'ina bata ganta ba sai ta koma bangaren Momy ta shige dakinta tana ta mamakin, ta ya Hajiya zata ce sun jidadi waye yake farinciki da mutuwar wani? Ko da kuwa nesa ne balle na kusa. Bayan Sallah magariba Yasir ya shigo dakin nata shi ma kana ganinsa zaka san mutuwar ta taba shi, domin ya dan yi rama ga idonsa yayi ja alamar bacin rai da damuwa. Yayana Ya maida kofar dakin ya rufe. Hurriya, Rukkaya ta tafi? Wani abu ya faru ne? Ta bar twins bata koma da su ba, kuma na kira wayarta bata daga ba sai text ta yi min yanzu wai na aiko da twins ana mata fada a gida Ina suke? Suna kasa, me ya faru? Ta yi shiru kamar ba zata fada ba gudun kar ace ta yi munafurci ko gulma. Hajiya ta yi mata fada, ta ce wai ta jidadin an yi mata mutuwa ai ta zo daukar rahoto ne, har tana cewa ko ita kadai ta rage ba saka aureta ba, kuma ta daina zuwa gidan nan Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Ta furta da murya can kasa irin mai bayyana damuwa, sannan ya zauna gefeb