← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 143

Sashe 111

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Captain ya fito tare da iyayensa, Bodyguards na take musu baya. Ko kadan Momy bata so zuwa duba Hurriya a asibiti ba, ba dan Captain ya so haka ba kuma iyayensa suka biye masa ba zata taba zuwa dubata ba, domin ta fi jin tsanar Hurriya a yanzu fiye da koyaushe, sanadinta suka fara samun da Captain gashi kuma yanzu ta ja musu abun kunya, sai dai babu yadda ta iya saboda an'uwanta ya so haka. A dokar asibitin lokacin da suka zo ba lokacin ganin marar lafiya ba ne, amman ba a hana su shiga ba domin ko na goye ya san kura. Ina ne? Captain ya tambayi Momy ba dan ita ma ta sani ba, sai da ta sauke ajiyar zuciya ta kalli yayanta sannan ta daga wayarta ta kira Namra. Gamu mun shigo asibitin, wane daki ne? Ta fada musu har da number dakin, a nan suka juya zuwa wani ward din da ba wannan ba, ko'ina suka wulga sai ya kallesu kana ganinsu ka san ba kananan mutane ba ne. A lokacin da suka isa dakin da Hurriya take sai Captain ya kalli iyayensa ya ce. Wata kila ba zata so ta gan mu tare da ku ba, zan fi jindadi idan na shiga ni kadai, na san idan na ce ku zauna a mota na shigo ni kadai ba za su yarda ba shiyasa ban yi magana ba A nan kam Momy kasa hadeye maganar ta yi cikin bacin rai ta ce. Mu iyayenka mu zamu jiraka har sai ka shiga duba wata banzar yarinya tukuna mu tafi? Sai kace kai ka haife mu? Idan hakan zai faranta ransa me ye a ciki? Shiga ka yi abun da zaka yi son zamu jiraka a mota Daddy ya fada sannan ya kalli bodyguard dinsa daya. Ka tsaya a nan idan ya fito ku same mu a mota Okay Sir Daddy ya juya tare da Ammy domin komawa gurin motarsu, Momy ma dole ta bi bayansu iyayen yaro sun goyi bayansa ita a su ta ki bi, a nan ta samu damar karanta musu kabli da ba'adi na Hurriya, tana ta kusheta. Sai da suka wuce sannan Captain ya murda kofar dakin ya tura ya shiga, tana zaune saman gadon ta lankwashe kafafuwanta tana fuskarta hadu da kofar dakin. Kai kuma kai ne wa? Gwaggo ta tambaya tana kallonsa. Sai a lokacin ya tuna be yi sallama ba. Dan haka ya jadada sallamarsa sannan ya karasa cikin dakin yana gabatar da kansa. Sunana Jamal amman an fi sanina da Captain ni dan Momy dan yayanta... Toh ko me ya sa ka zo? Ya kalli Hurriya da babu gilashi a idonta hawaye na zubo mata ya ce. Na zo na duba Hurriya ne? Namra ta fada mana tana nan Namra ta tafi gida tun dazu, kuma dan Allah ba ma bukatar kowa, daga dangin Nafisa har na Kaltume, wannan kiyayyar ta yi yawa, ba bar uwa ba a bar ya ba, babu kalar azabar da ba a nunawa yarinyar nan ba yanzu abun ya wuce nan har sai a hada da kazafi? Kazafin ma na zina? Ita da gidan ubanta amman bata da walwala? Bata da jindadi? Akan me? Yanzu gashi nan kun yi sanadi idanuwan nata sun rufe gaba daya, bata iya gani ko da gilashin, buri ya cika tun safe da ta farka bata cewa komai ba, an kashe yarinya tana ji tana gani Gwaggo ta karashe fadan da kuka, Captain ya sauke idonsa kasa hawaye suka zubo masa. Ina kyautata zaton ni ne mutum na farko da ban yarda Hurriya ta aikata wannan abun ba, ban zo nan domin cin mutumcinta ba, ita ma ta sani kawai dai na kasa natsuwa ne har sai na zo na dubata, ban san matsayinki a gurinta ba, amman dan Allah ina rokon Alfarmar ki bar ni na ga Hurriya Gata nan ka ganta, amman ba zan je ko'ina ba, kai ma ba zaka dauki hotonta ka yadawa duniya ka bata mata suna ba, kuma ko waye da hannu a lamarin kada Allah ya bar shi da salama, daga yaron har kowa Ameen Ta saka yatsansa ya cire hawayen sannan ya karasa gaban gadon Hurriya saitin inda take zaune ya tsaya yana kallon fuskarta. Hawaye take malalarwar irin malalar da gulbi yake idan ya kawo, babu yankewa kuma babu fasa zuba, yanayin yadda take kallon saitin da yake tsaye ya isa ya kara tabbatar masa da bata iya tantance fari da ja a yanzu, sai bakin da ya rufe ganin idanuwanta. Hurriya... Bata amsa ba, motsa ba bata bar masa wata alama da zai gane tana jin muryarsa, ibadarta kawai take ta kuka. Cikin kuka Gwaggo ta ce Bata cewa komai, kuma bata gani Captain ya hadeye yawu mai matukar aci fa ma i a ma oshi. Likita ne ya ce bata gani ko kuma ke kika ga alamar bata ganin? Na ga alama, sa safe da ta tashi zata shiga bandaki ga gilashi a idonta amman lalabe take, na fada Likitan da ya shigo suka duba idon suka ce ua samu matsala, shiyasa suka canja mana daki ai, yanzu ba maganar sumanta ake ba, maganar idonta ake Likita biyu ya duba idon zamanmu a nan sun ce sai an yi aiki wai jijiyar dake hada idonta da kwakwalwarta ta samu matsala Captain ya daga kansa sama kamar zai fashe da kuka. Ya Rahma.... Ya ambacin mafi rahamar masu tausayi, sannan ya sauke kai ya kalleta pointing finger dinsa ya kai saitin idonta kamar zai tsokale ido amman bata matsa ba, a nan ya tabbatar da bata gani da gaske. Jiya kin zo min a suma, kin fada min baki aikata ba, kuma na yarda da ke. Yau kuma ina tsaye a gabanki ne domin na fada miki wani abu, kowaye ya aikata miki wannan abun Hurriya, ba zai sake samun farinciki ba a rayuwarsa, sai ya kunyata fiye da yadda ya so ya kunyata ki, sai na sa duniya ta tsine masa irin tsinuwar da zai ce ina ma be aikata ba Ya kama hannunta ya rike a gaban Gwaggo. Na miki wannan alkawarin Hurriya, kamar yadda na yi miki alkawarin dawo miki da dan'uwanki, shi ma wannan ki rubuta ki aje nauyin yana kai na.... Gwaggo ta share hawayenta ta taso daga inda take zaune da sauri tana fadin. Kai kai kai sake mata hannu, ban san sharin da ka zo da shi ba kai ma Captain ya sake mata hannun ya nufi kofa yana share hawaye, be ma kula maganar Gwaggo ta halin da ya ga Hurriya da damuwar da yayi arba da ita a fuskarta ta tafi da tunaninsa. Gwaggo ta kama hannun Hurriya ta shafe mata da hijabinta. Babu abokin yarda a cikinsu, ni da na san haka rayuwa zata miki Hurriya da ban bari kin zauna a gurin Ubanki ba, ko da kuwa shari'a ce zan yi da shi... Wani irin numfashi Hurriya ta fara fitarwa da karfi, kamin ta daga kanta sama ta kwala wani uban ihu.... Gwaggo ban aikata ba....! Gwaggo ta rumgume ta da sauri tana kuka. Wallahi ban aikata ba....! Na sani, babu wanda ya yarda kin aikata daga ni har Rukayya Allah ka hana, wanda ya aikata min wannan abun farinciki, Allah ka hana shi jindadi da kwanciyar hankali, Allah ka nisanta shi da natsuwa ka kusantar da shi ga kunya da damuwa, fiye da yadda yayi min Cikin tsananin kuka Hurriya ta yi ma kanta addu'a tana fatar mahallincinta ya amsa mata. Ameen Hurriya Ameen Gwaggo na amsawa Hajiya Binta ta turo kofar dakinta ta shigo da sallama. Hurriya na jin muryarta ta juyo ta kai hannu tana lalaben inda take. Hajiya komai ya kare min, idanuwa sun tafi, mutuncina ya zube... Na barar da kimar Appa da Ammana a idon duniya, komai ya kare yanzu babu abun da ya rage min, kullum bakinciki ne yake kusanto ni yana nisanta ni da farinciki.... Share hawayenki yarinyar, farincikinki mai kyau shiyasa yake da tsada, duk mai hassadarki yana son ganin bayanki sai ya dawo karkashinki, wannan alkawalin Allah ne mai hakuri yana tare da riba Allah da kansa ya ce dukannin tsananin sauki yana nan damansa, idanuwanki za su bude Hurriya, damuwa zata yaye farinciki sai ki samma wani, karki damu da hotunanki sun shiga duniya, ko karuwanci zaki yi, ki je ki yi ki dawo Hurriya ni FATIMA BINTA zan karbe ki... Hajiya Binta ta fada tana dukan kirjinta da karfi, kana ganinta kasan tana cikin bacin rai... If you read my book ba tare da kin biya ba, indai hakkina ne Wallahi ban yafe ba, ku kuma masu sharing Allah ya muku yadda kuke min. I rest my case CAPTAIN POV. Ko da suka isa Family House dinsu, gidan yana cike da mutane, abun ka dake mai jama'a, daman sun tun a lokacin da yake asibitin suka tafi ganinsa aka hana su shiga. Kowa sai murna ganin Captain yake kamar wani Sarki, domin kowa a familynsu yana son Captain ko dan duniyar Ubansa da Hajiya Turai. Duba daya zaka yi ma Captain ka fahimci baya cikin farinciki ko kadan, ya zama so silent daga lokacin da ya baro asibitin da Hurriya take zuwa motar har kawowa gidansu. Wani abun da ya bawa Ammy da Engr AA Turaki mamaki shi ne takardar sammacin kotu da suka tarar an kawo a gidan. Engr ya karanta takardar ya sake karantawa ya dago ya kalli yan'uwansa dake cike da katon falo na Mahaifinsa. Waya kawo takardar? Ma'aikacin kotu? Wata kanwarsu dake zawarci a gidan ta amsa masa. Momy ta tabe baki. Daman na raya a raina na ce sai abun nan yayi tsananina, karya yaron mutane fa Captain yayi kuma ya fasa masa hakora! Ammy ya kashe ido. Ashe kariya ce ma kawai shi nw za a kai ana asibiti? Ko kashe shi Captain yayi ba zan bari ya tafi kotu ba balle kuma karaya kawai da zubar da hakora Engr ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya ce Anya Bashir Sarauta ya san Jamal ana ne kuwa? Har zai yanko sammacin kotu ya aiko a gidan nan? Kuma ana yake kara? Ni Bashir Sarauta zai saka ana kotu? Bashir Sarauta talaka a cikin masu kudi? Bashir Sarauta da yake
Chapter 111 · 0% Book details