Sashe 30
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ciki mu ji abun da ya faru domin mu ma hankalinmu duk a tashe yake Gwaggo, ni ma kaina ban san abun da ya faru ba. Shiyasa na kira Hurriyar na ji ta bakinta Can gida ba su fada maka komai ba.? Appa ya ki yarda su hada ido. Ba su fada min ba, Hurriya tana kusa? Eh tana dakin mahaifiyarta, bari a kirata Gwaggo ta tashi ta fita. Bata jima ba Iyami ta shigo falo tana sanye da digon Hijab har kasa Hurriya na rike da hannunta. Appa na kallonsa sai gashi ya mike tsaye yana kallon cikin dake jikinta cikin wani yanayi na rashin jindadi. Na fada maka babu uwar da zata so yayan wasu kamar nata, yanzu wannan tashin hankali duk na minene? Ba komawa gidanka nake bukata ba kwanciyar hankalin yayana kawai nake bukata a yanzu... Iyami zauna Amma har ta yi kamar ta ce masa ba zata zauna ba, domin niyarta ta kawo Hurriya kuma ta jadda masa amanar yayanta ta koma, sai kuma ta zauna domin bata saba musa masa a komai ba. Sai da ta zauna sannan shi ma ya zauna. Ba wani abu aka yi mata ba, ki daina saka kishi da son cusa kiyayyar Kaltume ko Nafisa a zuciyar yayanki, ba dukan Hurriya aka yi ba, ba wata bakar magana aka fada mata ba, babu wanda ya mata komai, ba mutuwa aka yi ba To miyasa ta zo tana min kuka? Kuma Yasir da ya kawo ta be shigo gidan ba ya fita? Ni ma shi na zo tambayarta Amma ta kalli Hurriya har lokacin hawaye take sai dai ba kamar dazun ba. Ta kalli Appa Ina Hamad...! Appa ya ji tambayar kamar saukar aradu. Appa ya kalleta ya kasa cewa komai. Ina Hamad Appan Hurriya? Dan Allah kin kwantar da hankalinki Kamar ya na kwantar da hankalina? Miye abun tashin hankali a tambayar Hamad? Ko kuma shi ya aikata wani laifin? be aikata laifin komai ba Wallahi, ki ba mu guri zamu yi magana da Hurriya Amma ta kalli Hurriya kamin ta mike tsaye ya fice daga falon. Appa ya tashi daga inda yake zaune ya koma kusa da Hurriya ya zauna ya rika yarsa. Hurriya Na'am Appa Ki kwantar da hankalinki kin ji, Hamad zai dawo soon da yardar Allah, babu abun da zai same shi, kuma na ji dadin da baki fadawa Iyami abun da ya faru ba, kin ga tana da ciki zata iya daga hankalinta, Ta daga kai ta kama hannun Appa ta jimke da karfi. Appa bana ganin komai yanzu, bana ganin komai sai abun da ya faru, me yasa suka dauke Hamad? Me yayi musu? Wallahi dukanmu ba su sani ba, amman dai an san ba zai wuce su ce a ba su kudi ba, kamar yadda suka yi ma Kaltume kuma shi ma za su sako shi Hadda Ruma aka kama Na sani duka zamu biya kudi mu karbo su Da yardar Allah, amman yanzu zamu tafi dake gurin police za su miki tambayoyi akan abun da ya faru, saboda kun sanar da ya sanda, kamin nan kuma ina son ki min alkawarin ba zaki fadawa Iyami ba, kuma ki daina kukan nan har sai mun karbo shi Kamin Hurriyya ta dauki alkawarin suka jiyo Amma daga jikin curtains din kofar dakin tana furta. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Daga Appa har Hurriya ba su san Amma ta yi labe ba sai a lokacin. Appa ya taso ya fito da sauri yayinda Gwaggo ma ta fito da sauri daga dakin Amma ta nufota. Gwaggo sun dauke min Hamad, su biyu Allah ya ba ni sun dauke daya, kashe shi za su yi Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Gwaggo ma ambaton Allah ta shiga yi tare da rike Amma dake shirin faduwa. Allah yasa kaddara ba musanya zata min ba, Allah yasa ba Hamad za a dauke a ba ni wani ba, La'ilaha Illallahu, Allah kasa kari zan samu ba musanya ko ragi ba, su wa suka dauke shi? Na san ana be jin magana amman su yi hakuri dan Allah idan wani laifin yayi, kowa ya min haka be kyauta min ba, me suke so Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Gwaggo ma sai da ta fashe da kuka saboda kukan da Amma take yi. Appa kuma yayi tsaye a gurin hopeless yana kallon tsohuwar matarsa dake dauke da cikinsa ya rasa me zai yi. Littafin nan kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 50 0 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660 ________________ https://chat.whatsapp.com/F1ch00M9VNvFxrVVgCEeXo Ina Yan uwan Yan gayu makotan Masu Kudi? Daku nake Magana. Matan da suka san ciyon kansu masu hada goma ta zamo ishirin kuzo ku sari Kaya acikin sauki da rahusa a Ummu Ahmad store muna kawo kayan mu ne daga Lagos masu quality da karancen farashi akwai kayan kitchen akwai shoes and bags, Akwai kayan abinci na awo laces,kayan yara,da sauransu Sannan akwai kayan gyara irin su tsimi kala kala gumbar mata daban daban maganin sanyi Akwai kaza me rubutu da wadda akeyi da sanyun magani Akwai taimako na haihuwa ga wadda taje asibiti akace batada matsalar komai akwai rubutun da muke badawa Wanda idan ta gama Al adarta zatayi amfani dashi za adace da yardar Allah Akwai kayan kamshin daki da na jiki Location dinmu zamfara Muna tura Kaya a koina kk cikin aminci da yardar Allah payment validate ur order Ummu Ahmad 08032350261 Ni Khadeeja Candy nake tabbatar muku ba zaku taba nadamar siyen kayan Little Mommy na ba, uwata ce ta jini ba lake lake ba, please patronize her tana siyar kaya masu kyau da imganci, zaku iya tuntubarta ko ma ku tuntube ni kai tsaye sai ku zo Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660 Sai da Gwaggo da Mama Rukayya suka yi da gaske sannan suka iya rarashin Amma ta yi shiru, suka dagata suka shigar da ita falon har lokacin Appa ya tsaye ya rasa abun cewa, Hurriya ma kuka take sosai tana tausayin kanenta tana tausayin mahaifiyarta. Dan Allah Gwaggo a kwantar mata da hankali, ba yau aka saba daukar mutane kuma ana dawowa da su lafiya, na san dai ba zai wuce su ce suna bukatar kudi ba, kuma ba mu biya mu karbo shi Toh Allah ya bayyana shi cikin aminci Gwaggo ta fada cikin kuka, sai a lokacin Appa ya samu courage din fice daga cikin gidan tare da Hurriya, a mota ma Appa ya wahala kamin ya samu Hurriya ta yi shiru, hankalinsa be kara tashi ba sai a lokacin da take bada labarin yadda abub faru. Duk wani abu da ya kamata su tambayeta sun tambaya kuma ta ba su amsa sannan Appa ya dauko ta a motarsa tare da Direbansa suka nufo gida. Appa ka kar ni a gurin Amma please bana son nan Zan maida ke can Hurriya, ita ma ai ganinki zai saka ta dan ji sanyi, zaki dauki tufafinki, sai kuma Yasir ya baki dayan glass dinki da yake can Daga haka bata sake cewa komai ba har suka isa gidan. A harabar Momy Appa ya umarci direban ya faka, sannan ya fito direban ma ya fito da sauri ya budewa Hurriya mota Appa ya rikata ta fito, suka nufi bangaren ransa a jagule gaba daya shekarar nan ta zo masa a yadda be yi zato ba. A hankali ya tura kofar falon Momy sai da ya fara shiga sannan ya rikota ta shigo. Captain dake zaune ya mike tsaye yana amsa sallamar Appa, Appa ya karaso cikin falon cikin yanayin dake nuna yana cikin tsananin damuwa. Momy bata nan Oh to ina taje? Ina zuwa Hurriya Ya saki hannunta ya juya ya fice daga falon. Ance kananki? Captain ya furta a hankali yana kallon kwayar idonta dake ta juyawa alamar bata ganin komai. Kamar ya tsikaro mata allurar kuka sai ta fara hawaye tana rawar murya. A yadda Namra ta fada min ke suka zo dauka, kin san su waye? Ta girgiza kai. Waye kai? Ta tambaya domin bata wayanci ko waye ba. Yayi shiru yana juya invitation card din dake hannunsa for some seconds. Soja ne...! Ta mika hannu ta fara lalaben inda take jin sautin muryarsa. Dan Allah zaka nemo min kanena? Tana daf da taba fuskarsa ya kawar da fuskar ya kai hannunsa ya rika hannunta, ba tare da ya amsa mata da eh ko aa ba. Dan Allah ka nemo min kanena idan zaka iya, shi ne farincikinmu, shi yake tare min fada dan Allah ka taimaka Malam Soja ka nemo min shi Yayi shiru har lokacin be ce komai ba ya saki hannunta daman ya rika hannun ne kawai a kokarinsa na kawaicewa taba fuskarsa. Shi dai abun da ya kawo shi gidan dabam ya zo ya tararda wannan tashin hankali. Malam Soja... Jin shiru kamar babu kowa a gurin. Sai ya kai hannunsa ya rika 5 fingers dinta ya matsa a hankali domin tabbatar mata yana tsaye a gabanta har lokacin. Dan Allah ka nemo min kanena, ku ne sojoji ai ku kuke kama masu aikin yan ta'adda Kallon fuskarta yake kamar ance masa tana ganinsa. Dan Allah ka taimaka mana, Appa na kudi zai iya ba ku please Ya sake rika 5 fingers dinta ya matsa hannunta. Idan ka min alkawari ka matsa sau biyu... It take him ten seconds kamin ya sake matsa 5 fingers dinta for the third time, sannan ya saki hannunta ya zari Invitation card daya a cikin wadanda suke dayan hannunsa na dama, ya dora su akan mini table dake kusurwar kujerar ya juya bayan dayan card din ya yaga ya ciro pen dinsa yayi rubutu akai sannan ya maida pen din ya sake barkar takardar ya kama hannunta ya danka mata rabin. Karki fadawa kowa, kuma karki taba jefar da wannan takardar matukar ina fatar Kanenki ya dawo Ta jimke yar ficikar takardar a hannunta tana sauraren takun tafiyarsa har ta ji lokacin da ya bude kofar falon ya rufe. Bayan kamar minti biyar tana tsaye a gurin aka sake bude kofar falon aka shigo. Hurriya Appa ya ce na zo dake Yasir ta karaso