Sashe 112
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
karkashin inuwar dukiyata...! Ai wani sarkin kakan wani sarkin ne... Amman ya ba ni mamaki, ni ma kuma zan ba shi mamaki Momy ta ce. Ai duk Hurriya ce sanadi, gashi masu arziki za su yi fada akanta, yarinyar da bata kai ba Captain ya kalleta kamar daman jiran yake tace wani abu a kan Hurriya. That's it, Hurriya this Hurriya that... Komai Hurriya kike blaming, yarinyar da bata isa ta daga idonki ta kalleki a matsayin uwa ba, yarinyar da bata isa ta shiga dakinki ta rokeki wani gata ba, yarinyar da bata isa ta shiga Kitchen dinki ta zuba abinci ta ci ba, yarinya kamara kun matsa mata kun firgita mata kwakwalwa, yanzu ga wata bakin hayakin ya rufe ta amman still baki ji tausayinta ba? Ammy ta kalleshi tana kai hannu ta taba shi kuma ta kwantar masa da zuciyar dake fisgar anta. Captain you can't talk to Momy this way... Haba.. Cikin lalama take fada tana dan kallo Momy. Captain ya kalli Ammy. Kiyayyarta da yarinyar nan wani abun ne da ya shafe ta na dabam, babu ruwana a ciki ni dai abun da na sani babu abin da zai hana ni auren Hurriya... God forbid... Ammy ta dauke hannunta daga jikinsa da sauri kamar ta taba mugun abu. Yarinyar da duniya ta gama ganin tairaicinta? Yarinyar da bata da kamun kai? Karuwa? Kuma makauniya? Ba zan karbe ta a matsayin suruka ba har abada Enough....! Daddy ya daka mata tsawa, sannan ya kalli Captain ya ce. Tashi ka shiga ciki ka huta Captain ya mike tsaye ya kalli mahaifiyarsa hawaye na zubo masa. A halin yanzu, Wallahi duk duniya Ammy ke kadai kika kai ki kira Hurriya da karuwa, na hade ban ce komai ba, kuma ban dauki mataki ba... Ki gafarce ni Ammy ni dai kam ban taba jin tsananin son wata mace a zuciyata ba kamar yadda nake jin Hurriya a yau, i love her more than life.... Kowa kallon Captain yake domin yau yayi abun da be taba ba, fadar yana son wata a gaban kowa, kuma har ya zubar da hawaye. Ko Aljana ka ce zaka aura Jamal zan aura maka ita matukar hakan ne farincikinka, kuma zan raba ka da wanda baka so matukar hakan zai dada ranka... Ka bar wannan maganar a hannuna tafi ka huta.... Cewar Daddy yana nuna masa hanyar bedrooms din dake stairs... Captain ya nufi bedrooms din yana jin kamar za'a raba kirjinsa gida biyu, Hurriya ce aka watsa hotunanta amman shi da ita ne suke raba nauyin bakincikin. Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 38 Yana shiga dakin ya nufi wata kujera ya dafa kanta ya sauke kansa kasa ya rufe ido. Kamar an tsikare shi ya bude idonsa ya juyo da sauri ya fito daga dakin, tafiya yake mai kama da gudu ya sauko stairs din. Ina wayata? Ya tambayi Ammynsa sai Momy ta bude jakarta ta dauko ta mika masa tana hawaye. Ya saka hannu biyu ya karba ya juya ya koma ciki. Yaya da gaske barinsa zaka yi ya auri yarinyar nan? Wallahi bata kai ba Yaya bata yi matsayin da zata zama surukar mu ba Idan aurenta ne abun da Captain yake so, zamu nemi aurenta kuma iyayenta za su ba mu ita dan dole ko da bata so, Allah ba hallatawa iyayen autawa Yayansu wanda basa so ba, ya dai mata ikon zaba musu na gari, kamar yadda ya hallata auren mazina idan sun tuba Ammy ta dubi Engr Ni fa ban gane ba, da gaske zaka aura masa yarinyar nan kenan? Ni ba da yawun bakina ba ba zan yarda Captain ya zauna da wannan yarinyar ba, ai abun kunya ne ace wannan yarinyar ta zama surukar mu duk matan duniya a rasa wanda zai aura sai karuwa? Ina tunanin kin fi ni son farinciki Captain... Ta kawar da fuskarta ta fashe da kuka. Wannan goyon bayan da zaka ba shi be yi ba Yaya, be kamata ka biye masa ba shi fa soyayya ce take dibansa lokacin da zata zubar da shi zai fada a mugun guri ne Wata kanwarsa ta fada. Engr ya mike tsaye rike da takardar sammacin ya ce. Idan har kuna ganin akwai rashin dacewa a auren yarinya to ku roki Allah ya sauya masa da wanda ta dace, kuma ki kwantar masa da hankali ku nuna masa illar hakan, idan ya sauya ra'ayinsa Falillahil-hamdu Ya nufi kofar fita ya fice daga falon yana kiran wani Assistant manager. Sai da ya fita sannan Momy ta dubi Hajiya Turai ta ce. Karki yarda Wallahi ta ya za'a kawo miki wannan yarinyar a matsayin suruka? Taya? Ai da kunya ma Wani gine ne Captain yake son na dora wanda ba zai iya karasa ba, ni dai kam ba zan taba karbar yarinyar nan a matsayin suruka ba Ammy ta fada tana share hawayenta. Wata step Mother din Engr ta dubi Momy ta ce. Kuma da gaske yarinyar nan ta aikata abun nan? Ba mu da tabbaci, ko da ace ba da gaske ba ne, ai be kamata ya aureta ba Hajiya, saboda duniya ta gama ganinta Idan shari aka yi mata bana ganin illar aurenta a gurin Jamal, illar kawai ace ta aikata ne, shi ma kuma idan ta tuba Allah zai karbi tubanta kuma yayi mata sakamako mai kyau, domin Allah yana son bayinsa masu komawa a gurinsa suna kuka suna rokon ya yafe musu, shin idan hakan ya faru da yarki zaki so wani ya juya mata baya? Ku yi tunani mana Ko ma dai minene Hajiya ba zamu yarda Captain ya auri yarinyar nan ba Momy ta amsa mata kai a ranta tana cewa saboda ba jikanta ba ne take fadar haka. Safa da marwa yake waya a kunnesa yana jiran wanda ya aikawa kiran ya amsa. Nafi'u ka duba hotunan kuwa? Ya gabatar masa da abun da yafi daukin ji fiye da gaisuwarsa da sallama. Sir barka da yamma, eh na duba Ya ake ciki? Editing ne i know I'm sorry Sir gaskiya ba editing ba ne, na duba na yi bincike ni da entire team dina ba mu ga wata alama dake muna editing ba ne Captain ya kai hannu ya shafa kansa ya runtse ido sosai. Maybe baka iya aikinka ba, maybe baka duba inda ya kamata ka duba ba Na iya aikina ranka ya dade kai ma ka sani, wata kila da wannan gaskiyar mai nauyi ce shiyasa ka kasa karbarta, amman na gano wani abu Ya bude idon da sauri ya nufi bathroom ya bude ya shiga ba dan ya boyewa wani ba sai dan rudewa da yayi jin abun da yake nema zai samu. Alamu ya nuna yarinyar nan bata cikin hayyacinta aka yi hotunan, ko kuma tana cikin bachi mai nauyi domin jikinta ya saki sosai, yadda yake rikota da ace a hayyacinta take ba ta yi yaukin jiki haka ba, kuma babu inda take shauki ko murmushi shi ne kawai yake yi, shi ma kuma akwai alamar tsoro a tare da shi ko kuma rashin kwanciyar hankali, yadda hannayensa ma suke a jikinta ya nuna shi yake rike da ita Captain ya zauna a jikin bathtub yana murmushi. Thank You, Thank You... Ka gano wanda ya dora hotunan? Shi ne ban gano ba, na yi bincike na biyeye abubuwan da suka kamata ban gane komai ba, amman na bibiye wandanda na ga hotunan a account dinsu na Facebook wasu unverified pages ne masu neman labari wasu kuma daidaikun mutane ne, sai da na bibiye wanda aka fi sharing hotunan da ya rufe wasu bangarora na jikinta sai na samu wani dan jarida ne a Kano, and na dauki wayarsa na fada masa daga ina nake kiransa kuma na tambaye shi a ina ya samu hotunan sai ya ce min a wani account ne, ya fara gani, dayan kuma a bauchi yake shi kuma yace min turo masa hotunan aka yi, na bukaci ya fada min account din da na bincika sai na samu an goge account din Kana aje wayar nan, ka duba list din mutanen da suka dora hotunan karka damu da yawansu ka turo min su, tare da sunanyen gidanjen jaridun, ka hado min da account number dinka Okay Sir Ya sauke wayar. Za su san sun taba mai gata, na miki alkawarin farinciki Hurriya zan cika miki shi... Ya fada sannan ya nufi madubin dake bandaki ya dora wayar ya cire tufafinsa ya sakarwa kansa shower. Ya bata minti arba'in a bandakin sannan ya fito yana rike da wayarsa jikinsa kuma na daure da tawul. Good Nafi'u Yayi forwarding sakon zuwa mabanbanta gurare sannan yayi waya da mutane daban daban. At the end ya kira Namra. Hello Captain Wace asibiti aka kai Adam? Kanen Salim Ban sani ba, ya jikanka? Bincika min yanzu Ya aje wayar ya dauki wani tawul din ya goge