Sashe 138
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dace kawai Amin Wannan karon Baaba Uwani ce ta amsa sannan ta mike tsaye ta bi bayan Gwaggo da ta fice dakin. Hindu ta daki cinyar Amma. Ke Wallahi ki koma dakin mijinki wannan kame kamen da yake ba na komai ba ne sai na neman aure, kin san yanzu aurensa ya koma kasa saboda kin cika idda dole shi ma ya shiga cikin manema, iyaka a nemi tsari kuma ki rike addu'a ba dare ba rana, ni kam da zaki bi yawa Wallahi Iyami karki bar mijinki, Gwaggo ma shi take so Amma ta kawar dai tana dauko wani zancen domin ita dai a yanzu har ga Allah bata son komawa dakin gidan Appa ita kadai ta san halin da ta shiga kamin ta samu kanta a yau. Kwana da yin haka Appa ya sauka gidan da kansa tare da wani dan'uwansa da Momy ya so a zo gidan sai dai yadda ta juya masa baya a lamarin auren nan ne ya saka dole ya aje lamarinta a gefe, Bappa da dake zaune a madaidaicin falo ya kalli Alhaji Haruna a natse sannan ya fara magana. Akan maganar da ka yi ne, ita Iyami tace tana ganin a tafi da kanwar Gwaggon yara wato Baaba Uwani da kuma kanwata Innar su Nasiru da Ibrahim dake can sokoto zan yi waya da ita ta zo sai ayi tafiyar da ita, da kuma Hindu, sai su ku duba kayan a tare da naka yan'uwan Appa ba haka ya so ji ba, domin ya so ayi tafiyar ne da Amma, kamar yadda yayi da Kaltume a lokacin da za su zabawa Maama kayan daki. Hakan yayi Bappa na gode sosai Allah ya saka da alheri, hakan ma wata alfarma ce, ina godiya Bappa kuma ina kara bada hakuri akan abubuwan da suka faru, ita kaddara haka take a yadda aka rubuta haka take zuwa, wani lokacin sai ido ya rufe hankalin ya gushe ka aikata abun da baka yi tunani ba, ba dan Allah ya rubuto haka ba Wallahi ban yi tunanin rana zata zo irin wannan ina raye ace bana tare da mahaifiyar Hurriya ba Haba wacan maganar ai duk ta wuce, sai dai ayi fatan Allah ya tsare gaba Amin Bappa Appa ya kalli dan'uwansa Alhaji Musa, Alhaji Muss na ganin kallon da Appa yayi masa ya fahimci inda ya dosa sai yayi hanzarin cewar. Bappa idan da hali ai sai a kira mana ita Iyami, akwai maganar da zamu yi da ita akan sha'anin bikin nan Toh babu matsala zan turo ta yanzu Bappa ya tashi ya fice daga falon da aka gina daga waje domin baki. Cikin gidan Bappa ya shigo ya zauna a kujerar roba dake aje kusa da Amma. Mun yi magana da shi na fada masa yadda muka yanke, yayi ta godiya kuma ya kara da bada hakurin abubuwan da suka faru A Duk lokacin da ya zo sai ya bada hakuri, shi kam ya fahimci mun hakura mana, gashi ana abubuwa gwanin sha'awa ma Ni ma dai shi na gani, daman shi aure ai ya gaji haka, tare da wani dan'uwansa ya zo shi yace suna son ganin Iyami akan maganar Hurriya, na fada masa zan turo shi Amma ba zata iya cewa ba zata je ba, domin Bappa ne mai fadar ya fada musu zata zo, ta ina zata ki umarnin mahaifinta, sai dai ita kam da za'abi ra'ayin zuciyarta sam bata son kebewa da Alhaji Haruna a yanzu, ba dan ta tsane shi ba, sai dan ta san maganar da zai fada ba zata wuce sake jaddada bada hakuri ba. Amma ta aje turen farin waken dake jikinta ta yunkura ta tashi tsaye ta nufi daki, Babba Hijab ta dauko ta saka ta fito ta saka talkamin ta kofar fita tsakar gidan sai kuma ta juyo kamar zata kira yaranta su tafi tare, sai dai gudun abun da Gwaggo zata ce ya saka ta juya ta cigaba da tafiyar. Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx Amma na yi sallama Appa ya mike tsaye yana amsawa kunyarta na rufe shi, ba yau ne karon farko da ya ganta bayan rabuwarsu ba amman yau ta fi cika masa ido saboda ya kebe ne daga shi sai ita sai kuma kanensa dake tare da shi a yanzu. Hajiya an wuni lafiya Iyamin da yake ce mata a da yanzu yayi masa nauyin furtawa duk da kasancewar ya girmi Amma nesa ba kusa ba. Amma ta amsa tare da zaunawa ta mikawa Alhaji Musa tasa gaisuwar. Lafiya Kalau Iyami ya hakuri? Ya gidan? Alhamdulillah, ya wajen su Larai? Lafiya Kalau suke, dan Allah Iyami a dai kara hakuri rayuwa sai da hakuri kullum kalubale sabo yake zama Babu komai Alhaji Musa an mun saba da jarabawa, Allah dai ya kara mana imani Amin amin haka ake so, Alhaji bari na jira a waje Ya tashi ya fice daga falon Amma ta bishi da kallo tana mamakin yadda yawancin yan'uwa suke goyon bayan hukuncin dan'uwansu a daidai ko kuskure, domin tun da suka rabu da Appa bab da Hajiya Binta babu wanda ya taba takowa a cikin yan'uwnsa da suna duba yaranta ko ita ko ya jajanta mata abun da ya faru, amman yanzu saboda Appa ne yake son zuwa gurinta da kansa gashi Alhaji Musa ya rako shi babu ko kunya ashe da rasuwa Appa yayi haka za su wofintar da Iyalinsa kenan! Bata samu amsar tambayar da ta yi ma kanta ba ta tsinkayo Appa yana fadar. Fatar dai duk kuna lafiya Ta maida kanta kasa ta amsa a takaice. Ina Hurriya? Tana can dakin Rukkayya kawarta Husna ce ta zo suna can tare Kallonta kawai yake sai a yau yake ganin ramarta, ta yi rama sosai tun daga lokacin da ta bar gidansa damuwa ta saka ta a gaba ciwo kuma ya rufeta sai ya abun ya zame mata biyu ga tunani ga ibadar ciwo. Sai dai ramar bata karawa Appa komai ba sai tausayinta da kaunarta a ransa. Bappa ya fada min hukuncin da kika yanke, zan iya sanin dalilin da ya saka kika cire kanki Tambaya yake kamar mai lallaba yaro. Babu komai daman ai abun da ya shafi an fari ko ar fari wasu ne suke shiga gaba su yi ba mu da muka haifeta ba, ni dai al'adar mu ta Fulani da Malam Bahaushe haka na sani Haka ne amman yanzu wannan ai duk ya kau Hajiyata, da dai za'ayi tafiyar nan dake zan fi jindadi Ba saboda kanmu zamu yi ba ai, ba dan jindadinmu ba, saboda yara zamu yi wanda su ne silar da ya saka na zauna a nan saboda Bappa ya fada min cewar kana son magana da ni akan Hurriya Appa yayi murmushi ya san halin kayansa ko a lokacin da take gidansa idan ta yi fushi bata iya ba. Hajiyata kenan, yanzu miye laifi idan na kiraki mun gaisa? Na san ba zaki fito ba ne sai da dabara shiyasa shi Alhaji Musa yayi haka, amman gaisuwa ce kawai Toh na gode Ta yunkura zata mike tsaye sai ya saka hannunsa aljihu ya dauko daurin kudi ya tashi a inda yake zaune ya isa gabanta ya aje kudin. Ki shigarwa Bappa da wannan Aa Bappa... Be bari ta karasa ba ya tare numfashinta. Ba na ki bane, balle ki ce ba zaki karba ba, na Bappa ne dan haka karki saka kanki a ciki idai ba kina jin wani abu a game da ni ba, Hajiyata a bar komai ya wuce mana, baki san iya damuwar sa faruwar abun nan ya haifar min ba, yadda Hurriya da yaran nan ma suke kallona wani abu ne da na kasa sauke nauyin da a yanzu nake jinsa, ban tana tunanin zamu kai ga aurar Huriyya ba ma tare da juna ba, amman haka aka rubuta mana dole haka din ne zai kasance Komai ya wuce Alhaji, babu amfanin ka yi ta nanata hakuri a duk lokacin da ka zo, ni na riga da na watsar da komai, daman shi aure ai kowa ya san Allah ya hallata saki a cikinsa, Hurriya ma da ka batawa gashi yanzu kana ta gyarawa yaran ma kanana ma yanzu kana jansu a jiki ai komai ya wuce Fata ma nake nan da wani lokaci kankane su koma gida tare da ni Na san kana da son yara Alhaji amman dai zaman a zai fi a kusa da ni ko Gwaggo A can din ma ai kusa da ke ne ke zaki rike kayanki Hajiyata har ma da wasu yayan idan Allah kaddara mana sai mu samu Amma na jin hakan ta fahimci gurin da Appa ya tafi ita bata je can ba, har a kasan zuciyarta ta san ta yafewa Appa kuma ta kawar da komai, amman zancen komawa gida a yanzu ko nan gaba ba abu ne da take da