← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 143

Sashe 125

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 44 Ni kaina ban yi farinciki da wannan auren ba, sai dai ba zaka iya nunawa Yaya ba ya fada maka ba daidai ba ko ma yace ba ka yi tunani ba, amman yarinyar sam bata dace da matar Jamal ba sam, sam sam Cewar Momy Ikilima a madadin ta kwantar da hankalin Ammy sai zugata take, Hajiyar Maru ce ta kawar da maganar Momy Ikilima ta hanyar nunawa Ammy ta karbi wannan kaddara ta so abun da danta yake so. Ba zan iya kallon yarinyar a matsayin surukata ba Hajiyar Maru, shi kansa zafin soyayya ne da rashin tunani yake dawainiya da shi, amman da zarar ya dawo hayyacin zai gane kuskure suka aikata shi da mahaifinsa Kamin su gane hakan, sai ki zuba musu ido ki ga yadda abubuwan za su yi, kin san dai ba zaki iya ja da mijinki ba ko? Ba zan iya ja da shi ba Hajiya amman ba zan karbi yarinyar nan a matsayin sukura ba Hajiyar Maru ta mike tsaye ganin ta yi iya nata ta fice ta bar ma Ammy dakin. Hajiya Turai ta dafe kanta tana kiran kukan da baya kusa da idonta. Sallamu Alaikum, daman ni na san ba da saninki Yaya ya aikata wannan abun ba, abun bakinciki abub takaici abun Allah wadai Momy ce take fadar hakan daga shigowarta dakin, Hajiya Turai ta dago ta dube. Ta ina zan yarda Captain ya auro yarinyar nan, Engr be yi shawara da ni ba, be fada min ba kawai yaje ya aiwatar da abun da zuciyarsa take so To wai haka kika hade hannaye suka zuba ido ba tare da daukar mataki ba? Matakin me zan dauka Hajiya Nafisa? An riga an daura aure me zan yi? Kin san dai Engr ba zai bari na cilastawa Captain sakin yarinyar a yanzu ba Momy ta zauna tana karkasa yadda bakincikin ya rabu mata gida gida. Har La'asar Hajiya Turai da Momy suna cikin dakin suna ta juya zancen, bayan saukowa daga sallah La'asar ne Daddy ya shigo dakin, Hajiya Turai ta dauke kai ta juya fuska sai dai hakan be hana shi zama kusa da ita ba, sai ma dariya da yayi yana tsokanarta a gaban Momy. Haba Turaita yar Baturiya yau kuma da Engr ake fushi? Momy ta kalli dan'uwanta cikin bacin rai ta ce. Dole Hajiya Turai ta yi fushi, abin nan ya wuce duk inda kake tunani Yaya, kuma ba a kyauta mata ba, ni ma kuma ba a kyauta min ba, na aikata abu ba tare da tunanin halin da zamu shiga ba, yanzu haka ko da na fito na bar Namra tana kuka saboda bakin auren nan da aka daura a yau da bakar yarinyar can, Namra da Captain suna kaunar junansu amman yanzu wannan auren da daura masa a yau ya lalata komai Da kamar mamaki Daddy yake kallon fitinanniyar kanwar tasa. Amman Jamal be taba gabatar min da wata magana makamancin haka ba a game da Namra, kuma ni na aikata abun da na aikata ne a yau saboda na gama karantar abun da Jamal yake so ne, sannan abun da kuke ta kushe yarinyar nan da shi koraren ne a gurin wanda ya san gaskiya, ni dai na ga video kuma yanzu haka shigowar da na yi a nan na zo ne da maganar Bashir Sarauta yana falo yana jirana yanzu haka Ai dansa ne ma ya dace ya auri yarinyar tun da yar'uwar badalarce, amman be nema nemawa dansa ba sai mu, kamar dai masu bakin uwa Daddy yayi murmushi yana kallon fuskar kyakkyawar matarsa take magana cikin kuka da fushi. Sheri ne aka yi mata Turai bata aikata ba, kuma ko da ta aikata tun da har danki yaji zai iya zama da ita a haka mu miye na mu a ciki? Ni dai ba zan karbeta a matsayin suruka ba, kuma ba zan bari ayi bikin komai ba domin ba za a yada hotunanta a matsayin matar Captain ba Daman daura aure dai shi ne wajib, kuma an yi, wadanna abubuwa ne da al'ada ta tana da, shi ma kuma idan bangaren yarinyar suka nuna sha'awar yin haka ba zamu hana su ba, ke dai a bangarenki ne ba zaki yi haka ba, ni ba tsegumi ya kawo ni nan ba, Bashir Sarauta ne ya zo tare da yan'uwansa da iyalinsa akan maganar yarinyar, da yi tunanin ko zaki so saurare a matsayinki na mahaifiyar Captain ko ba komai haka zai share zargi da rashin ganin kimar yarinyar nan da kike yi, amman yanzu na fahimci baki bukatar hakan Ya kalli agogon dake daure a wuyan hannunsa. Ki shirya na fada miki jirgina zai tashi 5pm na yamma Babu inda zan tafi na tafi na bar yarona a nan da wannan yarinyar nan, idan na bar garin nan sai idan tare da amaryar ne Daddy yayi murmushi. Amaryar da kika ce baki so? Ayi haka? An dai riga an daura aure yanzu a ba mu amaryarmu mu tafi da ita Kaduna? Ina aka taba haka? Daga daura aure yau babu kintsawa babu komai sai mu tafi karbar Amarya kuma mu wuce da ita Kaduna? A kaduna ina zata zauna ma? Ai dole mu ma muna bukatar lokaci ba yanzu yanzu ba Duk gidanjen da suke garin Kaduna ace ba a san wanda zata zauna ba? Kai kace wata yar zinari? Tarin gidaje ba shi ne mafitar ba, sai wanda mijinta yake sha'awar su zauna tukuna, wannan ma na aikin mu ba ne, ta ina ma za a dauki amarya akai a Kd bayan mijinta yana nan garin Gusau yana aiki, tare da mu zata zauna ni ba zan iya bari saboda Captain yayi aure ya zauna a gida daban, shi kadai Allah ya ba ni ba zan bari wata ta kwace min shi ba Daddy yayi murmushi ya dauke kai ya fice daga dakin, shi dai duk a tunaninsa Hajiya Turai take tana yi ne saboda ranta a bace, idan aka bata kwana biyu zata sauko ta. Wallahi ba zan taba bari ayi zaman auren nan ba, ba zan bar garin nan ba sai da yarinyar nan Bayan Daddy ya fice Ammy take fadar haka, Momy ta mata kallon rashin fahimta. To ai idan kika yi haka kin nuna kina sonta kenan, ai kamata yayi ki banza ajiyarta ki share yar banza ta fahimci familyn nan ba gidan aurenta ba ne Shiyasa zan yi haka ai, idan na barta a nan cikin satin nan zata iya tarewa, idan kuma ta haihu da ana ai zance ya kare, ina nan garin idan kuma ta tare sai dai ta tare a gidana Wannan ba mafita ba ne lokacin da zai saci kafa ya tafi mai nawa ko gani be yi ba, ki dai canja shawara Ammy ta juyo ta kalli Momy kamar zata fasa kuka. Momy ta yi shiru domin ita ma bata san abin yi ba a yanzu kanta a rufe yake. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un wannan abu da me yayi kama? Wane irin rayuwa ne wannan? Ni na rasa ma me ye abun yi, babu abun da yafi min bakinciki kamar neman auren yarinyar nan da aka yo a cikin falona kuma aka yo sadakinta da sinari Zinarin ma mai tsada, yarinyar ko gani bata yi. Amman ni na san abun yi ni na sani, ta yaro ai kyau take bata karko Ammy na maganar zuciyarta na kuna, kamin ta mike tsaye ta nufi bangaren da mijinta yake sauka idan ya zo gidan. Daddy yana fitowa daga dakin ya hau sama ya shiga dakin Captain kicibus suka yi da Daddy shi zai fito Daddy kuma zai shiga dakin. Daddy Captain ya fada yana sauke idonsa saka haka nan dai yake jin kunyar Daddy a yau. Kai ba mace ba miye na rufe kai a daki? Ko Ammy kake yi ma boyo? Captain yayi murmushi yana sosa bayan kansa. Daddy ya ce. Mahaifin yaron nan ne Adam ya zo tare da Iyalinsa, ya fara koro min bayana na takatarda shi saboda ina ganin kai da mahaifin yarinyar ne kuka dace da yin shawara ko yanke hukunci A take bacin rai ya mamaye zuciyar Captain da tsananin fushi ya ce. Me suka zo yi Daddy? Kamata yayi ka sauko mu ji, bana son bata lokaci 5pm zan wuce Kaduna Daddy ya karasa yana duba agogo hannunsa, a tare da Captain suka sauko, a tunaninsa iyayen Adam din za su sake bukatar ya basu dansu ne ko kuma wani abun da ya shafi karar da ya shiga a DSS. Captain be ji zai iya gaisawa da ko daya a cikin family ba domin dan su ya janyo musu kallon marasa mutunci yake musu. Salim be kalli gurin da Captain yake zaune ba domin kowa baya marmarin ganin abokinsa a yanzu. Sai da Daddy ya kalli Captain da fuskarsa take a gintse sannan ya ce. Ina tunanin kun san Captain, ko da iyalanka ba su sani ba kai dai ka san da cewar Jamal ana ne, Salim zai iya fadar hakan, dalilin da ya saka na dakatar da kai daga bayani saboda na kira shi ne, domin shi da mahaifinta suke masu hakkin akanta yanzu, kasancewarsa mijinta an daura Aurenta da Jamal a yau...! Da matukar firgici Salim ya kalli Captain da goshinsa ke kyalli kana arba da shi zaka san ango ne latest. Kallo kallo suke da Salim kowa ya kasa dauke idonsa. Maa Shaa Allah, abu yayi kyau Allah ya saka maka da alheri a wannan jihadin da ka yi, kuma ya baka wuyan dauka Cewar Bashir Sarauta yana jinjina kokarin Captain na toshe kunnuwansa a wannan mawuyancin yanayin da ba kowa zai iya ba. Salim ya dauke idonsa da mugun karfi ya mike tsaye fuuu ya fice daga falon Zaka iya cigaba ko kuma ka fara daga farko saboda ya fahimci me ke tafe da ku Alhaji Bashir ya kalli Captain cikin yanayin damuwa ya ce Daman mun zo nan ne akan maganar abun da ya faru da ne yi ma kowa dadi ba, DSS sun sanar mana su suka dauki Adam sakamakon karar da Captain ya shigar, sun ce sun dauke shi ne saboda bincike yanzu haka dai sun dawo da shi yana asibiti
Chapter 125 · 0% Book details