← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 143

Sashe 102

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a tsakanina da ke ne kawai Hajiya Fatee In Shaa Allah babu wanda zai ji, daman ba komai ake fadawa yara ba, amman dai tun farko ke kika yi sake Hajiya ga wanda ya saba miki aiki kika tsallake kika tafi gidan malaminta Kina da gaskiya wata kila malaminta ne, ko kuma malamin Nafisa ba, ita yar aikin ta hada kai a cutar da ni, aiko sai na ci ubanta idan abubuwa suka daidaita, dan Allah ki kara ba shi hakuri ga kudin nan za a tura masa a account ayi aikin da yace duk abun da ya dace ayi Da kaina zan yi magana da shi kamar yadda na yo yanzu, kuma ina tabbatar miki Alhaji a haukace zai zo ya maida ke kuma ya gyara duk kuskurensa, aure kuma ba za'ayi ba Iyami da yayanta kuma sai labari a gidan nan Haka nake so, Allah ya bar kawancen mu har aljanna Cikin yanayin damuwa da muryar rashin lafiya Hajiya Kaltume take karfin hali tana amsawa Hajiya Fatee. Ameen Ameen ai komai zai daidaita, bari dai Malam ya fara aiki ki gani ke ma ai kin san irin aikinsa Na sani kaddara ce ta kai ni gurin bokan Iyami, ko na Nafisa, wannan aure aure na Alhaji yana haifar min da masifa, kuma har yake son dauko wata saboda rashin tunani irin an namiji, su da sun ji suna da kudi ba zama lafiya sai aure, dan Allah ki ce Malam ya daure shi daga aure nan a hana shi aure ko bayan na mutum... Haka za'ayi, domin wannan yarinyar da yake son daukowa ma daga ganinta ita ma a tsaye take, kara a hana ta shigowa tun wuri Hmmmmm Alhaji ya ba ni mamaki Cewar Hajiya Kaltume tana girgiza kai... Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 34 Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660 Hajiya Fatee bata bar gidan ba sai da Khairy ta dawo daga bank ta tabbatar mata da cewar ta yi transfer kudin zuwa asusun Malam. Toh Allah ya miki albarka, ku kwantar da hankalinku da yardar Allah komai zai wuce Ameen Hajiya Ta amsa sannan ta mike tsaye ta fice bayan ta ajewa Hajiya Kaltume ATM dinta a kan gado. Hajiya Fatee ta dauki Hijab dinta ta saka ta mike tsaye tana rike da jakarta. Ina isa gida zan kira na fada masa an saka masa kudin, kuma yace da zarar ya saka hannu aka fara aikin nan da kwana uku komai zai daidaita Allah ya nufa Hajiya, wannan bakincikin kar ya kai ni Komai dai wuce, bari na tafi kar yamma yayi Toh na gode Allah ya bar zumunci Ameen Allah kara lafiya Ta fice daga dakin, Hajiya Kaltume ta gyara zamanta zuciyarta na mata mugun ciwon, idan ta tuna yadda Appa ya wulakanta sai ta ji kamar ya hade zuciya ta mutu, idan har bata hana auren nan ba kuma ta hana Amma da dawowa gidan tabbas ita din ba mutum ba ce, sanadin su komai ya faru, bayan rasa yarta ga kuma saki da Appa ya dankara mata sai kuma wulakanci ya biyo baya,ya kwatanta mata irin abun da yayi ma Iyami lokacin da ta haifi yan biyu. Cikin tsananin damuwa ta dago ta kalli kofar dakin da aka bude, Ruma ce ta shigo tana rike fa plate din abincin da take ci. Hajiya ga Momy nan da bakuwarta... Rufe bakinta yayi daidai da shigowar Momy tare da Hajiya Turai a dakin. Hajiya Kaltume ta gyara zamanta da sauri tana jin kunya na rufeta, kunyar sakin da Appa yayi mata bayan ta gama nuna karfin iko da isa a gidan, ga kuma jinyar da ta yi asibiti be je ba Hajiya Binta bata je ba haka ma Momy bata leka ta ba, har wata zuciyar na raya mata da ganganci suka shigo. Daga bakin kofa suka tsaya Hajiya Turai kamar mai kyamar dakin har da dage riga. Sannu da jiki Kaltume, Hajiya Nafiss ta ce min kwanan baya ma yarki ta rasu, sannun Allah ya mata rahama Hajiya Kaltume ta kalleta ta san wacece ita, yanayinta tufafin jikinta da gwagwalan dake wuyanta da hannunta sun wuce ta yi mata irin haukar da ta yi ma Maryam da Rukayya, hausawa suka ce wasa guri take samu. Dan haka ta amsa mata da lalama sai dai babu sakewar fuska. Amin na gode Hajiya Turai ta juya ta fara fita sannan Nafisa ta bi bayanta daman ita tun da aka shigo uffan bata cewa Hajiya Kaltume ba. Samun guri, wato kawota kika yi ta gan ni ko? Saboda yanzu ke ce kadai matar gida, ai Wallahi ko da ace Alhaji ba zai maida ni ba to sai dai duk abun da na tara ya kare shi kuma ba zai sake zama da mata ba har abada Tana maganar wani mugun abun zuciya na taso mata bakinciki yana neman yi mata yawa. Ita ma wannan Nafisar ba kaunata take ba, ko a leke bata leka ta duba ni a asibiti ba, ko da yake uban gayyar be tafi ba ita yar rakiya ya za'ayi ta tafi Ta yi kwafa ta girgiza kai. Tabbas na yi sake, da na san haka zai faru da ban tafi gurin wannan bakin bokan ba, gashi Iyami bata mutu ba yata ta mutu Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Allah sarki Salma Ta fashe da kuka mai karfi tana jin kamar ace zata iya dawowa da ita. Momy ta jero tare da matar Yayanta Hajiya Turai suka nufo bangarenta, Hajiya Turai dake murmushin kasaita ta ce. Sakin daya ma ta ya rage zai karasa mata shi nan kusa ki koma ke kadai, ban da rashin sanin darajar kai har yaushe namiji zai sake ka zauna a gidansa wai zaman yaya? Ba sai ta tattara ta koma gidanta ba ta tare, idan ma yana da ra'ayin maida aurensa sai ya same ta a can Ah to ke ma dai kya fada, ai haka na fada ni ma yaya dai da wayonsu ta bar su a gidan ubansu ko ta tafi da su duk daya, ni dai ba zan sake yarda a dauko wahala a kawo min ba, ga Hurriya nan har yanzu ban haife cikin bakincikinta ba Hajiya Turai ta dafa Momy. Ai kin yi kokari, ni zan iya rika kowa ban da yaran miji, shiyasa kullum nake godewa Allah da ya miji ba mutum ne mai aure aure ba, kin ga da mai wannan kwashekwashen ne da yanzu ya karo aure ko dan haihuwar nan da ta tsaya mana, amman duk be kula wannan ba, gashi yanzu girma har ya kama Wallahi kin huta, daman zuri'ar duk ba mu da wannan rayuwar ta son aure auren mata Allah yasa yaran mu su gado mu Amin, da alama kam Captain ma ba zai yi irin wannan rayuwar ba Hajiya Turai ta yi murmushi masu nairori. Captain wanda auren farko ma ya gagareshi, ina maganar kari? Na farko ma yana kusa, domin yanzu na lura kamar hankalinsa ya karkata gurin Namra kuma sai dai mu saka musu ido mu ga gudun ruwansu kamin mu ga abun da Allah zai yi Oh yanzu na gane dalilin da yake fada min cewar na kusa samun suruka, amman be fada min ko wacece ba, har nake ce masa ko da ka jitu da ita ai abun baya daurewa, sai ya ce min wannan kam idan har na ga be aureta ba to baya raye, amman ko naman jikinsa take yanka ba zai rabu da ita ba Momy ta yi murmushi zuciyarta na kara jaddada mata Namra ce. Toh Allah yasa, zaman da yake a garin nan yanzu gaba daya hankalinsa yana gidan nan komai aiki yayi masa yawa sai ya leko gidan nan Aiko zan jidadi idan haka ta faru, daman abun da muke fata kenan, wata kila idan ya dawo daga tafiyar nan zai gabatar min da ita Tafiya yayi? Eh tun last week yace zai tafi Abuja? Oh Allah sarki daga Kaduna ya wuce Abuja? Aikin na su ne ba zama Aa be zo Kaduna ba, daga nan Gusau ya wuce yace min sati daya zai yi Momy ta jingina jikin Range Rover din aka tuko Hajiya Turai tana mamaki. Ni kuwa ce min yayi Kaduna zai tafi Aa gaskiya Abuja yace min, tun last week jiya ma da muke chat da shi yake ce min ya kusa dawowa Wata kila kuma ban ji daidai ba, ko kuma an canja tafiyar tasa ce daga Kaduna zuwa Abuja Maybe Daga haka suka yi sallama da Momy, Dreban ya bude mata mota sai ta shiga ta zauna ya rufe Momy ta daga mata hannu ya ja motar. Momya ta
Chapter 102 · 0% Book details