Sashe 13
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mijin mata? Ina laifi ki rumgume talaucinki ki shafawa kanki lafiya, yanzu wa gari ya waya...? Mu hadu da ku page din gobe, amman kamin nan ina son na ga Comments baza-baza line by line in ji Bature... [10/18, 5:35 PM] Nana 1: Ana kiran sallah asuba ta sauko daga kan gadon ta nufi kofar dakinta ta bude ta fito, a hankali ta sauko downstairs, tana isa bakin kofar falon bata tsaya komai ba ta kai hannu zata bude kofar. Ina zaki je? Ta juyo da sauri domin bata yi tsammanin wani zai iya fitowa at this early ba. Fita zan yi Ta amsawa Namra. Cikin mamaki Namra ta wara ido. Asuba ne fa Na sani, Hijab zan dauko na yi sallah Haba Hurriya shiga dakina ki dauko nawa mana, saboda Hijab sai ki fita tun a asuba ki koma part dinku kamar wata bakuwa, ke a gida kike fa Hurriya ta dan sauke kai kasa daga barin kallon yayarta wadda ta bata shekara uku da haihuwa. Namra bata sake ce mata komai ta nufi kujerar da ta zauna a jiya ta dauki agogonta da assignment din da ta yi, sai da ta kusa hayewa sannan Hurriya ta rufa mata baya, cikin ladabi da natsuwa ta shiga dakin Namra ta tsaya jikin kofa, haka Hurriya take bata sakewa da mutane tana da wahalar sabo, musamman idan ta san zaka tsangwame ta ko ka yi mata fada. Namra ta juyo ta jefo mata hijab din cikin hanzari Hurriya ta cafke. Akwai carpet din Sallah a can? Aa babu Namra ta dauki nata ta jefa mata Hurriya ta sake cafkewa ta juya ta fice daga dakin zuwa dakinta. Bata shiga nata dakin ba sai da ta kwankwasa kofar dakin Hamad tana kiran sunansa. Na tashi Ya amsa mata daga can ciki, sannan ta wuce dakinta ta maida kofar ta rufe. Tun bayan da ta yi Sallah bata sake fitowa ba sai da ta auna lokacin makaranta yayi mata, sannan ta bude kofar a hankali kamar wata bakuwa ta rufe ta nufo hanyar saukowa kasa gabanta har faduwa yake kar ta hadu da Musib ko dan'uwansa Miwan balle kuma Momy da ta san bata ishe ta kallo ba. Sai dai ta yi rashin sa'a Momy da duka yaranta suna falon zaune, abun da bata saka tsammani ba domin Momy bata tashi da wuri sai idan tana bangaren Appa shi ma da zarar ta kai masa abun karyawa zata sake komawa bachi kuma babu mai tashinta sai gidan maigidan ne da kansa if not kowaye ya tasheta zai gane kurensa a ranar. Baka fada min zaka zo ba, ai da na saka an shirya mana abinci mai kyau Cewar Momy tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune a kujerar dake facing nata, kyakkyawan saurayin farin saurayin mai jini a jika ya girgiza mata kai yana duba agogo hannunsa. Noo Momy na gode tafiyar ta gaggawa ce, yanzu zan kama hanya, kawai na ce bari na biyo mu gaisa ne Momy ta yi murmushin kasaita irin na manya mata. Daman na sani, abinci idan ba na Hajiya Turai baka ci na kowa Ya dan fadada fuskarsa da murmushim da ya kara masa kyau da haiba yana daga kai ya kalli Hurriya dake saukowa. Momy ta dan juya ta kalleta kadan ta dauke kai irin ba ki isheni kallo ba din nan. Momy ina kwana Hurriya ta gaisheta cikin ladabi Momy har ta yi kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ci albarkacin bakonta amsa ciki ciki kamar an mata dole. Yaya Musib ina? Ya amsa, ta juya gurin dan'uwansa shi ma ta gaishe shi, sai ya amsa mata fuska a sake kamar dan'uwansa, ta kalli Namra ta gaishe ta kamin ta rufe baki Namra ta amsa tana mata an tashi lafiya, daga karshe Hurriya ta cike gaisuwarta da bakon da take kyautata zaton yana da muhimmanci a gurin Momy da yaranta ganin yadda suke ta murna da ganinsa kuma suka fito dukansu da sanyin safiyar nan suka zauna a falo just because of him. Ina kwana Ya d'auki 'yan dak'ik'u kafin ya amsa gaisuwarta, shi ma kuma ba da baki ba kai kawai ya daga mata and light smile. Binta yayi da kallo har ta wuce ta gabansa ta nufi kofar fita. ar Mijina ce, kanenta ne ka ga ya fita dazun Momy ta fada masa domin ta san ba zai tambaya ba, ta san kallon da yake mata be wuce na neman sanin wacece ba, dan zuwan da yake gidan jefi jefi be taba ganinta ba, haka ma bata yi masa kama da masu aikin Momy ba balle yace ko yar aiki ce, ba zai ce ya san kowa a gidan ba, amman yadda ya san familynsu musamman Momy idan har ta bawa wani damar shiga ma a falonta to yana da muhimmanci a gareta, sai dai abun da be sani ba wannan shigar ta dole ce ta cilastawar Appa ba dan Hurriya tana da muhimmanci a gareta ba. Yaya ance an daga bikinka Miwan ya tambaya yana kallonsa. Mutumen da Miwan ya kira da Yaya ya juyo ya kalleshi. Ka aje wannan Yaya aside ka kira ni da real sunana Jamal Momy ta yi murmushi mai sauti. Haba dai Captain dukansu fa kanenka ne ta ina za su iya kiranka da sunanka kai tsaye, dole sai da girmamawa Wallahi na tsani wannan Yayan na fi son a kira ni da sunana na gaskiya Ya amsa mata da murmushi sannan ya mike tsaye sai zuba kamshi yake. Namra ta mike tsaye kamar sauran yan'uwanta tare da fadin. Tafiya nan da nan Yaya ba zaka dade ba Da hannu ya nunata. Yanzu na gama yi ma Miwan gargadi shi ne ke ma zaki ana ko? Sai duk suka saka dariya ban da shi da ya nufi kofar fita yana yi ma Momy sallama. Momy ta mike tsaye ta rako shi har bakin kofar falon Miwan da Musib suka karasa gurin da ya faka motarsa suna masa a sauka lafiya, Momy da Namra kuma na tsaye jikin kofar har sai da ya shiga motarsa yayi musu horn ya fice sannan suka dawo cikin falon. Captain baka iya masa, Allah kadai ke masa daidai, komai ka yi sai yace ba haka ba ga zuciya abu kadan ya fusata shi Ai gaskiya Ammy tana hakuri da shi Cewar Namra Momy ta ce. Toh ya zata yi haka Allah yayi shi, kuma shi kadai ya bata daga ita har Yayana magajin da suke da shi kenan Kuma Allah ya hada jininsa da ke, duk ya zo garin nan sai ya zo nan Kin ji Namra da wata magana, uwa daya uba daya ai ta wuce wasa, ko kin manta alakata da mahaifinsa ne, ga kuma Hajiya Turai a bata da kawa a familynmu sai ni Duk da haka dai Momy, Wallahi idan baya ra'ayinki ba zai zo ba, ba ke kadai kuke uwa daya uba daya da mahaifinsa ba amman ke kadai ce yake zuwa gurinki, duk ya zo gurinsu Hajjo sai ya zo nan, waya ma akai akai yana yawan kiranki Haka kuma da maganarki, je ki taso masu aikin nan yau muyi tashi dole su zo su fara aiki, ke kuma ki shirya ki wuce makaranta Okay Ta amsa sannan ta nufi sama, Momy ta dasa hirar da su Miwan. Ku yaushe zaku koma hutu ne wai? January nan zamu koma, ni ai gaba daya na samu na bar garin nan na huta Musib ya ce. Kai gari kake son bari, ni Wallahi kasar ce ya isheni, ba dan halin Appa ba kamar mu zai hana a fitar waje, maza ne mu fa kuma yawanci yayan sa'ainsa duk suna waje suna karatu amman ya hana a fitar da mu kuma shi ba zai fitar da mu ba Jami'ar nan kawai zaku kare a nan, amman masters da duk wani abu da zai biyo baya a waje zaku yi shi, na gaji da halinsa shi har yanzu be gama jefar da wannan halin nasa na da can ba, kuma a yanzu tun da na fahimci baya bin ra'ayi toh kowa yayi nasa ra'ayin kawai, duba yadda ya daga mana hankali jiya saboda kawai Hurriya ta zauna a nan Wai me yasa ba zata bi mahaifiyarta ba? Kai kana ganin uwarta zata yarda ta bita su zauna a can? Ai ba zata yarda ba tana ganin ga gidan arziki Toh ai ko da sun koma Appa zai mata komai Musib ya sake fada. Amman dai ba kamar idan tana gidan nan ba, kuma Kaltume ba zata yarda Alhaji ya yi haka ba, yadda ba ta bar shi ya kula da yarsa Sapna ba haka ba zata bar shi ya kula wadannan yaran ba matukar suka bar gidan nan Miwan ya ce. Wai Momy saki nawa yayi mata ne? Ina ruwana? Balle na tambaya can ta matse musu idan uku ne sun hutu, idan daya ne ma ya dawo da ita duk ruwansu ne ba nawa ba, ni ta harkokin gabana nake shirya ba a kaina take zaune ba, daga ita Iyamin har Kaltume babu wadda zata nuna min komai gaba da baya, mu da talauci sai a baki shi ma dan ambata kawai, su ko babu wadda bata tashi a cikinsa ba, ni ko babu wadda be san ubana ba a garin nan ba Ai shiyasa Hajiya take shakkarki, yadda take ma Amma da yayanta bata mana haka Ai bata ga fuska ba ne, ita kanta ta san na fi karfinta ta ko'ina, kuma ni bana jiran abun Alhaji ita da Iyamin dai suka dogara gareshi Hira sosai suka yi ta yi Momy na koda kanta a garin gusau ma jin take ba ko wace matar mai kudi ce sa'ar yinta ba balle kuma cikin gidan Alhaji Haruna Mai Yadi. HURRIYA POV. Tana shiga part dinsu sai kewar Amma ya kara daduwa a ranta, ta san da a jiya ne da kwanakin baya da Amma take gidan sai dai ta fito daga dakinta ta sauko kasa ta yi breakfast ba dai taje wani bangaren ta kwana ba har tana fargabar arba da Momy. Kujera ta nufa ta zauna ta rike hannayenta hawayen dake idonta suka zubo mata. Huriyya... Ta kalli kofar kitchen din da sauri tana zabura domin ta