Sashe 70
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan mai ba da jimawa ba Kuma Appa zai yarda? Me zao hana shi yarda? Nafisa ma ba kasuwancin take ba? Ina ce nan take siyar da sinari a shagonta ga kuma shagon aski da na gyaran jiki da na cin abinci da take da shi a garin nan, babu mai kalar shagunanta, sai kuma yace zai hana ni? Ai ba zata sabu ba Toh Allah yasa albarka kuma ya hadaki da mutane na gari, amman ki kula sosai da wanda zai kula miki da abubuwanki Amin, ai kai nake son ka zama shugaba No ba zan iya ba, harkar kasuwanci ai sai Appa, ni ko zan iya sai nan gaba, yanzu akwai abubuwan da suke gabana? Aure? Tun da na san ka gama karatu kuma kana aiki Ya daga mata kai. Aure Hajiyata Wacece to? Da har kake tsoron iyayenta su ki karbarka? Ai babu yarinyar da zaka so a garin nan ita ko iyayenta su ce maka a'a Ya karkato ya fuskance da kyau. Har da Rukayya? Ko Wacece kuwa, amman wace Rukayyar? Sai da yaja dogon numfashi ya aje ya sauke idonta saka dan kar ya hada ido da Hajiya Kaltume sannan ya bata amsar tambayarta Rukayya yar wajen Bappa Ka kara batar da ni a duhu Yar wajen Gwaggo, kanwar Amma, little mom din Hurriya... Eeeehhh..... Hajiya Kaltume ta dage hannunta da sauri matsa can baya kama wanda ta ga abun tsoro. Ba a gidana ba, da yardar Allah ba a gidana ba, duk wani sihiri da suka ma mahaifinka ya kama shi har Iyami ta aure kai kam ba zai kama ka ba, Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, yau na ga bala'i ganin ido... Rukayya kuma yarinyar da ta fi Iyami rashin mutunci da raina mutane? Haba Yasir duk matan duniya ka rasa waye zaka so sai jinin Iyami? Yasir ya mike tsaye. Jinin Amma me ye matsakarsu? Suna da tarbiya suna duk wani abu da ake nema a gidan mutunci, meye matsalar Rukayya Bana sonta Yasir, ni da jinin iyami har abada, Hurriya ma rokon nake Allah ya raba ni da ita balle kuma ka dauko min wasu yan baki gida, ba ni ba yan baki gida har abada, kai kanka ba a banza suka barka ba Komai dai na magani ne a gurinki Hajiya, kin ce Amma ta mallake Appa da mallaka ce me zai saka ya saketa? Ni dai In son Rukayya kuma ita za aura, matsalata a yanzu na yadda iyayenta za su karbe ni ba, ba kuma saboda kowa mai sai dan ke Hajiya Ya bar dinning din ya nufi stairs ransa a bace, sometimes ya kan gane kan mahaifiyarsa, ita kam binsa kawai ta yi da kallo zuciyarta na karanta mata cewar ba a hayyacinsa yake wannan maganar ba. Irin abun da aka yi ma Appa ne aka yi masa, wato son suke ta ko'ina su mallake mata da da miji. A ranar da tunani ta kwana washe gari Sallah asuba kawai ta yi ta dauki wayarta ta kira Hajiya Fatee ta fada mata abun da ya faru, kamin ta kira Malaminta ta gabatar masa da bukatar. HURRIYA POV. Kafafuwanta a nade fuskarta kuma dauke da kayataccen murmushi take kallon Amma dake cin abinci da kanta, duk kuwa da kasancewar hannun nata rawa yake rabin abincin na zubewa, abun da bata iyawa tun a lokacin da ciwon ya same ta, gaba ta tisa Amma tana ta kallonta kamar zata cinyeta tsabar murnar mahaifiyarta ta fara samun sauki. Bayan Amma ta gama, Hurriya ta dauke plate din da cup din ruwa ta fitar sannan ta dawo ta zauna kusa da Amma. Allah na gode maka da ka fara bawa Ammata lafiya Amma ta yi murmushi domin shi ne kadai abun da take iya yi Idan farinciki ya same ta, idan kuma damuwa ce sai dai ta yi kuka, saboda bata iya magana, tana da abubuwa da yawa a zuciyarta da take son ta tambayi Hurriya amman babu baki, ita kuma Hurriya bata yarda ta yi hirar gidansu da ita, domin ba abubuwa masu dadi ne zata fada ba, ko da Gwaggo ta tambaye ta, ba zata fada ba sai dai tace tana zaune kalau. Cikin wani yanayi na tausayi da kauna da soyayya irin ta uwa zuwa ga yarta Amma ta mika hannunta dake rawa ta kama hannun Hurriya idonta na cika da hawaye.. Minene Amma? Bana cikin damuwa a yanzu, Appa ya maida ni gurin Hajiya Binta, kin san yadda take so na ai, ita tace min na shirya na zo nan na wuni, saboda na kwana biyu ban zo ba, ashe zan zo na farar da farinciki ne, gashi na ganki Amma kina cin abinci Tana maganar tana sharewa mahaifiyarta hawaye a idonta. Twins din Amma suka zo da gudu suka kwanta jikinta suna ta son yin fitina, da Amma ta kallesu sai ta ga sun hadu su uku babu daya, da Hamad yana raye da yanzu yayanta sun cika hudu cif. Hurriya yau ji take kamar ta cinye Amma saboda murna? Hurriya ta saka dariya tana kallon Rukayya dake taje kanta. Mama Rukayya da kun fada min Amma ta fara motsa hannunta da sai na saci hanya na zo Shiyasa ai ba a fada miki ba, ki saci hanya ki zo nan wannan Kalwar ta hada ki da Appanki, kin ga wannan mai fuskar yan wuta kiris ya rage ta shigeta, na tsani kamar nan kamar mutuwata Yanzu ai bana gidanta na koma gidan Hajiya, kin ga zan samu sauki, Hajiya bata hana ni zuwa ko'ina balle ma kuma idan nan ne To ya aka yi kika koma wai? Ita ta rarrashi Appa kuma ya yarda Wata kila ta ga wahalar da kike sha a gidan ta miki yawa ne Hurriya dai ta yi murmushi bata sake cewa komai ba, domin bata son a zafafa a maganar. Bayan sun yi Sallah la'asar ta fito tsakar gidan ta zauna tare da Amma, twins kuma suna ta wasansu kamin ta su fado kanta saboda tsokarnasu da take, sai aka jone ita da su aka rasa waye karami, ita da kurciyarta bata gama fita jikinta ko kuma su da a yanzu suke tasowa. Ana daf da fara kiran Sallah Magariba, Hurriya ta shiga ta dauko hijabinta da jakarta domin sun yi da Hajiya Binta zata wuni a nan ammam ba zata kai dare ba. Gwaggo zan tafi, Hajiya ta ce kar na yi dare Toh kin koshi dai ko? Idan kuma kina son dan'waken ki tafi da shi Aa na koshi a bawa yan biyu a ciki Sai suka saka dariya yana mulmula kan katuwar tabarmar da Gwaggo ta shimfida. Hurriya ta kai kasa tare da kai bakinta a goshin Amma ta sumbanci, goshinta ta sumbanci gefen fuskarta dama da hagu. Ina sonki Ammana Allah ya baki lafiya Amma ta yi murmushi tana binta da kallon da raunataccin idanuwanta. Gwaggo ta kalli Rukayya dake hankalinta ke kan waya ta ce Ba zaki rakata ba? Ke dai kullum kina nan a waya, sai ta saka ki hauka idan baki yi hankali ba Rukkaya ta kyalkyale da dariya. Gwaggo littafi ne nake karantawa na Khadeeja Candy, mai suna Mairo wai an bata apple ta ce a kara mata gorar binni, wai yan binnni gorabar taushi ne da ita Kyaje can ta shirmenki, kullum ai cikin karatun littafi kike, tashi ki karata ta samu Napep Rukayya ta mike tsaye har lokacin dariya take, sai da ta shiga ta aje wayar ta sako hijabinta sannan ta fito tana gyara talkamin kafarta. Mu tafi yar gidan Gwaggo, ke ko kishinki bata yi sai fada take min ban raka kishiyarta ba To idan ma ba yar wuta ba, wace kishiyar ce zata yi kishi da Hurriya baiwar Allah, kifi musulmin nama Hurriya ta yi dariya, ita kanta Gwaggo dake maganar dariyar ta yi, kamin ta raka da addu'a, Amma kuma ta bita da kallo tana dan murmushi kadan. Tare suka isa da Rukayya har titi suna tafe suna hira, Rukayya sai tambayarta take wai halin Hajiya Kaltume na nan ko ta daina. Me zata daina kuwa Mama Rukayya ni dai arzikina, daya bana gidan yanzu duk wani abun da zata fada ko ta yi ba zai shafe ni ba Wallahi kin huta, ai kara da Hajiya Binta ta dauke ki, kika rabu da wannan bakar kalwal mai bakar zuciya Hurriya ta kalleta tana murmushi. Amman dai Mama Rukayya wasa kike so? Hajiya fa mahaifiyar Yaya Yasir ce And so what? Ke baki ga yadda ta maida Amma ba? Ta mallake Appanku baya jin maganar kowa sai nata? Ni fa da zan samu sa'arta sai na dauko fansar duk abun da ta yi mana, saboda tana tsaye nan a makoshi? Toh kuma ki yi Yaya da Yaya Yasir? Wai ke ina ruwanki da Yasir din ne? Ke fa wata rana kamar munafuka haka kike Hurriya bata san lokacin da dariya ta subuce mata ba. Mama Rukayya ke dai yi a hankali, dan kin san Yayana fa, shi yake zane mu idan muka yi laifi To ni sai ya dake ni? Ke yarinya kama kanki, ai ko kirana yayi ban daga ba sai kin ga yadda hankalinsa yake tashi, idan kuma ya zo ya karbi wayata ko ya gan ni da wani ya fara kishi kenan, ni Rukayya i no dey carry last, haba ni ba halin Amma ne da ni ba, kowa ya ce min kule chasss zan ce masa A karo na barkatai Hurriya ta yi murmushi, ta tsayar da mai napep ta shiga bayan ta fada masa unguwar da zai kaita. Toh Allah ya tsare, damo sarkin hakuri Amin Mama Rukayya na gode Mai napep yaja suka dauki hanya. A bakin gate ya sauke ta ta ba shi kudinsa sannan ta shiga cikin gidan, tana yin arba da daya daga cikin motocin da mahaifinta ya fi yawan hawa gabanta ya yanke ya fadi, tun a nan ta fara rage tafiyarta, hakalimlnta be tashin ba sai da ta kunna kai cikin falon ta yi arba da Hajiya Kaltume da Appanta, Hajiya Binta kuma tana zaune saman kujera. Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon