← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 143

Sashe 120

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aura dan baro ko dan shara? Ko cikin masu ban ruwan fulawoyin gidan nan Yasir girgiza kai yana murmushi, ya bude akwatin zinari dake hannunsa. Wani ne mai daraja Hajiya, dan'uwan Momy ne da Zinari mahaifinshi yayi sadakinta, na naira miliyan hansi... A take fitsari an tsirin ya kubucewa Hajiya Kaltume ta cire dankwalin kanta ta aje a cinyar Khairy tana kallon zinarin kamar zata yaga ido.... **** **** **** **** Bayan Daddy ya rufe motarsa, suka jero tare da yan'uwansa suna tafiya ya ce. Mahaifinta yayi dabara ni ma na jidadin haka, ka ga mun tsallake ma duk wani tarko a yanzu, shi kan shi Jamal sau biyu ana saka ranar aurensa ana fasawa saboda fushi da wasu hujjoji da ba su kai ba, mu kuma muna biye masa ne saboda farincikinsa muke nema, amman yanzu ka ga wannan duk ya kau a yanzu Gaskiya haka ya fi, ka ga an huta da fitinar Hajiya Turai Daman fitinarta ai zan iya da ita, matata ce fa abun da dai nake tsoro ta canjawa Jamal din ra'ayi gaba daya Wannan gaskiya ne Cewar Alhaji Sadiq. A falon Nene suka zauna gaba dayansu, sai Daddy ya sa a kira masa Captain dake dakin sama tun safe be fito ba, kamin ya fito Daddy ya kalli Momy Ikilima ya ce. Ikilima ki shiga gurin Turai a cikin kayana akwai wata shadda irin wannan ta jiki sabuwa ce a cikin leda, a dauko ta ta hado miki da sabuwar hula, da turaren da ba a fasa ba Toh Yaya Ta tashi ta fice, domin bangaren da Daddy yake sauka dabam idan ya zo gidan. Fitarta da minti biyu Captain ya shigo falon, a kasa ya zauna ya gaishe da iyayensa. Ya karfin jikin Captain Alhamdulillah daman stress me kawai Abba na ji sauki Ya amsawa Alhaji Munzali, kamin ya daga kansa yana kallon dinkakkiyar Shaddar dake Ikilima take mika masa, ya saka hannu biyu ya karba. Shiga ka yi wanka ka saka wannan shaddar ka feshe turaren nan gaba daya a jikinka Daddy why? Ya tambaya da confused. Ina son ka raka ni airport ne kuma ina son mutane su ga yarona cikin mutunci, kuma karka dade ka fito yanzu nan ina jiranka Toh Daddy Captain ya mike tsaye ya fice daga falon na Nene. Dakin da ya zama masaukinsa ya shiga ya cire tufafin jikinsa yayi wanka ya fito ya shafa mai ya saka shaddar ya dauko turaren ya feshe jikinsa gaba daya sai da kwalbar turaren ta kai kasa sannan ya dauki hula ya saka a kasan shi kansa, ya dubi kansa a jikin madubi shi kanshi ya san yayi kyau abun da ake kira da kyau, farar shaddar ta haske shi matuka... Wayarsa ya dauka ya saka aljihu da wallet dinsa sannan ya nufi kofar dakin ta bude ya fita yana wani irin kamshi mai sanar da zuwansa tun kamin ya iso. Ga mamakinsa sai ya samu babban falon na kakarsa a cike da mutane ciko har da mahaifiyarsa da kakarsa da abokiyar zamanta da duka wanda yake gidan a lokacin. Da mamaki ya sauko falon yana kallon kowa kowa kuma yana kallonsa... Zo nan Jamal... Daddy ya fada yana murmushi, Captain ya nufi gurinsa sai Daddy ya mike tsaye ya saka hannunsa aljihu ya ciro goro da dabino ya ce. Bude min hannunka... Captain ya bude tafin hannunsa na dama ya mikawa Daddy, sai Daddy ya zuba masa dabino da goro dake hannunsa. Mun je jaje, kuma mun roki iri, kuma an ba mu, na nema maka auren Hurriya a yau, kuma an daura mun bada zinari na miliyan 50, a matsayin sadakinta, saboda dka fada mana mai tsada ce, shiyasa muka siye ta da kima, yau mai tsada ta zama mallakinka, Hurriya ta zama matarka halak malak... Kamar an aje hoto haka falon yayi tsit kamar babu wani abu mai rai a ciki, daga Captain har iyayensa babu mai motsi.... MASU KARATU BA BIYA A ZO A BIYANI HAKKINA A SAUKE NAUYI A HUTA 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 42 Da farinciki Appa ya shiga dakin Momy ya nufo inda take zaune fuskarsa da annuri ya zauna gefen gado. Da mamaki yake kallonsa daman kam mamakin kiran da Daddy yayi mata ya karbi sarka be gama fita mata ba. Alhamdulillahi Allah abun godiya Ta amsa sannan ta kalli goro da dabinon da ya shigo da su gabanta na faduwa. So da yawa kanyi abu basan alherinsa ba sai a gaba, wani abun kuma Allah ya barwa kansa sani, ban tana jin farinciki da alfahari da aurenki ba sai yau, Allah ua miki albarka Nafisa sanadinki yau na fita bakinciki an shafe min duk wata damuwa da nake jinta a raina saboda faruwar abubuwan nan Momy ta yi murmushin rashin gamsuwa. Daman ai Yaya akwai karanci, wani abun yayi maka ko? anki Jamal kuma dansa ya nemawa auren Hurriya, kuma be bar gidan nan ba sai da aka daura auren Momy ta kyalkyale da dariya har da daga kafa sama da buga a kasa. Yau kuma ni ake yi ma zolaya, taya za'ayi daurin aure a cikin gida ba mu sani ba kuma daga kai sai yan tairarun mutane? Kila dai aurenka ne za a daura ko kake min kwano kwano Appa yayi murmushi mai kyau. Shi aure ai ba dole sai an tara mutane ba, amman amsu aikin gidan nan da yayanta Yasir sun shaidin auren Hurriya aka daura da Jamal a yau, kuma yayanki ya bada Zinari a matsayin sadaki Ya aje mata goro da dabino na daurin auren a gadonta. Kin ga goro da dabino nan! Ta kalli goron da dabino har lokacin dariya take domin maganar Appa ba magana ce mai kama kai ba, sai dai kume? Appa ba zai mata wasa ba, ba zai ce anyi ba alhalin ba ayi ba. A take dariyar ta bace mata bat ta daga kai ta kalli Appa. Da gaske Alhaji? Yayana ya zo gidan nan ya nemawa Captain auren Hurriya? Har an daura, yace ba zai iya da rigimarki ba, dan haka ya wuce yace ni na sanar miki.... Momy ta mike tsaye wayar dake cinyarta ta fadi kasa. Aure Alhaji? Auren Hurriya aka daura da Captain? Kwarai, kowa ya ji zai yi mamaki, kuma tabbas Alhaji Turaki ya kai mutumen kirki har ya wuce, ya yaye min bakinciki kuma na yarda zai rike yata da amana Momy ta dafe zuciyarta. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un La'ilaha Illallahu Muhammad Rasulullahi Sallalahu Alaihi Wassalam Appa ya bita da kallon al'ajabi ganin yadda ta yi kamar wadda aka fadawa mugun abu. Yanzu duk matan duniyar nan Captain ya rasa wa zai aura sai Hurriya? Yarinyar da duniya ta gama ganin tsiraicinta? Yarinyar da ko ido bata shi a yanzu? Anya Captain yana cikin hayyacinsa? Ita Hurriya ba mace ba ce? Da kike fadar ya rasa wa zai aura sai ita? Wane irin magana kike haka ne Nafisa? Captain ya fi karfin Hurriya bata cancance shi ba, rantsuwa fa na yi cewar Captain ba zai auri Hurriya ba, shi ne Yaya zai shammace ni? Kuma ya biya sadakinta da zinarina da ban taba sakawa ba? Naira miliyan hansi akan makauniya yarinyar da duniya ta gama da ita? Appa ya mike tsaye ya daga hannu kamar zai mari Momy sai kuma wata zuciyar ta hana shi, a madadin haka ya nunata da yatsansa. Ki san abubuwa da kike fada akan Hurriya, kamar kin mace a gaban waye kike tsaye ni fa na haifi Hurriya, a madadin ki yi farinciki jininki ya auri jini sai ya zama abun bakinciki a gurinki Idan kai ne mahaifin Hurriya sai me? Na yi farinciki an'uwana ya dauko yar kishiya ya kawo a matsayin suruka? Ya tsallake Namra ya tsallake duk yaran family ya fada gurin Hurriya Appa yayi murmushi yayi girgiza kai. Yanzu na fahimci komai, Allah ya huci zuciyarki yara kuma Allah ua ba su zaman lafiya... Appa yayi dariya mai sauti ya fice daga dakin. Momy ta dora hannu a kai tana ta rawa kamar mai jin sanyi. Daman wannan ne dalilin zuwa? Har kana fada min Captain ya hakura? Ni kake yi ma wayon Yaya? Ko ba zai auri Namra ba me yasa zaka amince masa ya auri Hurriya? A cikin falona za a nemi auren yar kishiyata ba yata ba, duk tarin dukiyar Yaya da ta matarsa aya da suke ji da shi ya rasa wa zai aura a duniya sai Hurriya? Yarinyar ido ya rufe mata? Aka tallata tsiraicinta, yarinyar da uwarta ma ga aiki ta yi, talakawa maskakanta, tarin dukiyar Yaya Yau Hurriya ce yarinyar da zata raba a jiki a dukiyar gidanmu, kuma ta bangaren da ya fi gwabi Daki cinyarta tana jin kamar ta zaga tufafin jikinta, a matukar fucece ta fice daga dakin ta shiga dakin Hurriya ta fara yaye Bedsheets dinta
Chapter 120 · 0% Book details