Sashe 21
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yana dan taba mata hira, ita kuma ta kasa cewa komai sai kallon gari take har lokacin tsoro be fice ta ba, garin kuma tana ganin kamar ya sake saboda dadewa da ta yi bata fita ba. Bismillahi Ta furta yayin da ta bude motar zata fita, zuciyarta nata rawa, Yasir ya rakata har cikin falon Hajiya Fatee, yan aikin Hajiya Fatee suka fara gaisheta. Lafiya Kalau Ina Hajiya Fatee Tana dakinta Hajiya Kaltume ta juya ta kalli Yasir. Bari na kirata ku gaisa Okay Ya nufi kujera ya zauna, Hajiya Kaltume kuma ta nufi dakin Hajiya fatee ta tura kofar ta shiga da sallama. Kuka ya hana Hajiya Fatee amsawa sai dagowa da ta yi ta kalleta da idanuwanta da suka gama kumbura. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Hajiya Fatee abun har ya kai haka Ya wuce, Hajiya Kaltume ina cikin bala'i da tashin hankali Hajiya Kaltume ta juya ta leka falon saitin da yasir yake zaune. Yasir ka tafi kawai idan zaka dawo daukata sai ku gaisa, amman fa da zarar na kiraka ka zo da sauri Toh Hajiya Ya tashi ya fice cike da ladabi. Sannan Hajiya Kaltume ta koma dakin ta zauna kusa da kawarta da rabin kibar jikinta ta zube saboda tashin hankali. Wannan abu be yi dadi ba, yanzu miye abun yi? Hajiya Fatee ta share hawayenta ta kalli aminiyarta. Ban sani ba Hajiya Kaltume, wannan shi ne likita na uku da ya fada min haka Hajiya Fatee duk laifinki, da tun farko kin yarda anje asibitin an duba lafiyarki da duk be kai ga haka ba? Haba Hajiya, ina zan yarda aje asibiti a fadawa ana abun da mutanen nan suka min? Tsoron kar ya kalleni da abin kuma kar bakinciki ya zauna masa a zuciya ya saka na ki amincewa da zuwa asibitin, kuma ni ma na san idan har ya sani ba zan samu salama ba Hajiya Kaltume ta rafka tagumi. Wallahi duk wannan Iyamin ce ta ja mana, ba zan tana yafe mata ba, ni kaina yanzu sanadinta har tsoron fita nake Ni yanzu ba ta Iyami nake ba Hajiya ta kaina nake, kar asirina ya tonu, ga ni ta surukar da bata kaunata, ga makiyi babban tashin hankali kuma rashin auren nan, yau shekara goma da rasuwar Alhaji me zan fadawa duniya idan abun nan ya fito da shekaru na haka har da jikoki Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya. Hajiya ko dai daurewa zamu akara yin allurar nan ne? Ko Allah zai saka abun ya zube Hajiya Fatee ta dauki robar yawu ta tsargar da yawunta cikin ta aje ta kalli Hajiya Kaltume. Likita nan fa ya fada min, ta farko ma da na auna arziki ne, da yanzu na wuce, ni kadai na san azabar da na sha lokacin da aka min allurar nan kuma gashi bukata bata biya ba, kuma cirewar sun ce ko na mutu ko na yi rai ne Hannu biyu Hajiya Kaltume ta dora saman kai ta fashe da kuka tana taya aminiyarta alhini. Kai wayyo Allah wannan Iyami wannan Iyami Allah ya isar mana gareki, kin aure min miji kin fitine ni yanzu kuma sanadin nan mun fada cikin bala'i, ni Wallahi ma rasa ya zan yi da matar nan da yaranta, kin ga cikinta ya shiga wata na tara kenan wani zata haifowa Alhaji, yayanta da suke gidan ma be hada kowa da su ba, birthday nan da Hurriya ta yi sarkar zinari ta miliyoyan kudi yayi mata kyauta, ni da nake matarsa be taba siya min ba, sarkar da Nafisa take ta kuri da ita yau Alhaji ya siya irinta ya mallakawa Hurriya, ga birthday Hamad tafe waya san iya abun da zai masa shi ma, kuma saboda ita yanzu ya budewa kofa kofar birthday, abun da da ya hana Hajiya Fatee ta daki kirji. Sarka Hajiya? Lallai Iyami ba zata gama da duniya lafiya ba, ta mallake shi yanzu ta bar gida ta bar muku ya ku yi kishi da ita Hmm abun nan ya ishe ni, ai saboda na san kina cikin taki matsalar ne ya saka ban kawo miki kukana ba, amman ciwon matar nan yana nan a kirjina, a yanzu bana da burin da ya wuce na ga Alhaji ya fita lamarin yaran nan, kuma dukiyar da ya bata ta lalace Ba ke ba, ai ko ni ba zan iya yafewa Iyami ba Hajiya, sanadinta yara kanana sana'in yayana suka daure mu a daji babu kalar wulakancin da ba su min ba, yanzu kuma ga wani abun bakinciki ya sake biyo baya, ban san ya zan yi ba Ta karashe zancen tare da fashewa da kuka. Toh ni dai ina ganin abun da ya kamata kawai mu saka a nemo mana malamin nan ko Allah zai saka mu dace Hajiya Fatee ta mata wani kallo galala. Waya zai koma a wannan dajin? Ko gawata ba za a kai ba Aa ina fa? Ni ma ai ba zan yarda ba, ba komawa zamu yi ba nemansa zamu yi idan ya so shi sai ya zo ya same mu Ta ina? Duka wayoyin mu suka karbe fa, ba ni da number ba, kuma da aka yi welcome din Sim din har yanzu be kira ni ba, waya sani ma ko shi ya turo a dauke mu? Mutanen nan kauye nan fa ba su da kyau Kai bana tunani haka, kin ga ni fa na ga kyau aikinsa domin shi kadai ne yayi min aiki kuma aikin yayi yadda nake so har Iyami ta bar gidan nan, shekara nawa ina kashe kudi a banza ban dace ba sai a gunsa, sa zaki yi a nema mana shi waya nuna miki gurin Malamin Wata kawata ce Salame Toh ita zaki saka ta je ta dauko mana shi, sai mu saka gurin haduwa da shi ba dole sai ya san gidan mu ba, mu gabatar masa da bukatanmu mu basa kudin aiki, daga nan ma sai na tambaye shi ina aka kwana zancen aikin Iyami, ke kuma sai ki saka yayi miki na wannan mugun abun da yake cikinki Kallon rashin fahimta Hajiya Fatee ta yi mata Ya danne miki shi mana, ba zai taba tashi ba har ki mutu, ko baki san ana haka ba? Na Iyami ma so nake a danne shi kar ta haifa ma Alhaji mugun abu, dan na san duk wayonta be wuce Alhaji ya mutu ta ci gado ba Hajiya Fatee ta kalleta wata rahma na saukar mata a ruhi, jin kamar ta samu mafitar masifar da take ciki. Kuma kina ganin hakan zai yi? Me zai hana? Ki dai ki zuba masa kudi kawai, ni ma kudin zan zuba masa, kuma a hannun Alhaji zan karbe su, kudin sarkar zinarin da ya siyawa Hurriya da kudin da ya bawa Iyami duk sai na fanshesu a hannunsa, yanzu ne za su gane sun yi kuskuren taba mace kamar ni, kuma Wallahi sai na malleke Alhaji ko ta halin yaya, sai ya dawo a tafi hannuna Iyami da anta sai sun ana ku arsu, Iyami sai ta gane kuskuren da ta aikata na aurar min miji, sai ta yi nadamar hada shimfida da Alhaji, matsayin da ta taka a baya na tana Matar Alhaji ina Matar Alhaji sai na saka ta yi nadamar haka... Ba ita ba har Nafisa sai na sake mata sabon karatu na goge mata hadda. Dukansu sai sun dawo a tafin hannuna Ya daki tafin hannunta tana kashe ido alamar yanzu ta shiryawa rashin imani, da kuma fada da Iyami da Momy. ________________ Hmmmmmm Allah yasa kuna hango abubuwan da nake hangowa Tafiyar fa duk duka yanzu aka fara.... Ku daura amara ku zage damtse domin domin alkalinmin da zafinsa ya zo Kar a manta idan an karanta ayi sharing [10/18, 6:15 PM] Nana 1: Hello Habibaties Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy Musib ya aje ma Captain keys din motar Momy da ta bada umarnin a dauko masa. Kallon Keys din yayi sannan ya mika hannu ya dauka ya mike tsaye. Tsabar bacin rai zuciyarsa har zafi take kamar zata fashe, baya jin yana da sauran wata magana a yanzu kuma baya bukatar yi ma Momy sallama bayan an bata masa tayun mota a gidanta. Shi ya fara fita sannan mahaifiyarsa ta bi bayansa Momy da Musib suka biyo shi suna ba shi hakuri kamar su suka masa laifin shi dai be ce uffan ba ya matsa key hannunsa motar ta fita key ya sannan ya nufita har suka bar gidan kalma daya bata sake fitowa daga bakinsa. Ran Momy be yi dadi ba ganin an'uwanta da take ji da shi ya fita cikin bacin rai. Ni abun nan ya ba ni mamaki, wai waye yayi wannan aika-aikar Zai wuce Kaltume? Ai bata son kowa da alheri a gidan nan kuma ta ga mota mai tsada ina za so haka, ballantana fitowar nan da ta yi dan uwa ko daya be je ya mata barka da fitowa ba Amman Momy Yasir dai ba zai yi haka ba kin san ko da ta saka shi Su matan fa? Kuma shi ma ba munafurci ba ne da nuna soyayyar ido, ai ta ciki na ciki dan'uwa be taba son dan'uba ba har abada Ko kuma ta aiko wani yayi ba Ta juyo tare da Musib suka shigo falon, ko zama ba su yi ba motar Appa ta faka a harabar ya bude ya fito ya shigo cikin falon fuska a dauke. Ku ba mu guri zan yi magana da mahaifiyarku Appa ya fada immediately after ya rufe kofar falon, Musib ya dubi Miwan sannan suka tashi suka haura sama, Momy kuma ta zauna ita ma nata ran a bace tana sauraren da wacce Appa ya zo. Nafisa ina son na tambaye ki, akwai laifin da Hurriya ta yi miki ko kuma Hamad? Wani abun aka fada kuma? Akan wani dalili zaki nemi banbanta su da sauran yayanki? Fada min banbanci dake tsakinsu da Namra ko Miwan, dukansu ba Yayana ba ne? Akan wane dalili zaki ce Hurriya sai dai ta share dakinta da kanta kuma idan zata hau stairs ko ta sauka ba ta hau kamar yadda Namra ko Musib suke yi ba? Momy ta rike baki. Oh Allah na