← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 143

Sashe 107

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

so ka jirana idan na fito zamu yi waya Be jira abun da Salim zai sake cewa ba ya kashe wayar, ya aje a cikin motar ya cigaba da tukunsa, a babban Masallacin kan wurin Sarki dake garin Gusau yayi Sallah Jumma'a sannan ya kira Salim at that Salim yana mosque domin ba masallaci daya suke sallah ba, and akwai banbancin lokacin sallah Jumma'a a Masallacin Sheik Umar Kanoma da na kan wuri. A kokarinsa na martaba lokaci ya nufo gidansu Salim din kai tsaye, a harabar gidan ya shiga ya faka sannan ya aika masa da sako. Idan ka gama ina harabar gidanku Ya aje wayar ya bude gurin da yake cewa ajiye pistol dinsa ya dauka ya saka a jikinsa sannan ya dauki counter dinsa dake cikin motar ya laka a yatsansa yana tannawa, ya san yau ranar jumma'a ce ranar da aka ce a ninka salati ga Annabi Muhammad S A W, idan kuma baka yi ka yi domin shi salati haske ne a duniya da kiyama. Ya kusan minti talatin a gurin sannan reply din Salim ya shigo wayarsa. On my way Ya karanta sakon ya sake maida wayar ya saka aljihu ya cigaba da salatin, yana kallon harabar gidan iyakarta rabin na su harabar dake Kaduna. Tsaki ya dan ja ya duba agogon hannunsa, wata zuciyar na ce masa ya kira Salim ya fada masa idan sun hadu a gurin aiki za su yi magana domin baya son bata lokaci a gurin, kamin ya kira motar Salim ya shigo harabar gidan ya faka daidai gurin da motar Captain take, kusan a tare suka bude motocin kowa ya fito, but jin kai irin na Captain ya hana shi isa gurin Salim sai da Salim din ya karaso gurinsa ya jingina jikin motarsa. Minene? Captain ya tambaya ganin seriousness a fuskar Salim. Karamar ajiyar zuciya Salim ya sauke sannan ya fara taba wayarsa dake hannunsa. Ina dawowa na tararda wani labari marar dadi a gidan nan Captain ya dauke kai. Kan da son jan zance, kai ba mace ba balle ace zan bika ina lallabaka, tun a mota ma ya kamata ka fada min ko minene amman baka yi ba yanzu kuma na zo kana abu kamar mai rubuta littafi, and you know bana son wannan bata lokaci Akan Hurriya ne, wani abu ta aikata ita da Cousin dina, so abun ya daure min kai na tura maka hotunan yanzu ta whatsapp ka duba Ba zan duba ba idan ba zaka fada ba zan tafi Tana mu'alama da cousin dina, ina tunanin shi ne reason din da ya hana ta amsar soyayya ta, and Alhamdulillah na jidadin haka Captain ya tsaya cak yana kallonsa with so many questions zuciyarsa ta soma zafi kamin ta tafasa, idonsa na kokarin sauyawa, the word mu'alama kowa ya ji ya san bad thing ake nufi kalma ce ba mai kyau ba. Salim ya mika masa wayarsa Duba wannan Captain ya karbi wayar ya sauke idonsa akan mugun abun da he wish be kalla ba, hotunan Hurriya ne a sirara tare da mutumen da yake ganin idan ya zo gurin Salim, wani gurin suna kwance a gado daya, wani gurin kuma ta kwanto jikinsa wani kuma ta yana kissing dinta ya tallabo kanta da hannunsa dake cikin gashin kanta, na karshen ne hannunsa yake kan kirjinta and duka hotunan daga ita har shi babu mai tufafi a jikinsu. Wannan ba Hurriya ba ce Ni ma hala na fada da farko domin yadda take da tarbiya da mutumci ba zaka yi zaton ta aikata ba Captain ya dago ya kalleshi naman fuskarsa na rawa cikin wata kalar murya mai fita da sauti ya ce Waya turo maka wannan? Cousin dina ne fa, yanzu haka case din da na zo gida na tarar ana yi kenan, i was shocked da na ga abu kuma na yi magana da shi ya fada min gaskiyar itace amman be san ya aka yi hotunan suka fita ba Captain ya hade yawun bakinsa sannan ya nuna wayar Salim dake hannunsa da yatsansa na hadu. Ina yaron nan yake Salim? I need to talk to him... Yana ciki bari na kira shi... Salim ya nufi main house din da saurinsa shi kansa mamakin abun yake ta wani bangaren kuma yana gode Allah da be yi soyayya da Hurriya ba. Captain ya juya ya kife kansa jikin motar zuciyarsa na bugawa da karfi, wani numfashi mai zafi yana fita a hancinsa da bakinsa, wani irin kuna zuciyarsa take tana isarwa har cikin kansa. Can kuma ya juyo ya jingina da motar, kamin ya daga ya fara zagaya motar hannayensa nade a baya rike da wayar ta Salim. Hurriya....? Ya furta mamakin zayyane a fuskarsa, juyowa yayi ya dawo gurin da Salim ya bar shi ya tsaya ya rumgume hannayensa yana kallon Salim din da ya fito tare da Adam, kamin su karaso Captain ya nufi gurinsu suka hadu a tsakiyar gidan. Abun da Salim ya nuna yanzu nake son na tambaye ka it's real or fake? Adam ya kalli Salim ya sake kallon Captain. Wane irin tambaya ne wannan Captain ya kawar da fuska yayi murmushi, Salim ya kalli Adam. Just answer him It's real Captain ya kara matsawa kusa da Adam yana wasa kafafuwansa kamar wanda yayi shekara a tsaye. When how? Where? A inda muka saba haduwa? Da saninta ka dauki hotunan? Aa ba da saninta ba, kuma ban san ya aka yi hotunan suka fita ba Captain ya juya baya ya busar da iskar bakinsa ya juyo ya kalleshi. Adam idan wani ya saka ka yi wannan abun i cam pay you fiye da abin da aka biyaka Adam ya girgiza kai. Babu wanda ya biyani, kamar baka san waye ni ba? Wa zai biyani na yi wannan abun? Captain ya kalli Salim, Salim ma ya kalleshi kamin ya kalli Adam a karo na biyu. Ina kuke haduwa da ita? Tudun wada low-cost Why not gidansu? Saboda iyayenta basa so na Ya aka yi ka san yarinyar nan ina ka santa? Hurriya...? Na hadu da ita a bikin birthday din yayarta Khairy daga lokacin muka fara soyayya sai kuma iyayenta suka fara nuna basa son alakata da ita, daga lokacin sai muka yanke gurin haduwa daga nan dai sai shedan ya shiga tsakaninmu Captain ya maida dubansa gurin Salim cikin kalar yanayi dake sauya kyau fuskarsa da raunin idonsa. Idan kana son Hurriya bata so ka ba, wannan normal ne an saba haka, amman kokarin aikata wani abu, martabarta da ta gidansu kake tabawa Ya matsa kusa da Salim irin matsawar da yan dambe suke yi idan suka kullace mutum a zuciya. Ba zan bar wannan ba, ba zan kyale kowa da hannu a lamarin nan ba What do you mean? Ni zan saka kanena ya aikata haka? Shi ma an taba martabarsa da ta gidanmu ko ka gane? I don't care shi namiji ne zai iya haka, ko kai ka saka shi ko kuma yana sonta a karan kansa zai iya haka? Hurriya ba zata aikata wannan abun ba ba zata yi hakan a cikin hayyacinta ba Saboda yana wearing innocent face tana nuna ita ta kwarai ce? Baka da wannan tabbacin Captain, miye alakarka da ita wai da kake ta wannan kokarin Captain ya matsa baya ya watse wayar Salim dake hannunsa cikin daga murya da ya hankalonta da idon kowa a harabar zuwa garesu ya ce. Ubanta ne ni Salim.... Haka kake son ji? Cikin zafin nama ya riko hannun Adam ya lankwashe hannun hoton da ya gani na hannuns aa kirjin Hurriya kawai yake ta gani a idonsa har yanzu. Salim yayi hanzarin rike Captain No no no no... Captain.. Captain ya fisge hannunsa ya rika hannun Adam dake ihu da hannu biyu ya daga kafarsa ya karya hannun Adam, da mutane suka yo kansu kamin su kawo ya dunkula hannunsa ya kai a bakin Adam a take ya barar masa da hakora daya jini ya wanke baki, Salim ya rike Captain da karfi amman hakan be hana Captain shimfidawa Adam duka a kirjin da ya kwantar da kan Hurriya ba. Mutanen suka rike Adam dake ihu kamar za a cire masa rai. Salim ya sake shi da karfi ya dawo gabansa ya tsaya Captain miye haka? Miye alakarka da ita? Dan me zaka rasa control akan wannan abun? Sai kuma ya juya da sauri ya tare wani yayan Adam din dake son kaiwa Captain duka. Aa please matsala ce da za a iya magancewa dan Allah Kabir ka bar wannan abun a hannu Bar shi ya taba Captain din soja ya jawa kansa bala'i Salim ya juyo gurin Captain dake maganar ya kalleshi ganin yana kokarin ballo masa wasu ruwan ballo masa ruwa a lokacin da yake son toshe wata hanyar, kowa dake gidan sai yayi ma Captain uzuri saboda suna zaton yayan Hurriya ne, shi kansu abun ya taba su balle kuma shi da yake da kanwa mace. Captain ya bude motarsa ya shiga ya bar Salim a tsaye yana bawa Yayan Adam din hakuri domin yau jumma'a wasu yan'uwa duk ba su dawo daga gurin Sallah ba, masu aikin gidan ne kawai sai wannan yayan nasa da kuma mahaifiyar Adam din wacce ta fito tana kuka tana fadin ba zata bar Captain ba. Yadda abun ya taba martabar gidansu haka ya tana martaba mu, kuma ai tare suka hadu suka aikata saboda me zai fadawa dana? Ba kyale maganar za'ayi ba, dole za a bi kadi ai, yanzu dai abun da ya fi a dauki Adam din a kai shi asibiti Su biyu suka kama shi, Salim da yayansa Kabir suka saka shi a motar Salim din suka nufi asibiti da shi. Suna isa Emergency Salim be tsaya an karbi Adam ba ya bar Kabir da Adam din a gurin ya juyo da motarsa ya bi bayan Captain ya san ba zai wuce ya tafi gidansu Hurriya ba. Kamin Captain ya iso gidansu Hurriya ya kusa balla sitiyarin motar saboda yadda yake dukansa da mugun karfi yana fisgarsa, gaba daya ya rasa ta ina zai fara tunani. Yana yin fakin be tsaya kashe motar ba ya bude ya fita ya bar motar a bude, yadda ya tura kofar falon Momy
Chapter 107 · 0% Book details