Sashe 18
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya daidaita tsakaninta da Appa, sai dai ta bar kyau tun ranar haihuwa domin bata damu da yin azkar din neman tsari ba, tana ta tawaya a wannan babin, duk kuwa da ta san tana cikin kishiyoyi irinsu Hajiya Kaltume da Momy. [10/18, 5:35 PM] Nana 1: Hello Habibaties Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy Washe garin ranar... Hurriya na cire uniform dinta na makarantar boko ta dauki bakar abaya ta saka, ta bude gurin da take zuba hullunata tun bayan da ta kwaso kayanta daga bangaren Amma ta dawo da su bangaren Momy a dakin da aka bata, ta dauko farar hulla ta saka a kanta. Sannan ta fara gyara dakinta ta kintsa komai, cikin natsuwa ta fito daga dakin ta shiga dakin Hamad da ya watsar nasa uniform din akan gado ta dauka ta aje masa ta gyara masa dakin, daman shi be kula da gyara daki ba ko a lokacin da Amma na gidan balle kuma yanzu da tufafinsa ma sai da Hurriya ta kwaso ta dawo masa da su dakinsa dake bangaren Momy. After ta gyara nasa dakin ta sauka kasa domin dauko abun shara da mopper haka take kullum idan ta dawo take gyara nata dakin da na Hamad domin Momy ta hana masu aikinta share dakin Hamad da Hurriya haka ma ta hana ko cokali suka aje masu aiki su dauka, kamar ya yaran gidan ba haka Momy take treating dinsu, musamman ma Hurriya da bata iya budewa kowa cikinta, Hamad kuma idan ya ci abinci a nan yake bari sai dai Hurriya ta dauke masa, ba kowane rules and regulations na Momy ya sani ba, ko na ya sani ba amfanin da za su masa domin ba bi zai yi ba. Gurin da ake aje kayan taje ta dauko ta hauro sama a hankali, domin Momy ta jaddada mata bata son jin karar tafiyar kowa a saman, hakan ya saka take kokarin ganin ta kiyaye dokokinta, ta san ba dan komai take nata haka ba sai dan ta takura mata idan kuma ta fadawa Appa wata kila zata iya jawa kanta matsala a gurin Momy. Dakin dan'uwanta ta fara gyarawa sannan ta shiga nata dakin ta fara sharewa. Cikin oki Hamad ya shigo dakin nata. Hurriya za mu je dauko Hajiya yanzu Ta juyo ta kalleshi da sauri. Wace Hajiya Hajiyar Appa tace zata zo, Appa ya kira ni yace na zo muje daukota yanzu nan Hurriya ta daka tsalle tana murna, daga ita har Hamad suna matukar son zuwa gurin Hajiya Binta kuma suna daukin ganinta a gidan ubansu, al'adace ta Alhaji Haruna, duk ranar da mahaifiyarsa zata zo gidansa da kansa yake zuwa ya daukota idan kuma ta tashi tafiya shi zai maidata gidanta, komai yake zai aje ya dauko ko ya kaita gida matukar gidansa zata zo, wannan ya saka tun ana sauran kwana biyu ta zo gidan take sanar masa, shi kuma ya sanar ma matansa a shirya mata tarba mai kyau. Murmushin da murnar da Hurriya ta gani a fuskar dan'uwanta Hamad ya ninka farinciki zuwan Hajiya Binta da take a gidan, domin tun tafiyar Amma bata san wata rana da Hamad ya sake fuska yana far'a kamar yau ba. Zan mata wanka mai kyau kin san ta iya tsokana ta tana cewa ban iya wanka mai kyau ba, tufafi zan canja yanzu nan Da karfi yake maganar, kamar yadda ya saba yi a bangaren Amma idan yana cikin farinciki. Hurriya ta yi saurin yi masa alama. Yi a hankali kar Momy ta ji ta fara maka masifa? Saboda me? Bata son hayaniya kuma tace idan zamu hauro ko sauka stairs mu yi a hankali kar mu yi making sound bata son ana hawa mata da karfi Yaushe tace haka? An dade, kai ai ba zama kake bangaren ba sai idan zaka kwanta shiyasa baka sani ba Sai na fadawa Hajiya duk abun da ake mana a gidan nan Hurriya ta saki mopper dake hannunta ta nufo kofar dakin gun da Hamad yake tsaye. Hamad kar ka yi haka, kasan zata yi ma Appa fada shi kuma zai yi ma Momy, idan aka yi Momy kuma kan mu zai dawo Sai na sake fada mata, Appa ma dan ina fushi ne da shi shiyasa ba zan fada masa ba, ni ba zan ma iya zama bangaren nan ba i hate them Ya saki kofar ya nufi tasa kofar ya bude, Hurriya ta dora hannu daya akai tana jin ina ma ace bata fada ba, tsoro take kar ace daga dawowarta bangaren ta fara hada munafurci, kuma ta san at the end abun gurinta zai dawo. Hamad na canja tufafi ya dauki turare ya saka ya canja shoes ya fito daga dakin ya sauko kasa ya fice daga falon daga Miwan har Namra dake falon be cewa kowa komai ba. Miwan ya bishi da harara Yaro nan fa ya raina mutane, idan zai shigo haka zai shigo babu sallama idan ya tashi be iya gaishe da kowa Yaya idan ka ce zaka biye ta Hamad za ku yi ta samun matsala ne fa, Amma ma da tana nan fama take da shi balle kuma mu Ba ruwana da rashin jinsa ko rashin kunya ni ubansa zanci Wallahi Ya amsawa Namra yana ayyana yadda zai yi ma Hamad mugun duka idan ya shiga gonarsa. Namra dai bata sake cewa komai ba ta shiga ta jera warmers din da masu aikin Momy ke ajewa a kasan dinning, Hurriya ce ta fito rike da boket din da ta yi mopping da mopper ta nufi hanyar tsakar gidan dake ta cikin falon Momy ta bude kofar baya ta fita ta wanke komai sannan ta dawo cikin falon, a daidai lokacin da aka turo kofar falon aka shigo wata doguwar mace ce tana sanye da bakar abaya da aka kawata da blue stone ta daura dankwalin atamfa saman kanta sannan ta dora mayafin abayar a sama ya sauko mata, hannunta na rike da Gucci bag, tsalle Namra ta saka ta kwala ihu ta nufi matar da alama ta nuna murmushi sai ma sai yayi yaki yake samun mazauni a fuskarta, kallo daya zaka masa ka fahimci ta ninka Momy kasaita da ji da kai. Ammy sannu da zuwa Cewar Namra cikin zumudi tana rumgumeta, Miwan ya mike tsaye yana gyara rigarsa tare da yi mata barka da zuwa. Namra...ana gida Ta fada kamar mai jin wahalar magana. Eh Ammy sannu da zuwa, tun safe muke duban hanyarki Toh gani na iso, Ina Hajiya Nafisa? Ta tambaya tana kallon Hurriya da ta yi tsaye da ta fito daga dakin da da ake aje mopper. Momy Momy Momy... Namra ta daga murya tana kiran Momy, Hurriya kuma ta dan risina kamar yadda ta saba ta gaisheta. Ina wuni Lafiya... Ta amsa tana binta da kallo tare da dan yamutsa fuska. Ita ce ..... Hurriya Namra ta karasa mata, sai ta watsawa Hurriya wani kallo daga sama har kasa ta yamutsa fuska kamar wadda ta yi arba da wani abun kyama. Hurriya ta kalli jikinta sannan ta kalli matar da tuni ta kama hanyar stairs gurin Momy dake saukowa da saurinta tana mata lale marhabun. Da alama Namra bata ji dadin abun da matar da take bakuwa a idon Hurriya ta yi ba, sai ta kama hannun Hurriya ta nufi kitchen da ita suna shiga ta rufe kofar kitchen din ta kalli Hurriya da har lokacin mamakin yadda matar ta yi mata kallon wulakanci take, bayan kuma bata da wani abun wulakantawa a jikinta ko suturarta, gashi alama ya nuna ta santa ita kuma bata wayanci wacece matar da Izza ta cikawa ciki har ta bayyana a kamaninta ba. Hurriya dan Allah kar abun da ake miki a gidan nan ya dame ki, kin san dai matsayinki a gidan nan, dan haka karki kula komai kin ji? Hurriya ta amsawa yar'uwar tata da kai. Wacece wannan Matar Yaya Namra? Big Brother din su Momy to natarsa ce wannan, ba a nan suke ba, a Kaduna suke zaune ta zo duba mahaifiyar mijinta ne da bata jindadi maybe shiyasa ta biyo ta nan saboda suna good time da Momy sosai Nan ma da kai ta amsa mata sannan ta juya zata fice daga kitchen din. Kin ci abinci? Aa Hamad ya ce Hajiyar Appa zata zo, ina jiram ta zo ne sai mu ci abinci tare Yayi yar gidan Hajiyar Appa Hurriya ta yi murmushi ta bude kitchen din ta fito tana rike da hannayenta ta nufi upstairs, Miwan ya wurga mata harara yana jin haushin yadda Namra take mata sanyi ko a lokacin da Amma take nan balle kuma yanzu, hakan ya saka suke mata kallon munafukar cikinsu, domin ita halinta dabam da na su, kishi da ya kamata ace tana taya Momy bata yi ta bar musu sai dai su yi. Hurriya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta nufi gadonta ta kwanta ta takure gurin daya kamar wanda aka tsare sai hawaye ya fara saukowa a idonta, tunanin barin gidan da Amma ta yi ya dawo mata sabo. **** **** **** Cikin annashuwa da aukin gani Momy take kallonta. Ai har ina cewa maybe ba zaki biyo ba, na ga Yamma ta yi Matar dake kawar da kai daga barin kallon aikin Momy dake jera mata kayan da aka shirya mata ta kalli Momy. Ai kin san halin Captain shi ya fi son tafiyar dare Tare da shi kuka zo kenan? Amman be shigo ba? Yana waje, waya yake Oh Soyyayar da bata karewa, ai dai an kusa auren nan a huta, ke ma ki samu hutawa Ammy Toh sai a taya mu da Addu'a Allah ya daidaita tsakaninsu Tana maganar tare da kai hannu ta dauko plate din grapes din da aka rolling ta cire ledar ta fara ci. Tsabani suka samu ne? Cikin mamaki Momy ta bukaci sani. Kamin ta bata amsa sai da ta juya ta kalli kofar dakin Momy da daya daga cikin masu aikinta taja. Wai har cikin daki kike barin masu aikinki suna shigowa? Toh ya zan yi Hajiya Turai? Kin san dai ba zan yi aiki da kaina ba, dole su zan saka Ai ni iyakacina da mai aiki falo