Sashe 89
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duk inda nake saka ran samu wannan turaren Kapter Bokur Perfume ance min babu shi, wasu sunce sai Abuja da Kaduna ake samunsa ko Kano, wasu ma cewa suke ba su sanshi ba Ya dago daga aikin da yake yana murmushi ya jingina da kujerar da yake zaune yana lilo, shi kanshi daman ya san ba za a samu turare ba domin abun da babu ne be ya fada mata, shi ya hada sunan turare and ya san babu turaren dake da exiting mai irin sunan. Okay, na baki zabi ki zabo min turare mai kamshi Aa ka fada dai, kar sai na dauko maka turare ka zo kana min fada ko ka ce mai warin albasa ne, kasan wata rana ba a maka daidai, garin gwaninta sai a bata maka rai Ssi ka ce ni nafi kowa muguwar zuciyar? Please select ina jiranki Ta kashe wayar, sai ya juyo kansa a hankali ya kalli gurin da Hurriya ta zauna, rabin abincin da ta zuba a duk a kasa yake garin sauri ta zuba kuma ta ci. Mtscheeeeee Yaja tsaki ya tsani guri da datti ko kadan ne balle kuma na abinci, telephone dinsa yayi using ya kira aka shigo aka gyara gurin aka maida komai gafe daya, bayan kamar awa daya Namra ta kira sai ya fada mata inda zata zo ta same shi, a lokacin da ta iso gurin ita kanta sai ta tsoro ya kama ta even though ta taba zuwa amman yadda aka gyara gurin aka canja komai da tsaurara tsaro ya fi na da, arzikinta daya ya aiko aka shiga da ita har ciki. Tana shigowa Office din ya dauke hannayensa daga aikin da yake yana murmushi. Allah yasa kin zabo mai kamshi I try my best na ga na samu mai kamshi kuma mai dadi, shiyasa na siyo kala biyar ba daya ba Ta matso kusa da teburin ta dora bag din da turaren yake ciki ta fara cirowa tana nuna masa. Ba laifi duka suna da dadi kuma duka na maza ne, amman babu kalar nasa a ciki, haka yayi mata godiya ya karba ya aje, a lokacin da take kokarin dauke idonta daga teburin idanuwan nata suka yi arba da gilashin Hurriya dake kan teburin a take ta kai hannu ta dauka tana dubawa. Kamar gilashin Hurriya Nata ne Ya amsa mata kai tsaye ba tare da tunanin komai ba. Ta juya ta karewa ko'ina na office din kallo sai ta dora hasashenta akan abinci ta kawo masa saboda kulolin Momy da ta gani. Abinci ta kawo Ashe kuwa ta yi hasashenta daidaita, sai dai wani abun ne ya tsaya mata a rai da ta kasa hadewa har sai da ta tambaya. Me ya kawo gilashinta a nan? Sato shi na yi kin san ni barawo ni Ta dan yi murmushi. Ni ban ce ba, na san bata gani sai da gilashin ne shiyasa Na bata wani, ki zauna mana Ta zauna tana jin numashinta kamar zai shake zuciyarta na bugawa da mugun karfi. Kuma ta karba? Da na yi mata ta karfi ba, kin san kanwar nan taki akwai musu da kafiya, amman kuma tana samun sa'a na duk fushin nan nawa na kanyi kokarin controlling kaina na daga mata kafa saboda kawai lalaurar da take tare da ita Yana aikin yana amsa nata da babu alamar wasa ko second thought a tare da shi. Ka taba bata wani abu kamin yau ta bata karba ba? Yayi shiru na wasu mintuna sannan ya amsa mata. Na taba bata kyautar gilashi a gabanki bata karba kin tuna? Kanenta ya hanata karba saboda ya fi ni iya fitina Ta yi murmushin karfin hali. Hamad din ne ya fika fitina? Anya akwai wanda ya fika fitina Captain Yep ai shi yaro ne yake da wannan fitinar, yayarsa ce fa amman tsoronsa take Kai ma ai kowa tsoronka yake saboda fitinarka Captain, gaskiya bana jin akwai wanda ya fi ka saurin fusata, fadar bakar magana, da kuma fitina Ya tsaya ya dubeta. Ashe haka kuke kallona, zan baku mamaki wata rana Babu wannan ranar ai Deal Deal Ta amsa tana dariya, sai ya lumashe ido ya bude ya girgiza kai. Ki wuce da kulolin Momy, kuma ki fada mata na gode sosai Tana jin haka ta san ya sallame ta kenan, that's means yana bukatar ta tashi ta tafi. Okay Ta mike tsaye ta nufi gurin da kulolin suke ta dauki wadanda zata iya ta fara kaiwa a mota sannan ta dawo ta dauki sauran. Zaka shigo anjima? No maybe gobe shi ma maybe Okay sai anjima, a sha aikin lafiya Thank you Sis, be a good girl please I will.... See you soon Ta ja kofar ta rufe masa, tare da rakiyar wani sojan ta fita gurin zancen gilashin da ya bawa Hurriya ya tsaya mata a rai, kuma yana kokarin gushe mata duk wani farinciki da take ji na sakata neman turare da yayi. Amman what if shi ba da wata manufa yayi ba? Balle ma yadda yake da halinsa anya zai iya da tafiya da Hurriya? Yarinyar nan tana da shegen kyau zata iya jan hankalinsa kamar yadda ta ja hankalin Salim, gashi har yana fadar wai ta yi sa'a yana iya controlling kansa Ta amsawa kanta da kanta tana juya sitiyarin motar, zuciyarta na raya mata karya da gaskiya deep down inside her ta san she feels jealous why zai bata gilashi bayan ta ki farko few years back, and why ma zai ce ta kawo masa abinci? Saboda kin tafi siyo masa turare Namra, shi ma abun alfahari ne zai saka turaren da kika siya masa so wannan ma ba wani abun daga hankali ba ne Ta bawa kanta amsa a daidai lokacin da masu gadin gidan suka bude mata gate. Misalin karfe 8:30pm Hurriya na dakinta kwance ta soma jin kara kamar ana jifan gilashin windows dinta, bata saka ran wani zai yi haka, wannan ya sska bata damu ta tashi ta duba ba, har sai da ta ji jifan yayi yawa, sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi windows, curtains din ta fara dagewa ta leka waje mutum ya hango sanye da kananan kaya komai fari, ta bude window tana kallon Captain dake kasa, sai ya jefar da dutsen dake hannunsa ya dago dayan hannunsa dake rike da karamin bokitin roba ya nuna mata sannan ya aje a kasa, ya nufi hanyar da kofar falon Momy yake, ta nan kam ba zaka iya hango wanda zai fito ko ya shiga falon na Momy ba. Kamar yadda wanda ke tsaye a bakin kofar baya iya ganin wanda ke sama har sai ya fito daga gurin. A bude ta bar window ta juyo da sauri ta bude karamin teburinta dake gurin ta dauko takardar da pen ta yi rubutu a jiki da girma yadda zai gani sannan ta nade takardar a hannunta ta nufi kofar fita ta bude ta sauka falon. Ko da wasa be kalli inda take ba yana ta magana da Momy dake tambayarta ya aiki. Aiki kam akwai shi kwana biyu nan, yanzu haka a gajiye nake i need to rest gobe ma da wuri zamu fara Namra ta fada min ta same ka kana ta aiki dazun, daman kuna haka ne Yeah idan ana karshen shekara da kuma canjin duty ana samun irin haka, lafiya kalau Ya karashe tare da amsa gaisuwar da Hurriya take masa, sai a lokacin ya kalleta ya dauke idonsa. Ina Namra? Tana bangaren mahaifinta ko a kira ta? No, ni ma wucewa zan yi Yanzu? Na dauka abincin dare zaka ci No na ci abinci Wallahi, har fa na shiga gida na tuna ban siye abu ba dole na fito, shiyasa na biyo nan Hurriya ta fice daga falon har da hadawa da sauri ta nufi gurin da ya aje mata karamin bokitin, sai da ta fara daga bokitin ta cire karamin tawul din dake sama sai ta yi arba da bakar leda da kuma fara har ta yi kamar zata bude wata zuciyar ta raya mata Momy ko Namra za su iya tararda ita a gurin dan haka ta aje masa takadar da ta rubuto tun a dakinta ta dauki bokitin ta juyo ta dawo cikin falon a daidai lokacin da Captain ya mike tsaye. Momy na ganinta ta fara masifa Kin fa san bana son tsautsauniya, miye haka Abun da na shanya dazun ne Ta amsa da sauri tana wucewa, Captain ya kalleta irin kallon nan na ashe ita ma ta iya karya, ita dai bata juyo ba har ta shige dakinta. Har bakin kofar falo Momy ta rakoshi kamar yadda ta saba, shi kuma ya gangara ya fara sauka yana duban gurin ya hango takarda a aje, kai tsaye ya nufi gurin ya dauki takardar Momy na can tsaye kofar falon tana son sai ta ga wucewarsa sannan ta koma ciki. Ba zan iya amfani da wannan gilashin ba, saboda Hamad ya hanani karba, idan ina amfani da shi zan ji kamar na aikata laifi ne, yana tuna min da dan'uwana dan Allah ka ba ni nawa please Shi ne rubuce a jikin takardar, kansa ya daga sama ya kalli window dake bude amman be ganta ba, daman ai ba zata bari ya ganta ba saboda ta san ta aje masa sako. Wani abun ne? Momy ta tambaya. Aa takardar dana fito da ita ce dazun ta fadi Sannan ya juya ya nufi motarsa. Momy da kin koma ciki akwai aikin da zan karasa a mota kamin na tafi Toh shikenan Captain Allah ya tsare hanya sai da safe Sai da safe Momy Ya bude motar ya shiga ciki ya zauna ita kuma ta koma ciki, a lokacin ne Hurriya ta samu dagowa ta leko window kadan ta yi saurin labewa tana lekonsa ya dade a cikin motar sannan ya fito ya aje mata takardar a daidai inda ta aje masa, sannan ya koma cikin motarsa yayi mata key ya juyata ya bar gidan, sai ta ga fitarsa sannan ta fito dakin da sauri ta sauko falon, samun falon babu kowa ya saka ta ji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, sub sub sub ta fice kamar wanda zata yi sata ta dauko takardar bata