← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 143

Sashe 6

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a gurin kawai ya sauke mata mari Oh Subhanallahi, Sannu Hurriya ina glass din naki? Cikin wani irin kuka mai tsarke numfashi Hurriya ta soma magana. Hamad.... Hamad... Hamad.. Ya fasa.. Shi.. Saboda me? Kai Hamad akwai mugun hali ita Iyami tana aikin me yayi miki haka? Line by line ta fada musu abun da ya faru tun a school har dawowarsu gida, ciki har da tafiyar Amma da hudubar da ta yi musu. Ciki wani yanayi na damuwa da rashin fahimta da kuma faduwar gaba a lokaci daya Yassar ya kalli Hajiya Kaltume, Hajiya Kaltume kuma ta juya ta kalli arta Umm Khairi, suna ha a ido fuskarsu ta soma fadada da murmushi, tunawa da Yassar na dakin ya saka Umm Khairi ta fara tarin karya, Hajiya Kaltume kuma ta daure fuska. Yassar da ya tattara hankalinsa gaba daya gurin kanwarsa Hurriya ya ce Kamar ya sai ta haihu zata dawo? Haka tace mana, kuma bata jima da tafiya ba, har ya fara min duka, Wallahi kashe ni zai yi idan muka zauna a can mu kadai Ya kalli Hajiyarsa cikin yanayin damuwa sai ta girgiza masa kai alamar bata san komai ba, hannun Hurriya ya rika. Zo muje part din na ku Har lokacin kuka Hurriya take tana biye da yayanta dake rike da hannunta suka fice. Umm Khairi ta sauko da sauri tana murmushi ta dafa Hajiya Kaltume da ta kai zaune baki har kunne tana mamakin jin kalaman Hurriya. Hajiya Appa ya saki Amma kenan? Ina kyautata zaton haka, domin dazun da safe shi ya kira ni da kansa ya ce min na dauke Bedsheets dinta na kawo masa abun karyawa, har na ce masa bana son ta ga kamar ina shigar mata hakki, sai ya ce min baya son digon zance zan karbi girki a yau Umm Khairi ta rumgume Hajiya Kaltume da sauri tana murna. Wayyo Allah na dadi, amman me yasa ba ta fadawa Hurriya gaskiya ba? Waya sani? Toh ko ganin take zata dawo? Zama be gan ni ba ungo wannan kai min Kitchen bari na kira Hajiya Fatee Ta mike tsaye da sauri, daga ita har yarta Umm Khairi kallo daya zaka yi musu ka fahimci farinciki dake zuciyarsu, da rawa Umm ta karasa kitchen ta aje plate din ta fito ta shiga dakinta ta dauki wayarta ta fara kiran yan'uwanta da basa gidan tana musu albishir domin sun dadi ba su samu wani labari mai dadi da faranta zuciya ba irin na yau. Hajiya Kaltume na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta saka key dan tabbatar da ita kadai ce a dakin sannan ta nufi wayarta cikin nauyin jikin dake hana masu kiba da teba hanzari a duk lokacin da suka yi yunkurin yin haka. Sai da ta fara zaunawa sannan ta dauki wayar ta lalabo number aminiyarta Hajiya Fatee duk kuwa da kasancewar ta girme ta nesa ba kusa ba, sai dai friendship be duba age ko level idan jini ya hadu, cikin natsuwa Hajiya Kaltume ta aika mata da kira, zuciyarta har wani bugawa take irin na jindadi da farinciki da tun da aka auro Iyami rabonta da irinshi. Assalamu Alaikum Hajiya Kaltume Na'am Hajiya Fatee ke kadai kike? Ni kadai nake yanzu yar iskar yarinyar nan ta fita Ba dai Afra ba? Ita fa Ikon Allah yaushe kuma ta fara zuwa gidanki? Yanzu fa, ina zaune sai gata ta zo ita da yara wai an zo a gaishe ni, waya sani ko wani mugun abun aka kullo min a kawo min, ta mallake ni kamar yadda ta mallake min Tsab kuwa zata iya shi, indai magani ne wannan yarinyar babu inda bata sani ba, gashi ta tsaneki ko maganin mutuwa ma zata iya miki Kamar an yi a gabanki, ai an sha fada min ta yi ta yi samun sa'a ne bata yi ba, shiyasa na tsaya a kafata bana wasa kar ta jedar da ni a zuciyarsa kuma Wallahi idan ina da rai sai Fadil ya kara aure To ke Hajiya Fatee anya wannan shedaniyar surukar ta ki zata yarda ta bar Fadil yayi aure? Hajiya Fatee ta yi dariya. Hajiya Kaltume kenan kina magana kamar baki san wacece ni ba, ai idan ta kwana da shiri wani a hanya ya kwana, daga ita har uwarta sai sun kyale min ana, komai shige shigensu da tsafe tsafe da yardar Allah sai hankalin Fadil ya juyo kaina ni ma sai na sarrafa ana yadda nake so Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana kara yarda da zancen Hajiya Fatee. Na yarda da haka, domin a yanzu na sarawa lamarinki, ni yanzu ma kira na yi na yi miki albishir, dazun da safe Alhaji yake ce min na kawo masa abun karyawa na cire Bedsheets din da Iyami ta saka, ni tun a lokacin na san wani abu zai faru, kuma na tambaye shi lafiya be fada min ba, yanzu kuma Hurriya ta shigo tana kuka wai Hamad ya daketa a nan take fada mana Amma bata gidan wai ta tafi gidansu har sai ta haihu zata dawo Hajiya Fatee ta daki cinyarta da karfi ta kyalkyale da dariyar eta da jindadi. Ke daga jin haka ai kin san abun da muke nema ya samu, ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha, kuma gadon ari sai fanna, sirrin iya sai mar ibo, yanzu kam sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya tada kai yayi kallo, ai na fa a miki kowa yace zai iya ha eye gatari to sakar masa ota, kuma idan ta sha mu ba mu karya ba, yaro baya ja da mu muja da ubansa... Haka Hajiya Fatee ta rika jero kirari da karin magana cikin alfamari da tin aho. Hajiya Kaltume ta mi e tsaye ta fara yawo a akin tana jin kamar ta taka rawa. Wallahi sai a yau na ji wannan unci da nauyin da ya tsaya min a zuciya ya sauka, tun da Alhaji ya auri Iyami farinciki ya gagareni, duk wani abun da zan samu a duniyar nan farincikina raggage ne, saboda Iyami, yarinya daga zuwa aiki kin aure mai gida har da su a gashi ya murje ido ya nuna kamar ya fi sonta da kowa, anta ma kamar ya bude ciki ya saka su ya rufe haka yake ji Toh daman ina ke ina kwanciyar hankali da farinciki Hajiya? Mai aiki ta aure miki miji? Ai haka suke shiyasa ake cewa an iska na birni shege na kauye sai tsoron ansa, ai da zarar sun yalla ido sun ga ana jindadi a gida to sai sun aure miki miji, ita wannan shegiyar gorar Afra da ta fahimci duniya kin ga duk bokonta bata son ko mai raino balle kuma wata mai aiki Tana da gaskiya Wallahi, sai dai haka kuma ba zai hana an mu kara aure ba Aure kadai? Ai sai ta bar gidan nan matukar ina raye, duk wata mallaka da ta yi ma ana sai na kwance ta, kuma ki zuba ido ki gani ba dai wannan Malamin ya iya aiki ba zaki sha mamaki Yanzu so nake ki shirya mu kai masa sallama kuma na sake fada masa bukatar domin ina gudun kar ya maida ita Karki damu, bari sai kura ta laba zamu sake komawa, daman ai na fada masa duk abun da aka ba shi karin alkalami ne kawai, biya sai bukata ta biya Lallai kuwa zan masa biya mai kyau, domin ya yaye min bakincikin da nake kwana na tashi da shi, a kullum burina Iyami ta tafi ta bar min miji, yau kuma wannan burin ya cika Alhamdulillah Dariya suka yi a tare sannan Hajiya Kaltume ta yi mata sallama ta sauke wayar tana jin kamar an mata bushara da gafara. [10/18, 5:34 PM] Nana 1: Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Shi ne abun da Hajiya Binta take ta nanatawa idonta a rufe domin danta be zo mata da labari mai dadi ba, a cikin matansa daga wanda ta rasu har wadanda suke a gidansa yanzu babu wanda take so irin Iyami, domin macece wadda ta san kanta take bata girma take rawar jiki da ita tana kyautata mata kamar uwarta. Subhanallahi Tsoho baka kyauta ba, ka yi gaggawa kuma daman gaggawa aikin sheidan ne, ina ma baka aikata ba ka dan daga mata kafa ko kuma na turata gidansu har sai ka samu natsuwa Cikin wani kalar rauni da rashin sukunin abun da ya aikata ya sake noce kansa kasa ya sauke ajiyar zuciya. Hajiya natsuwar ce ta gagare ni samu, ba yau na fara jin bana da sukuni idan bana tare da Iyami ba, ji nake kamar wani abu ne a saman kaina, sai a yanzu da na sauwake mata sannan na ji nauyi ya sauka, ni kaina ina son Iyami amman bana jin natsuwa a zamantakewarmu yanzu, kuma na yi ta addu'a ina fatan samun sauki abun amman hakan ya gagara wata kila sakin shi ne mafi alheri daman aure rai ne da shi Har saki nawa ka yi mata tsoho? Daya na yi mata Hajiya To da sauki idan abubuwa suka daidai wata kila za a iya gyarawa, ko dan yan diyanta Tsoho, dubi Hurriyya da Hamad ga cikin dake jikinta yaran nan ba za su taba jindadin zama a gidan idan bata ciki ba, ko ma kallon iyayen kowa na nan ta su bata nan sai ya saka su jin wani iri In Sha Allahu zan ba su duk wani jindadi da farinciki da yaya suke bukata a gurin uwa da uba, ban taba fadar maganar nan a gaban kowa ba sai yau a gabanki, Hajiya duk cikin yayana na fi kaunar Hurriya, saboda kokarinta ga kuma lalurar da take tare da ita, Allah ya saka min tausayin yarinyar nan, fitowa daga gida zuwa nan Wallahi yaran nan kawai nake ta tunani a raina Tsoho Ta kira sunansa sai ya dago ya kalli mahaifiyarsa da fatar jikinta ta fara zazzaga saboda tsufa. Dan Allah idan ka samu sukuni ka dawo da Iyami dakinta, ko ba komai ta saba da rayuwar jindadi ga kuma ciki ga tunanin yaranta be kamata ka saka mata da haka a irin wannan lokacin ba, idan ma baka yi hankali ba tana cika idda wani
Chapter 6 · 0% Book details