Sashe 133
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mu zo mu dubaka mu koma, direban ma yana waje Wacecw Gwaggo? Kakar Hurriya mahaifiyata Captain ya dariya. Ashe ma kaka ce, idan kin koma ki fada mata mijinta ya riketa, daman ya fi Kaka iko da ita Zata min fada Fada kadai zata miki ashe, Wallahi Hurriya ba zata koma yanzu ba, akwai maganar da zan yi da ita so ki tafi kawai karamar uwa madaukar zunubi Babu yadda Rukayya ta iya bayan yi masa fatan samun lafiya ta fice daga dakin Hurriya na ji kamar ya ce mata kar ki tafi. Captain ya matsa kusa da Hurriya jikinsa na taba nasa daman ficewar Rykayya kawai yake jira. Ni kike gudu? Ta yi shiru tana jin kunya na rufe ta, sai ta ji dakin yayi mata girma daga ita sai shi daman tana jin alamar kamar su kadai ne a ciki. Ya saka hannayensa biyu ya zafaye ta ya dora wuyansa a kafadarsa. Fada min ya kike? Lafiya kalau Ta amsa da sauri, tana kin bashi hadin kan tsuma yatsunsa a cikin nata. Ya sumbanci kuncinta ya kalli gefen fuskarta yana kai dayan hannunsa ya taba Lips dinta Ki yi hakuri na mari dukiyata na fasa bakin nan da kaina, ban jidadi ba I'm sorry Ba komai ya wuce Ta mike tsaye tana jin wani iri, ya sauke kansa kasa yana murmushi kamin ya mike tsaye ya koma gabanta ya tsaya ya dafa kafadarta. Alhamdulillah komai ya wuce a yanzu ko? Ya wuce a cikin gida, amman yana nan a duniya za'ayi ta kallona da abun ko da na bar duniya Ya kura mata ido kamar mai kokarin kure kallonsa. A hankali ya zaunar da ita ya zauna gefenta ya saka hannunsa a cikin nata ya kwantar da kanta a jikinsa. Abu mai muhimmanci a yanzu, mahaifinki be yarda kin aikata mahaifiyarki ma haka, Ubangijinki ma ya san baki aikata ba, mijinki ma haka duk wanda zai zargeki a bayansu ba shi da amfani Kai ma ka yarda ban aikata ba? Yayi dariya marar sauti ya dagota daga jikinsa ya fuskance yana kallon kyakkyawar fuskarta. Na yarda amman ban tabbatar ba Zan iya rantse maka da kur'ane kamar yadda na yi ma Appa Ban karyata ki ba ai, zan tabbatar da kaina, na gaba kadan Yaushe? Me yasa ba saka tabbatar a yanzu ba? Kin matsu ne? Ta daga mishi kai a bakin gaskiyarta, sai ya saki hannunsa ya mike tsaye yana murmushi domin ya fahimcin bata gane dawon garin ba. Kofar dakin ya nufa ya bude ya leka hagu da dama sannan ya dawo ya tsuguna a gabanta hananyensa a cinyarta yana kallon fuskarta a dora, sai fara kokarin mikewa tsaye tana ture hannayensa. Babu wanda zai ce wani abu a nan, ni mijinki ne, halak malak, ni zan bawa duniya shaidarki daga yanzu har karshen rayuwarki Ya kama yatsansa yana murzawa a hankali. Mai tsada na yi yadda zan iya na ga mutunci ya karu a idon duniya, na iya kokarina na saka an goge hotunan wadanda suka wallafa hoton sun goge, sai dai wadanda ban sani ba Ya sumbanci hannayenta duka biyu ya saka su a fuskarsa. I will fix what they broken, zan zama zama hasken da zai haska duhun dake rayuwarki, zan yaye miki damuwarki, zan saka ki yi alhari da ni a matsayin miji, da ace zan iya sauya lokaci na koma baya da na rayu da ke tun kurciya har tsufa, saboda ina bukatarki a rayuwata, i will spend every hour of the day keeping you safe Hurriya, na miki wannan alkawarin Hurriya, zan baki wata duniya mai cike farinciki, duniyar da babu kuka babu damuwa babu tashin hankali babu tsana babu kiyayya.... Hawaye ke sauko mata jikinta yayi sanyi, ba a taba siyeta da kalamai masu dadin irin na yau ba, wani be taba yi mata kalam kwantar da hankali kuma ta ji hankalinta ya kwanta ta samu natsuwa irin yau ba. Is Okay is alright.... Ya mike tsaye ya zauna kusa da ita ya share mata hawayenta. Ban taba fada miki wannan ba Hurriya, bari na fada miki yau.... I LOVE YOU... INA KAUNARKI HURRIYA fiye da duk wani namiji da ya nuna miki soyayya a duniyar nan Wasu hawayen ne suka sake zubo mata, sai ya kai bakinsa ya sumbanci hawayen nata ya hade goshinsa da nata yana goga mata hancinsa, numfashinsa da nata yana tarayya. Ina jin wannan din ma kamar mafarki ne Ta fada cikin sautin kuka, sai ya dora bakinsa akan nata ya rufe ido. Gaskiya ne... Zahiri ne wannan Hurriya... Lokacin da Daddy yace min mai tsada ta zama taka sai na ji kamar ba a taba bani farinciki irin na ranar ba, saboda ke ce Hurriya Yana maganar lips dinsa na taba nata, kamin ya bude idonsa yana kallon nata idon dake rufe. Sannan ya sumbanci banki ya sumbanci hancin ya mike tsaye ya dauko wayarsa ya dawo kusa da ita ya zauna. I have another surprise for you Ya kunna mata video sanin bata iya gani sai ya kara mata muryar a kunne. Kamin ta gama saurare hawaye ya jika gaban hijabinta, sai ta kasa jin farinciki kuma ta kasa jin bakinciki ta tsaya a tsakiya tana jin ba gaskiya ba ne. Taya yar'uwa ta jini da uba mai daraja ya hada su, zata aikatawa yar'uwarta wannan abun? Ko dai sheri yake mata? Na san Yaya Khairy bata shiri da ni amman wannan yayi muni, mai kiyayya da ta yi zurfi da kai ne kawai zai iya aikata wannan! Idan ma bata raga dan ni ba ai ta rangwanta ko dan mutuncin gidanku, a karkashin inuwa daya muke da ita wannan abun ya taba mutuncin kowa a gidan bata gane ba? Na ma kasa yarda ita ce ta aikata haka Captain ya rumgume ta, domin kukanta a yanzu yana daga masa hankali. Zamu kara tabbatar da hakan nan gaba kadan, gaskiya zata kara bayyana Hurriya ya rushe da kuka a kirjin mijinta ta kamkame shi. Na tuna... Na tuna ranar da ta fita da ni... Ranar da tace na raka ta gidan kawayenta, Yaya Khairy ta cuce ni yar'uwa ta cutar da yar'uwarta ta jini, me na mata amman me na mata Captain ya dagota jikinsa da sauri ya rike fuskarta da hananyensa. I know this not easy, baki mata komai ba Hurriya, makiyinka baya bukatar ka yi masa laifi sannan ya hukuntaka baki mata komai ba Ta saka hannu ta rufe bakinta tana girgiza kai, yayi mata nauyi yyi mata muni ace yar'uwarta ce ta aikata haka. Ya sake rungume. Shiiiiiiiiiiiiiiiiiii wannan ya wuce yanzu, ita ya kamata ta yi kuka ba ke ba Be dagota daga jikinsa ba sai da ya tabbatar ta daina kukan. Sannan ya dagota daga kirjinsa ya kalleta. Kin rame wannan abun ya saka miki damuwa sosai, yaushe rabon da ki ci abinci Ta kasa yin magana. Ya shafa fuskarta. Kina bukatar cin wani abu? Ta girgiza kai. Kwanta a nan ki huta Ya kwnatar da ita kan gadon na dora mata kafafuwanta sannan ya subancin fuskarta goshinta da saman idanuwanta da suke rufe. A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya matso da kujera ya zauna yana kallon fuskarta, ya matsa da kujerar ya shafa fuskarta zuwa hancinta yana gaba lips dinta. Can kuma ya matsa baya ya kalli drip din da ya cire dazun, sai ya janyo karfen ya maida ruwan da kansa ya daidaita komai a yadda yake, kana yayi relaxing akan kujerar yana kallon kyautar da Allah yayi masa. Ajiyar da na baki ajiya ce ta har abada, na gode da kika ba ni hadin kai, lallai kasancewa da Hurriya abu ne da kike muradi, akwai farinciki a auren matar da kake so kake tausayi... Na ji hakan yau, na yarda na karba na aminta wannan din mai tsada ce, ta canja min siffa, ta sauyan lissafina ta rike linzamina... I will take every risk for her, i will bend the rules... Thank you.... She's my world... My Hayatie... My Rayuwa.. Thank you for this cause I know you feel the same... Yana maganar hannunsa dafe a saitin da zuciyarsa take aje, idanuwansa kuma suna ta bawa abun da ruhi yake bukata... Mursa kofar dakin da aka yi ne ya saka shi juyo sa kai ba dan ya gundura da kallon rayuwarsa ba ya kalli kofar. Daga Momy har Ammy Momy Ikilima da Hajiyar Maru tsaye suka yi suka kallon ikon Allah, Hurriya na kwance a kan gadonsa shi kuma yana zaune a kujera da drip a hannu. Minene haka? Me yarinyar nan take yi a nan? Waya kawo ta? Ammy ta tambaya a tsawa, Hajiya Maru ta yi hanzari tariyar numfashinta. Turai ki saurara mana Hajiya haba mana? Yaron da bashi da lafiya aka kawo asibiti shi ne za a kawo ta? Shi yana zaune a kujera da ruwa a hannu ita tana kwance a gadon asibiti? Makauniyar me zata masa? Hurriya ta zabura ta tashi zaune da sauri sai kuma ta sauko ta yi tsaye gabanta na bugawa da karfi, bata san su waye ba, bata ji muryar wadanda ta sani ba, gashi bata gani balle ta matsa daga gurin. Captain ya mike tsaye ya kalli mahaifiyarsa cikin damuwa. Haba Ammy kamar baki san wacece ita ba? Kin tsorata ta kuma ba laifin be laifina ne... Really..... Ammy ta furta tana masa kallon mamaki, sannan ta juyo ya kalli Captain din ta saki jakar dake hannunta. The only thing you care about is her, baka yi tunanin ya zan ji idan na ganta ba? To na bar mata sai ta yi jinyarka Ta juya ta fice, Hajiyar Maru ta bi bayanta tana kiranta, Momy kuma ta duka ta dauki jakar da Ammy ta saki tana yi ma Captain mugun kallo sannan ta juya ta fice, Momy Ikilima ce kadai ta iya karasowa ta aje kayan dake hannunta ta kalli Hurriya ta kalli Captain sannan ta fice cike da takaici. Captain ya kama hannun Hurriya ya rike Karki daga hankalinki da yawa Hurriya when i meet you i tell myself that i will love you and protected you at any cost.... Hurriya ta sake hannunsa ta dan matsa baya. Yaya... Ina son na tambayaka... Ask me any question, zan amsa miki Ina masu