Sashe 137
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasu abubuwan Gwaggo zata tafi tare da Hindu Lagos su siyo (Duk mai bukatar kayan kitchen, Bedsheets da kayan kawata falo ko daya, akwaituna da kayan lefe kamar su laces shadda atamfa materials da Shoes and bag, sarka yan'kunne turareka zai samu a gurin Khadeeja Candy Store cikin sauki da rahusa, muna aikawa ko'ina a fadin Nigeria da sakashen dake makota da mu kamar irin su Nijar Togo da Ghana cikin aminci da yardar Allah, mai bukata sai ya tuntube ni a business line dina kamar haka :- 080361266660) Appa ya sauke ajiyar zuciya jin kamar Amma bata fahimci inda ya dosa ba ya ce. Kayan daki nake magana kamar gado da kujeru da sauran abubuwa na cin abinci, gidansa da ke Kaduna za a iya siya a Kd a saka a can ko kuma a siya daga Kano a kai can, da son samu ne ma a siyo mata komai a waje na fi aminta da kayan can fiyeda na cikin gida A Kanon ma babu kalar kayan da babu, suna dauko kayan waje domin saukakawa masu gaggauwa ba sai an kashe kudin jirgi ba wata order ma sai ka yi bata iso da wuri ba, zaka iya zuwa Kano ka duba mata Da zamu tafi tare ai da zai fi domin ke ce idonta a yanzu, kuma duk yadda zan yi zabe ba zai kai ga ke yadda zaki zaba ba Babu wata hujja da zata saka na shirya baka tafiya da kao Alhaji ko dai ka manta ni din nan ba matarka ba ce? Ba daga ni sai ke nake nufin tafiyar ba tare da familynki, shiyasa zan baki dama ki yi shawara da su daga nan zuwa gobe abun da kika yanke sai ki fada min To shi ke nan mu kwana lafiya Yayi saurin dakatar ta ita daga kokarin yanke wayar da take. Idan ba zaki tsaya mu gaisa ba, toh ina yarana Hassan da Husaini? Sun tafi Islamiya Hurriya fa bata kusa? Rukayya karbi mikawa Hurriya waya Amma ta cire wayar a kunnenta ta mikawa Rukayya da ta mike tsaye ta nufo gurin da suke zaune ta karbi wayar ta fice daga dakin zuwa dakin Bappa da Hurriya ta shiga dazun tana ganawa da kakanta. Ka ji min wata magana wai Hajiya Binta dake Saudi gurin Ummara ta ce masa zaben kayan daki na mace ne Baaba Uwani wadda ta kasance kanwa ga Gwaggo ta bude hannayenta jin an sosa mata gurin dake mata kaikayi. Daman ai na fada, dama nan ya bar zabin komai zai fi, domin dai zaben Kaltume ko wannan Hajiya Nafisa ba za su zabo ma Hurriya abun kwarai ba Daman ni ban saka ran da Kaltume za a je ba, domin babu aure yanzu tsakaninsu, Nafisa nake saka ran zata taimaka masa gurin zaben kayan ita na san ba zata zabo abun kirki ba domin ba son Hurriya take ba kuma tun da aka daura auren nan har yau bata tako gidan nan ba Hindu dake bude gi a ta ce Da gaske wai bata zo ba? Amma ta waiga ta kalli kawar da za'a iya cewa yanzu ta zama yar'uwarta ta ce. Wallahi bata tako ba, kuma kin ga ko cikin danginsa da suka zo bata biyo su ta zo ba kuma bata zo ita kadai ba Namra ma bata da tako nan ba Allah da iko yake, da alama ma fa ita ma bata son auren nan, ke bi ba dan na ga yaron ba tubarkalla Maa Shaa Allah da shi da zan iya cewa aura mata shi aka yi saboda sun ga ba mutunen kwarai ba ne, ina fatan dai an bincike halinsa ba shi da wani nakassu Ta karasa zancen tana jefa gi a abakinta. Amma ta an ta e baki. Bashi da shi gaskiya domin shekaran jiya kamiN Hajiya Binta ta wuce Ummara ta zo gidan nan yi mana bankwana take fada mana Appan Hurriya yayi saka an masa bincike a akan yaron ta hallayarsa ta zamankewa da mutane kuma ba su ji wani aibu ba, Allah ne fa ya wanke Hurriya kuma yayi mata sakamako da wannan, ki duba ko video nan na Khairy yanzu da ya cika gari Appanta yace shi ne ya shiga ya fita ya ga komai ya warware, an goge hotunan Hurriya ta inda zai iya kuma ya saka suka bata hakuri, kuma shi ya cilastawa yaron fadar gaskiyar abun da ya faru, kina jin yadda aka daura auren nan da sadakin kin san abu ne kawai min indin Allahi, karki so ki ga yadda ya zo gidan nan, baya ma iya daga ido ya kalleni, son kakarsa ma ta zo ita da abokiyar zamanta da kanen mahaifinsa su biyu da yayar mahaifiyarsa dukansu kuma ban ga wani abu a tare da su ba, idan ba dayar ba dake ta hankada tana harare-harare Gwaggo da ta gama sallame sallah a yanzu ta ce. Daman ai ba za a taru a dangi ace kowa sai ya so ka ba, dole za a samu wanda ba ya ra'ayinka, balle dai yadda yaron nan yake ba za su rasa matar ba shi ba Gwaggo ai gabanki Hurriya ta fada mana yadda Namra da Momy suka mata gargadi akan yaron, ashe dai shi ne mijin ba su sani ba Amma ta fada tana mike kafarta da har yanzu bata gama warke mata ba, tana kallon Gwaggo ta cire hijabinta tana fadar Ki kwantar da hankali ki cigaba da yi mata addu'a ita ma kuma ta cigaba da yi domin ba bari abun da aka zaba za'ayi ba musamman Kaltume Allah kadai ya san hassadarta akan auren nan, kuma kin ga Saurayi ne ba mai mata ba balle ki daga hankalinki da tsoron abun da zai biyo baya Ko mai mata ne ma Gwaggo ya zan yi tun da mahaifinta ya riga ya bada ita? Ai babu yadda zan yi sai hakuri, dan yasan Hurriya ata ce ai ya saka shi yin haka, da Momy ce ko Kaltume ba zai taba yi ma yaransu haka ba a daura aure ba tare saninsu ba, kuma na ji dadin da be bawa kowa siyayyar kayan ba ya kawo kudin nan yace a siya komai Yanzu fa ya dawo hayyacinsa kina ganin yadda yake rawar jiki da yaran nan wai ni me yace ma kiran da yayi yanzu na ji kina masa zancen ya siya can? Amma ta fadawa Gwaggo abun da ya bukata, Hindu ta kyalkyale da dariya, Gwaggo da Baaba uwani suka yi murmushi. Ba wani nan shiri yake nema, yana son ya kyautata miki ne kuma ya samu kanki Amma ta tabe baki tana wofintar da zancen Hindu da be kama kanta ba. Hindu ke dai baki rabo da zance a bakinki, ni yanzu ina ni ina Alhaji Haruna? Daman can kaddara yara ce ta kaini kuma an haifa, Wallahi yanzu ni baya gabana gidansa be burge ni sam, ke ni fa auren ma ya fita a raina ma gaba daya na wasun mazan ma, balle na Alhaji Haruna mai mata irin Kaltume ko makiyi ba zan so ya zauna da kishiya irin Kaltume ba, kamar dai kun manta inda aka fito? Magana wannan ina son na yi amman na kasa daga kwance sai kwance babu abun da zan iya kawarwa bayan an raba ni da aurensa an juye kansa, hakan duk be wadata ba aka koma a gurin yarana? Shi kuke gani da fatan zan iya komawa? Ai har abada...! Allah dai ya zaba abun da ya fi alheri amma mace ai bata cewa ba zata sake aure ba, kuma idan da yara ko an rabu kamar ba a rabu ba ne yanzu ba gashi ba? Kuma idan baki koma ba ai ita Kaltume ta samu abun da take so kenan Cewar Gwaggo domin ita ma a yanzu ta gano zaman auren ya fi babu, ko da wani namijin ne balle kuma uban yayanta da aureta tun tana budurwa gashi har an kai ga aurar da Ni dai na hakura da Alhaji Haruna, idan har auren alheri a gare ni a gaba Allah ya kawo min wani mai mutunci da sanin ya kamata, kuma ya ba ni abokiyar zama ta gari Amin, idan kuma akwai alheri Allah ya maidake dakinki Iyami, ko dan yaranki, nan gaba kadan zai ce zai karbi yaran nan kuma idan baki a gidan ba za su jidadi ba, ni dai a matsayina na mahaifiyarki ina rokon idan ya nemi maida aurensa karki juya masa baya dan Allah Amma ta kalli Gwaggo idonta na cika da hawaye. Gwaggo ban manta wahala da azabar da na sha saboda auren bawan Allah nan ba, kuma ke da kanki kika ce inda shi ne ba zan koma ba, ko da fari ku kuka karfafa min guiwar aurensa kuma... Kuma hakan be haifar miki da komai ba sai alheri, ki rika duba wannan ina son ki sani ita kaddara a rubuce take ko da Kaltume ko babu ita sai kin yi irin wannan ciwon sai haka ta faru, ita dai ta zama sanadi ne kawai kuma yanzu gashi ai kin samu sauki jinyar kuma ta zame miki ibada, bari na dubawa Hurriya maganin Infection da muka siya gurin UMMU SA'ADA WOMEN'S SHOP 09160547983 Gwaggo ta mike tsaye ta fice daga dakin tana amsawa Baaba Uwani dake yaba kyau maganin na infection. Ai da yana da daci ko tsami ma Hurriya ba zata yarda ta sha ba, yadda na san Hurriya da son zaki ba zata sha ba idan yana da daci Cewar Amma tana share hawaye Hindu ta ce. Shiyasa ai nake jindadin maganinta, ba shi da daci kuma baya saka zawo ko tashin zuciya ki sha abinki kamar kina sha tea, ga aiki a jiki kuma gashi da saukin kudi daga 500 yake farawa har zuwa sama za ki ga yadda wanke marar mutum ta yi tass shiyasa aka ce kar mai ciki ta sha, gashi har kala biyu take yi da mai kamshin takafarnuwa da wanda ba shi da shi, saboda wasu basa son masu warin tafarnuwa, kuma zaka iya sha tare da miji da yara matukar sun haura shekara biyar Gaskiya na ji ana yabon maganinta, mu ma dai mun fara ganin aikinsa a yanzu, Allah dai ya sa a