← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 143

Sashe 104

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a yau ta kara yarda da tabbatar da ko wace a a duniya gatanta uba ne, ko magana yake maka mai dadi zaka ji ka fi kowa rabo da dace a duniya. Hurriya ina tunanin dawowa da yaran nan a gidan nan, saboda ita can ba lafiya ta wadace ba, kuma ni ba wani sanina suka yi sosai ba, yadda nake rayuwa da duk yarana su ban yi rayuwa da su a haka ba, ya kamata su dawo nan ni daman bana son rikon a a gurin kowa, na fi son yarana suna hannuna, ballantana kuma su da suke kanana, yanzu suke bukatar gata Da gaske Appa ne yake wannan maganar ko kuma dai mafarki take yi? Shawararta yake nema ko kuma fada mata ne yake abun da zai faru? Ta juyar da fuskarta ta matse kwalla sannan ta juyo ta ce. Za su fi jindadin zama a can Appa saboda Amma tana can kuma Gwaggo zata kula da su sosai Sai a lokacin Appa ya dago ya kalleta. Ga ki zaki iya kula da kanenki ai kamin a sama miki admission, kuma za a iya daukar mai aiki ta kula da su, amman maganar gaske ni bana son zaman yarana a ko'in sai a gidana Tabbas haka ne, ba ita kadai ba kowa ya shaida hakan a familynsu Appa baya bada rikon yayansa ga kowa ko da kuwa Hajiya Binta ce da ta kasance mahaifiyarsa, shiyasa a lokacin da aka haifi yaran be je duba su ba kuma be je duba mahaifiyarsu ba ya baya kowa mamaki, sannan ya kyale su be tana cewa bari ya dauko su ko shi ya tafi ya gansu ba. Wani mamakin be kamata ba sai da Appa ya katse mata hanzarin tunanin da take ta hanyar aje mata kudi mai kauri a dan space din dake tsakaninsa da yarsa. Ki bawa Hassan da Husaini wannan, kuma ki musu magana ina son zan shigo mu gaisa da yarana Toh Appa Wannan karon bata iya taimako kanta ba har sai da hawayen suka zubo mata, ta dauki kudin ta bude motar ta fita ta shiga cikin gidan. Appa na zaune a motar yana kallon kofar gidan ya takure fuskarsa a yanayin damuwa kamar mai tunanin wani abu, can kuma ya sauke ajiyar zuciya. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Allah ka raba mu da aikin dana sani Ya fada yana kallon twins din da Hurriya ta fito tana rike da su ta nufo motarsa. Bude gefensa yayi sai suka zo da gudu kamar wasu wadanda suka saba rayuwa da shi, suka shige motar suna murna. Jinin alakar uba da a ya saka sun wayanci shi din ubansu ne tun a ranar da Rukayya ta tafi da su har suka kwana a gidan, daman kuma Gwaggo na nuna musu hoton mahaifinsu a wayar Rukayya saboda su san shi ko da ba su rabe shi ba. Gwaggo tace na kawo maka su ka gansu Hurriya ta fada cikin rashin jindadi domin bata so Gwaggo ta hana shi shiga gidan ba. Appa yayi murmushi domin shi ba yaro ba ne ya gama fahimtar komai a kawo masa yaran da aka yi a waje. A haka ma na gode, na jikin Iyami? Da sauki.... Me yake damunta? Hurriya ta yi hankali da wayon sanin ba komai zata fadawa mahaifinta ba dan haka ta ce Ba wanda ya sani har yanzu An bincika komai nata lafiya kalau? An bincika amman yawanci suna cewa hawan jini ne, ya saka jikinta yayi haka, tana shan magani kullum sai dai har yanzu babu sauyi Appa yayi shiru ya sauke ajiyar zuciya. _Hawan jini? Wata kila saboda ni ne_ ya fada a ransa feeling guilty. Kadan ya taba wasa da yaran ya sauke su a motar saboda jiran da ake masa gurin kasuwancinsa. Hurriya ki yi magana da Gwaggo, idan ta aminta an ba ni dama sai mu fitar da ita waje ko za a dace Appa da gaske? Hurriya ta amsa da karfi, sai ya daga mata kai da dan damuwa a fuskarsa. Da sauri ta saki hannun yaran ta fada motar ta rumgume shi ta fashe da kuka. Appa na gode, Alhamdulillah Appa na gode da ka sake nuna mana kulawa, kada Allah ya kawo wani abun da zai tare idonka daga son farincikinmu.... Kuka take sosai da ya saka zuciyar Appa karaya, Direban ya juyo ya kallesu kadan yana jin tausayinta, daman ya dade yana tausayin Hurriyya da halin da yake ganin tana ciki. Hakkina ne Hurriya, abun da ya kamata na yi ne tuntuni, kuma In Shaa Allahu zan yi Ta dago daga jikinsa. Na gode Appa Ta fita daga motar ta rufe masa, direbansa ya juya motar suka bar unguwar. Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 35 Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660 Hindu ta rike haba tana mamaki. Shi da kansa? Gwaggo ta amsa mata Ni ma abun ya ba ni mamaki, sai dai ba a mamakin ikon Allah, kuma daman shi maganin dan kwana arba'in ne, idan ba a zafafa ba to sanyi yake daga nan har ya karye Hindu ta taba hannu. Hmmm a haka ma mun gode Allah mutunen nan ya fara dawowa hankalinsa mugun abun ta na magani ne ya koma mata Ya fa koma, yanzu haka saki biyu yayi mata kuma idan na yanzu aka sallame ta ba tana can asibiti kuma an ce be je ba Hindu ta daki kirjin idonta a waje tsabar mamaki har da su gyara zama. Ya saki Kaltume fa kika ce Gwaggo? Wallahi Hindu ya daga hannu sama. Allah na gode maka da baka kashe ni ba sai da na ga wannan ranar, sai ta dandana ta ji idan akwai dadi, wulakancin da ta saka aka yi ma Iyami yau an mata shi, Allahu Akbar Allah baka da dole, Allah na gode maka Ni ma dai haka na ce, kuma karshenta ba zai yi kyau ba domin ba, domin hakkin Iyami ba zamu yafe ba kuma ga Hamad ma zai bibiyeta Shiyasa aka ce idan zaka haka ramen mugunta ka gina gajere, ba a farinciki da mutuwar aure amman na jidadin mutuwar na Kaltume, saboda ta san yadda ake ji yanzu, dazun da ya zo har fadar yake wai a min magana yana son ya fitar da ita waje Hindu ta kara girmaman lamarin Ubangijina. Tabbas wanda ya aje kayansa a gurin Allah baya kunya, kuma mai hakuri mawadaci, gashi nan Alhaji ya fara dawowa hayyacinta, Allah mai iko, ai tun da kika ce yace a kawo masa yara su gaisa na san asiri ya fara karyewa Hurriya tace ya fada mata zai dauke yaransa ya maida su gurinsa, ni kam ba zan yarda ba aje a musu wani sherin kuma karshen daga haka zai iya cewa saboda Iyami ta koma Ah.. Gwaggo to ai abun da muke nema kenan, Iyami ta koma gidan Mijinta ta rumgume yayanta ta haifo masa wasu, idan bata koma ba ai bukatar Kaltume ta biya ta samu abun da take so kenan! Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya ta girgiza kai. Hindu ba zan iya da sha'anin magani ba, mace idan aka ce miki tsafi take a gidan mijinta to zaman aure baya dadi ga abokan zama, kuma ba fasawa zata yi ba Yanzu kuma Gwaggo ai ba zata iya komai ba, daman can rashin kula da addu'a ne da kuma tsarin jini, amman yanzu babu wannan sakakacen duk abun da zata yi kanta zai koma, wannan sakin da aka mata ma kar ki yi mamaki ace wani sharin ne ta dauko ya koma mata, Dan Allah Gwaggo karki hana Alhaji maida matarsa idan ya bukata, ita kanta Iyami da yayanta za su fi samun hankali idan suna guri daya, ba baki nake ba amman da zarar shi kansa maganin ya sake shi ba zai barku ku zauna lafiya ba sai an maida masa da natarsa ai yana kaunarta sosai shiyasa aka raba su, ba zai taba barinta a gidan nan ba Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya. Ni kam da na tsorata sosai, har ina cewa ko da wani auren zata sake yi ba zan bari ta auri ta auri mai mata ba, wai wanda matarsa ta mutu ko kuma ba shi da auren gaba daya, ina ganin kishi kala kala amman na Kaltume ya tsorata ni sosai, mata babu tsoron Allah a ranta Karki ji komai, da yardar Allah karshenta ne ya zo, ni akwai wani Malami ma da na ji yana bada taimako kuma ana dacewa gashi babu wani kashe kudi da za'a gwada na Iyami ko Allah zai saka a dace Shi kuma a ina yake? Lamarin maganin ne yi ake kamar
Chapter 104 · 0% Book details