← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 143

Sashe 94

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gadon Hurriya ya dafe goshinsa. Ana cikin wannan halin na mutuwa me ya kawo magana irin wannan kuma? Daman sai da tace min bata son Hajiya ta yi mata wani kallo na ce ba za'ayi ba Ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya mikawa Hurriya. Kira Amma idan Gwaggo ta daga ki ce mata twins za su kwana a gurinki Ta karbi wayar bayan ya cire mata password ta saka number Amma dake haddace a kanta ta kira, Gwaggo na dagawa suka gaisa ta fadawa Gwaggo kannenta za su kwana a gurinta. Aa ki zo ki kawo su yanzu Gwaggo dan Allah, haba Gwaggo ba su tana kwana a nan ba, zan jidadi idan suka kwana za su rage min kewarku Shikenan gobe amman su dawo gida, kuma ki kula da su Toh Gwaggo na gode sai da safe Ta kashe wayar ta mika masa, ya karba ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi kofar dakin ya bude, ita ma ta sauko daga kan gadon ta bi bayansa tana jin farinciki kanenta za su kwana a tare da ita. Ko da suka sauko falon babu kowa sai Momy, yan'uwanta da suka zo gaisuwa sun tafi tun dazun. Hamid Momy na ke yi ma fada wai yana ta yi mata kiriniya a kitchen ya ki ya natsu. Yasir ko kallonsu be yi ba ya fice domin ta shi ta isheshi ga rashin yar'uwa ga damuwar abun da ya ji Hajiya Kaltume ta yi ma Rukayya, ga fadan da Rukkayya ta rubuto masa ana yi mata a gidansu, goma ta hade masa da ashirin. Momy ai dole su yi, saboda ba su saba ba, gidansu ko rabin kyau wannan be yi ba, kuma ba a saba ganin kayan dadi ba, sai bude fridge yake yana rufewa kamar wani tsohon bakauye Cewar Namra dake zaune dinning tana lasa wayarta. Maganar ta soki Hurriya irin tsokar da take jin bata zata iya mata kara ba, domin ita ma bata ti mata ba. Can inda suke zaune ba gidan mahaifinsu ba ne, gidan kakarsu ne, nan din dai shi ne gidan mahaifinsu Hurriya ya rufe na rufe baki, Momy ta matsa ta wanke mata fuska da mari. Dan Ubanki Namra ba yayarki ba ce kike fada mata magana any how? Hurriya ta dafe kuncinta ta fashe da kuka. Amman Momy baki ji me take fada ba? Gidan uwata take kushewa Karya ta fada? Kuna da irin wannan daular a gidan uwar taku ne? Da yara sun saba da jindadi za su zo suna wannan rashin natsuwar ne? Me kuke da shi a gidan uwar taki? Cikin kuka Hurriya ta matsa ta rika hannun kanenta zata ja su zuwa sama sai duk suka bata fuska ganin an daki Hurriya har tana kuka, dayan ya ware hannunsa ya daga sama alamar zai daki Momy saboda ta doki Hurriya, Namra na ganin haka ta bar dinning din ta nufo inda suka ta yi masa dudu a baya. Marar kunyar yaro, Momy zaka daka Dayan ta doka kamin ta dauke hannunsa Hamad ya fashe da kuka ya zageta da hannu, shi ma ta rikoshi zata dunduma masa dudu a baya, Hurriya na ganin hakan ta shiga tsakani ta tare shi, sai fadan ya koma tsakaninta da Namra. Okay hana ni zaki yi na dake shi? Ko baki ga zagina yayi ba? He's just a child, daukar alhaki ne kawai Yaya Namra Okay to bari ke na dauki alhakinki na lura ganin kike kamar ni din nan sa'arki ce ko? Namra ta kama wuyan rigar Hurriya ta shaketa har sai da ta fada baya kan kujera, Hurriya na kokarin kwantar kanta tana kuka saboda karfi ba daya ba Momy kuma na tsaye ta ki ta raba sai zuga Namra take wai idan ba duka ta yi mata ba zata daina raina ta ba. Hamid da Hamad kuma suka hau kuka suna dukan Namra ta bayanta, dayan ya dauko remote din dake Center table ya jefi Namra da shi. Kin ga wadanan berayen babu tarbiya a tare da su sam... ban san me ya saka Yasir ya shigo min da su nan ba A tsakanin rufe bakin Momy da turo kofar falon da Captain yayi ba a iya shaidar wanda ya riga wani ba, shigowa yayi cikin falon ya bayan ya rufe kofar yana kallon Namra da ta danne Hurriya har a ganinta. Me yake faruwa? Captain Momy ta fada, sai Namra ta dago da sauri ta juya ta kalli kofar, hakan ya bawa Hurriya damar silalowa kasa tana tari kamar zata mutu, ba karamin shaka Namra ta yi mata ba, a kokarin ganin ta kece rainin a tsakaninsu ta kusan aikata lahira ba da niya ba. Captain na hango Hurriya ya nufi gurin ya saka hannunsa ya dago kafadunta sai nishi take daker tana tari hawaye na fitowa a idon da bata iya shaidar waye a gabanta saboda babu gilashi a idon nata. Hamid ya dawo gurinsa yana dukansa yana kuka a zatonsa shi ma wani abun zai mata. Captain ya juyo ya kalli Momy. Momy kina kallo ana kokarin yin kisan kai? Hurriyar ce bata jin magana Captain rashin kunya take yi ma Namra kamar ba yayarta ba, saboda yaran nan ta kama Namra da kokawa Ya saketa ya mike tsaye ransa a bace. That's mean wani abun aka yi da ya kufular da yarinyar nan, idan ba haka ba babu yadda za'ayi ta kama Namra da kokawa, yarinyar da ko yatsa aka saka mata a baki ba zata ciza ba, ban san me ya faru ba amman zan iya shaidar ita ke da gaskiya Captain baka san me ya faru ba, be kamata... Tasss ya wanke fuskar Namra da mari tun kamin ta karasa furucinta. Ya nunata da yatsa wani abu na fisgeshi yana kokarin ninka masa bacin ransa. Idan kika sake kai hannunki a jikin yarinyar nan....! Sai kuma yayi shiru be karasa ba sai wani mugun kallo yake watsa mata. Namra ta rike fuska daga ita har Momy mamaki ya hana su sake cewa komai. Ya juya ta nufi gurin da gilashin Hurriya yake ya dauka ya kama hannunta da take lalabe da shi ya danka mata gilashin. Sai ta karba ta saka ta kalleshi. Na gode, na gode da ka zo... Ta furta wasu hawayen na sauko mata, ta san ba dan ya zo in time ba wata kila da yanzu an yi gawa ta biyu a gidan. Me ya faru? A madadin ta yi magana sai kawai ta fashe da kuka, daman haka take ko a can da idan suka yi fada da Hamad bata iya maida magana saboda kuka, Hurriya irin yaran nan ne da idan aka yi fada basa iya bitar abun da ya faru ko da kuwa su suke da gaskiya saboda kuka. Tausayinta sai ya kara kama shi, daman zuciyarsa ta raya masa tana nan bata ci abincin dare ba, wata kila ma har da rana domin ya lura da yanayinta a dazun shiyasa har ya dawo gidan da dare, ashe da rabon ya tararda wannan fadan ne. Namra ta lumshe ido sai a lokacin kuka ya zo mata, Momy ta kama hannunta suka nufi stairs tana kuka, Momy kuma rai bace an taba mata yar gudaliya gashi babu halin ta yi magana saboda Captain ne, ta san idan ta yi magana zai iya cewa saboda ba ita ta haife shi ba shiyasa ta yi magana dan yi mari Namra, wata kila ma yayi fushi, kuma idan abu yayi zurfi ba zai tsaya iya tsakaninsu ba. Hurriya ta mike tsaye ta share hawayenta, ta kama hannun kanenta. Su waye wadanan? Kanena ne Ta amsa tana jansu, shi ma dai ya tambaya ne saboda confirmation amman ya ga kamanin a fuskarsu ai. Hurriya ta haura sama da yaran ta shiga dakinta ta saka Hijab dinta ta sauko tare da su, a lokacin Captain na zaune a sofa yana kallonta har ta sauko tare da su. Ina zaki je? Gida zan kai su Cikin dare? Daman Gwaggo bata so su kwana a nan ba, ni ce na takura su kwana a nan, kuma gashi yanzu saboda su ana yin fitina Je dakinki ki kwanta Ya bata umarni kai tsaye. Daman Amma bata son... Bata karasa ba ya daka mata tsawa. I thought na fada miki bana maimaita magana Ta juya da sauri jikinta na rawa ta nufi stairs, daman tsoronsa take balle yanzu da ya mari Namra a gabanta. Twins na ganin ta nufi stairs suka fashe da kuka suka bi bayanta, Captain ya kallesu. Dawo ki zauna a nan Kamar umarni take jira ta juyo da sauri ta dawo ta zauna sai suka nufeta suna zauna suma kusa da ita suna kuka. Ki rarrashe su mana, ki zubo abinci ku ci Ta mike tsaye ta nufi dinning tana waigensa, daman dai bata isa tace masa Momy ta hana ta taba abinci idan bata ci ba, kar yayi mata fada, babba plate ta dauka ta zuba abincin ta dawo tsakiyar falon, ta koma ga dauko ruwa sannan ta zauna ita da kanenta suka fara cin abincin kamar wasu marayu. Hamid sai kallon Captain yake abun da Hurriya ta kasa yi gaba daya tsoronsa ya cika mata zuciya, hantar cikinta sai kadawa take. Wuta.... Little Hamad ya fada yana nuna kitchen din. Gaba dayansu suka dago suka kalli kofar kitchen dake cikin da hayaki, Captain ya mike tsaye da sauri ya nufi kitchen din, hankalin Hurriya ma ya tashi ita ma ta bi bayansa kamin su karasa suka ji ihun Namra, Hurriya ta yi zaton wutar kitchen din ce ta fito da ita daga dakinta har take ihu. Kunamu a dakina sun cijeni akan gadona suka har uku wayyo Allah na.... Sai suka ji wani abun na dabam, sai kuka take tana sosa bayan rigarta kamar zata fita daga hayyacin, har wani tsalle take tana saukowa kai kace ma fadowa zata yi a stairs din. Captain ya kalli Twins din dake ta cin abincinsu, dayan yana kallon Captain dayan kuma yana kallon Namra dake mirgina a stairs tana kiran Momy. Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama
Chapter 94 · 0% Book details