← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 143

Sashe 19

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai kitchen da haraba, har yaushe mai aiki ta yi matsayin shigo min bedroom? Kina gani ai idan kika je gidana, su Larai ke kula min da daki Toh ni wa zan saka? Ke ai kina rikon su Larai da Aliya Wannan yar mijin na ki da kika fada min ta dawo nan hutu ta zo yi? Idan ma baki sonta sai ki duba a cikin dangi ki dauko wadda zata iya kula miki da daki, amman ba dai masu aiki ba Zan duba a dangi, yar miji ina sakata za ace bana kaunarta Hajiya Turai ta yi murmushi mai sauti tana mamakin sakarcin Momy domin a gurinta abun da Momy take fada ko take gi sakarci ne. Ke ma dai ban da abun ki Hajiya Nafisa waya taba son a ko ar kishiya? Ai ba wani boye boye, ba zan hana ka aure ba amman fa ba zan so matarka da anta ba Ai Wallahi Hajiya Turai ba karamin sa'a kike yi ba, da yayana baya sha'awar aure-aure, ba kamar nawa mijin ba, domin ni ko a yanzu da ya saki Iyami tunani nake ko dai ta dawo ko kuma ya auro wata Shi ne banbancin tashi a gidan arziki da kuma cintar arzikin, da ace mijinki ma kamar tashin Engr ne, da ba zai yi wannan aure-aurenba, ai talauci mugun abu ne, da zarar sun ga sun yi kudi sai su ga babu abun da ya dace da su kamar aure, amman Engr kam ai rayuwarta turawace da shi, babu ruwansa da wannan hange-hange Wallahi ya huta, da alama ma ana halinsa zai gado Hajiya Turai ta tabe tana girgiza kai cike da kasaita. Hmmm Captain? Ai idan ba Allah ya sauya masa hali ba, da wahala ma ya iya zaman da mata, yanzu ma addu'a muke kar ya ce ya fasa auren, shiyasa na ce ban yarda ya zauna ko'ina ba sai a kusa da ni Momy ta kasa dariya. Haba dai Hajiya Turai Hajiya Nafisa kin manta halin an naki? Wannan mugun fushi da bakar zuciyar ta Captain tsoro take ba ni, komai aka yi masa a duniya ba a masa daidai, ko kallonsa kika yi zai iya cewa kallon ya wuce kima ya fara masifa ko ma ya ce hararasa kika yi, yadda kika san shaidan aka nade aka saka masa a zuciya haka, abu kadan sai masifa sai fushi baya iya controlling kansa, ga zafin hannu a family babu wanda be san halinsa ba, ita kanta yarinyar da zai aura yanzu, ba dan tana hakuri da shi ba da yanzu rabu da ita, da inda abun ya zo da sauki ita mai sanyi hali ce kuma tana gudun zuciyarsa Toh ai sai a kiyaye, haka Allah yake son ganin kayansa, Captain murdaden mutum ne iya masa sai Allah Ina ta addu'a dai Allah ya sauke masa wannan mugun fushi da bakar zuciyar, idan ba haka ba zaman auren ba zai jima ba, kuma ya fada min idan yayi wannan auren ba zai sake yi ba har abada, wai ko matarsa mutuwa ta yi ko suka rabu a haka zai zauna har karshen rayuwarsa, ni kuwa ba fatan haka nake ba, ni da nake son na yi ta ganin jikoki a makwafin an da Allah be ba n i ba Gaskiya kam, muma muna son gani ai balle kuma ke da shi kadai kika haifa... Hajiya Turai na taba kayan marmarin suna hira da Momy har time ya fara ja, hakan kuma be saka sun yanke hirar ba har sai da Namra ta shigo turo kofar dakin ta shigo. Momy Hajiya ta iso Momy ta yatsina fuska domin ta san wace Hajiyar ake magana, wato Hajiyar Binta surukarta uwar da ta haifi mijinta. Toh shi ne kuma sai an fada min? Kin san ai ba nan take fara zuwa ba sai ta gama da ko'ina take lekowa nan, to miye damuwata da ita, je ki fadawa masu aiki su kai mata abinci "Okay Ta juya ta fita. Momy ta yi tsargi da fuska. Idan ban je na gaisheta ba, sai ki ga ya shigo yana ta bala'i, alhalin ba so take ba, idan ta zo bata sauka bangaren kowa sai na Iyami, kuma sai ta fara shiga bangaren Kaltume sannan take leko nan ikon Allah haka take ita kuma! Allah kyauta rayuwarku sai ku Hajiya Nafisa Cewar Hajiya Turai da kamar gatse tana jin ita duk ba zata iya daukar wannan ba, domin kowa yana da yancinsa. Namra na fitowa bedroom din Momy ta nufi dakin Hurriya ta tura kofar dakin, Hurriya na ji an taba kofar ta yi saurin juya fuskarsa ta boye kukanta. Hurriya Hajiyarki ta iso, Appa ya aiko Ya Musib ya fadawa Momy Hurriya ta share hawayenta da sauri ta juyo, sai gata ta sauko daga saman gadon bata ko kula Namra ba ta ratsa gefenta ta fice da gudu, duk wata dokar sauka ko hawa stairs na Momy manta su Hurriya ta yi a lokacin saboda zumudin zuwan Kakarta Hajiya Binta a gidan, kamar yau ne zata fara ganinta a gidan haka Hurriya ta ji. Da sauri ta bude kofar fita falon Momy bata kula komai ba ta saka kai zata fice, da mugun karfi ta ji kanta ya daki wani abu mai karfi har sai da ta yi baya kamar zata fadi. Dagowar da zata yi ta duba me ta buga domin be yi mata kama da karfe ko icce ba, ta ji an wanke mata fuska da lafiyayen marin da ya haddasa mata ganin wadansu kananan taurari, gilashin da yake mafaka ne a idonta ya fadi kasa, sai hudu da buji suka mamaye ilahirin idanuwanta. Sai ta tsaya cak irin tsayin da ta saba yi a duk lokacin da wani bakon al'amari ya ziyarceta. Gafen fuskarta ya hau zugi yayi ja, idanuwanta suka masa tantance mutunen da ke tsaye a gabanta, fafadane ta ga hakan a cikin hudun idanuwanta, dogo ne irin tsayin da ta tsaya iyakar kirjinsa. A hankali ta sulale ta kai kasa ta saka hannayenta tana lalaben gilashinta hawaye na kwankwaso mata kofa. Lalabe ta yi ta yi amman ta kasa jin gilashin, kamar yadda ta duka haka ta mike tsaye a hankali ta juya ta lalabi kofar falon ta fara tafiya. Hurriya... Me ya same ki Namra ta tambaya tana nufota da sauri ta kama hannayenta ta rike domin hawaye take kamar an bude kofar fanfo. Ya... Ya... Namra... Gilashi... Na... Namra bata tsaya komai ba ta rika hannunta ta juya da ita suka fita tana janye da hannunta, har lokacin Mutumen da ya mareta yana a gurin tsaye ko yatsansa be motsa ba. Namra ta kalleshi kamin ta sako hannun Hurriya ta fara duba gilashin, can gefe ta hango shi ta nufi gurin da sauri ta dauko mata. Har gefen ido daya ya fashe daga sama, me ya faru Hurriya Ta saka mata gilashin da kanta, lokaci daya ganinta ya dawo fashewar da gilashin yayi ba irin wadda zai hanata gani ba ne, daga sama ne ya fashe shi ma kuma kadan. Hurriya ta daga ido ta kalli mutumen da be mata uzuri ba ya wanke fuskarta mai tsada da mari. Hawaye be daina mata zuba ba, hakan kuma be hana idanuwanta ganin mutumen da kyau, dubansa ta yi ta dube shi, ta sake dubansa sannan ta sauke idonta kasa ta ratsa gefensa ta fara sauka kasa. Slowly ya juya ya kalleta kamar mai son gasgata wani abu ko karyatawa. Bata gani sai da gilashi, me ya faru Yaya? Ya juyo ya kalli Namra a fusace. Aza min bindiga sai na fada miki Jinin jikinta ta sha ta kauce ta ba shi hanya ya shiga ciki, ita kuma ta ja kofar sannan ta bi bayan Hurriya domin gaishe da Hajiya Binta, kamar yadda Appa ya sabarwa kowa a gidan ko baka cikin gidan idan mahaifiyarsa ta zo matukar kana cikin garin sai ka zo ka gaisheta... [10/18, 5:16 PM] Nana 1: Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy Da kallo ya bi Hurriya da Hamad har suka fice sannan ya kalli Hajiya Kaltume ya dauke kai ya nufi stairs. Yana shiga dakinsa abun da ya fara yi shi ne duba gurin da ya aje gilasan Hurriya, amman be ga ko daya ba, a nan ya fara tunanin ko ya canja musu gurin ajiya ya manta, haka ya bi komai na dakin ya duba ba gilasan babu alamarsu, fitowar yayi mamaki duk ya cika fuskarsa ya sauka kasa sai ya samu mahaifiyarsa a gurin da ya barta zaune sai dai wannan karon waya take amsawa, gefenta ya zauna a hannu kujera har sai da ta gama wayar sannan ya tambaye ko ta dauka. Me zan yi da gilasai kuma? Komai dai ni, ubanka ya dora min laifi matan ubanka su adabe ni kai kuma yanzu ka zarge ni da satar gilasan Hurriya saboda ga Kaltume makiyiyarta ko? Maganar Hajiya bata masa dadi ba kuma ya san duk wani kalami da zai dora bayan nata a yanzu ba zai fahimtar da ita. Dan haka ya tashi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi dakin yan'uwa daya bayan daya ya bi yana tambayarsu kowacce tace masa bata dauka ba, Khairi har da hadawa da rantsuwa saboda ta fi kowa rashin tsoron Allah. Toh ko Hurriya ta zo ta dauka ko Hamad ban sani ba? Ya tambayi kansa, sai dai ya san ba su taba masa haka ba, idan tana bukatar abu zata yi masa magana kuma idan ma ta dauka zata fada masa. Fitowa yayi daga bangaresu ya nufi bangaren Momy, kamar ance masa juya ka gani, yana juya ya kalli bangaren Appa sai ya hango Hurriya tsaye tare da Appanta ta rike hannunsa tana ta bata rai da alama makiya take masa kan wani abu. Fasa nufar bangaren Momy yayi sai ya nufi bangaren mahaifinsa domin tambayarta ko ta dauko gilashin be sani ba. Appa dan Allah daga wannan ba zaka sake yi ba Ta fada cike da shagwaba tana kara rike hannunsa. Haramun ne, ba kyau Hurriya ni bana sha'awar irin abubuwan nan Appa ya fada yana kallon Yasir da ya iso gurin fuska a sake. Me take so Appa? Birthday kuma ka sa be da kyau ba al'adar
Chapter 19 · 0% Book details