← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 143

Sashe 71

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660 Hurriya an dawo Far'ar da Hurriya ta gani a fuskar Hajiya Kaltume lokacin da take fadar haka ya fi daga mata hankali fiye da ganinsu da ta yi a gidan. Cikin rashin kuzari da faduwar gaba ta karasa kusa da Hajiya Binta ta zauna a kasa, sannan ta mikawa Appa gaisuwa. Lafiya Kalau Ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Kaltume na murmushi tana kallon Hurriya irin murmushi na murnar ganinta, bayan kuma a kasan zuciyarta ba haka ba ne. Hajiya Ina wuni? Lafiya Kalau mutan aljanna, an dawo? Tun dazun muke nan ai, Hajiya ta ce kin tafi duba Iyami ya jikin nata Tana jin sauki? Sosai? Maa Shaa Allah... Ta kasa cewa Allah ya bata lafiya, saboda hausawa suna cewa addu'ar fatan alheri ta makiyi karbabbiya ce, wai idan yayi maka sai an karba. Hurriya ta juya a hankali ta kalli Hajiya Binta dake zaune fuska ba yabo ba fallasa. Hurriya an dawo? Eh Hajiya sannu da gida Sannu dai yar Albarka, kin yi Sallah? Aa ina tahowa ne aka yi kira To tashi ki shiga ciki ki yi Sallah ki Hajiya Kaltume ta ce Ai da ta bari sai mun tafi sai ta yi sallah a can Babu inda Hurriya zata tafi, ai na fada miki tun da ya koreta ta dawo nan kenan idan kika ga ta bar gidan nan to bana raye ne A take Hajiya Kaltume ta saka kukan munafurci. Haba Hajiya yanzu duk hakurin da muka yi ta baki baki hakura ba, ita dai Hurriya na san bata da matsalar komai kuma ko yanzu zata so komawa gidan ubanta domin babu kamar gidan uba a duniyar nan Nan da take ai daji ne, da bata da alaka da kowa, ke ni kar nake ganinki, halinki babu wanda ban sani ba Kaltume, tun kina da kurciyarki har yanzu da kika yi yaya, saboda na aika muku da shi ne kika taso mijinki gaba kuka ta so wai azo a kalailaye ni da dadin baki a tafi da Hurriya ku karasa kasheta a can ko? Wallahi ba manufata kenan ba, ni taya zan ce na kashe rai balle kuma Hurriya haba Hajiyaba zan iya aikata haka ba, kawai maganar da kika fada mana ne, na lura da haka ya kamata na yi kasancewa uwa, a wacan lokacin idona ya rufe ne ni da Alhaji shiyasa har ya koreta, ni kuma na kasa dakatar da abin amman na bashi hakuri Hajiya, ita kanta da zata fadi gaskiya ta sani Cikin kuka Hajiya Kaltume take maganar da hawaye shabe shabe a fuskarta. Kukanta ya bata ran Appa har yayi sanadin da ya watsawa Hurriya wani kallo daya saka ta sauke idonta kasa da sauri. Hajiya, ki yi hakuri haka ba zai sake faruwa ba Ba fa zata koma ba, daman can ni bana son zamanta a gidan nan, ba za a kula da ita ba yadda ya dace, gashi ba iya magana take ba fa ma Hamad ne shi ne mai iya magana da fadar abun da aka yi har ma ya rama, amman ita ba zata fadi komai ba, ko a lokacin da aka ce taje ta yi gulmarka a wani guri ai be kamata ka yarda ba, domin idan akwai wanda ya san halin Hurriya ciki da waje a duniyar nan kai ne, yadda ta shaku da kai bata shaku da mahaifiyarta haka ba Appa ya sauke kansa kasa har lokacin hakuri yake badawa yana neman yafiyar Hajiya. Ni na yafe maka amman tabbas da baka zo ba kam, ina nan rike da wannan abun a raina kuma ba zai maka dadi ba saboda ni uwa ce, ko ban fada ba idan raina ya bace zaka iya gani a al'amurranka ko a jikinka ma Toh a yafe min Hajiya hakan ba zai sake faruwa ba, kuma dan Allah ki bar mu mu tafi da Hurriya Ba za a tafi da Hurriya ba, idan ka ga ta bar gidan nan to a dayan biyu ko dai ta yi aure ko kuma na mutu Hajiya ta sake fashewa da kuka, ita kanta Hurriya ta tsorata da yadda Hajiya take son komawarta a gidan har da hawayenta. Cikin kukan Hajiya Kaltume ta kalli Hurriya data kasa tashi a gurin da take zaune ta ce. Subhanallahi, ki yi hakuri dan Allah, kuma ki sak baki Hajiya ta hakura ita ma, wannan maida magana baya da ake ba shi da dadi, takas mahaifinki ya zo saboda ya tafi da ke, dan Allah ki yi hakuri Hurriya Hajiya Binta ta yamutse baki. Hurriya bata da ikon kanta, ikonta yana gurin mahaifinta da mahaifiyarta sai kuma ni, dan haka ki daina saka Hurriya a cikin maganar nan Hajiya na fadar haka Appa yayi karaf ya kalli Hurriya ya ce. To idan haka ne, Hurriya ina baki umarni a matsayina na mahaifinki ki koma gida cikin yan'uwanki, idan ba haka ba zaki yi mamakin abun da zai biyo baya... Appa na gama fadar hakan ya kalli Hajiya Kaltume ya ce. Tashi mu tafi Sannan ya mike tsaye, Hurriya ma ta mike tsaye da sauri, cikin karfin hali na tsufa Hajiya Binta ma ta mike tsaye ta rike hannun Hurriya. Hurriya ba zata koma ba, gaba daya ka canja tsoho ta ya zan yi umarni kuma ka yi kokarin karya wannan umarni? Anya kana cikin hayyacin Tsoho?'' Ya kada kansa kasa. Hajiya ba umarninki nake kokarin karyawa ba, bana son zaman Hurriya a ko'ina sai a gida, sanin kanki ne tun kamin yau kin ce na baki ita ban baki ba, saboda bana son kowa ya rika min da Hajiya Binta ta masa wani kallo na tsanaki, shi kuma ya ki yarda ya daga kansa ya kalleta sai yawo yake da idon a kasa. Tun tashinsa har girmansa bata ba shi umarni ya tsaba sai a yanzu, ba kuma yanzu ta yau ba, yanzu da girma ya cin masa ita kuma take gangarawa. Ko a lokacin da ya saki Iyami babu yadda bata so ya dawo da ita ba yaki, yanzu kuma saboda Hajiya Kaltume ta sako shi a gaba ya zo a maida Hurriya yake wannan bubutan. Kai ma haihuwarka aka yi, kamar yadda ka haifi Hurriya idan baka yi hankali ba, kai ma sai na baka umarnin da idan ka saba ba zaka ga da kyau ba Hajiya Kaltume ta kama gafen mayafinta tana share hawaye tare da mikewa tsaye domin ta lura ran Appa ya bace kamar yadda na Hajiya Binta ma ya bace har ta fusata. Ba za'ayi haka ba, ba ta kai ga haka ba, Alhaji mu tafi, tun da Hajiya na zon zaman Hurriya a nan ka barta ta zauna Allah ya bada hakurin zama Appa ya kalli Hurriya sai da hantar cikinta ta kada ta fara kokarin zare hannun Hajiya Binta a hannunta, ba kuma dan komai ba sai dan saboda Hajiya Kaltume, sannan ya dan risina ya ce. A tashi lafiya Hajiya Hajiya bata amsa masa ba bata ce masa komai ba har ya fice, kana ita ma Kaltume ta yi ma Hajiya sai da safe ka roki gafararta sannan ta fice. Sai a lokacin Hajiya Binta ta zauna ranta a jagule. Hajiya dan Allah ki yi hakuri ki bar na tafi, kar na kawo rudani tsakaninki da Appa, ko kuma Appa yayi fushi da ni kamar yadda ya fada Hajiya bata kula hawayen Hurriya dake saukowa ba ta daka mata tsawa. Ke rufe min baki nemi guri ki zauna babu inda zaki je, gaba daya sun canja masa kwakwalwarsa, idan yace ya yafe ke ni ma sai na yafe ki, idan takamar yana da kudi yana kula da ni, ai ai ba haka ya tashi yana ciyar da ni ba, Allah ke min komai Hurriya ta duka tana kallon Hajiya bi ta data koma ta zauna. Idan kika samu tsabani da Appa saboda ni, zai kara wutar kiyayyata a zuciyarsa ne, kuma zai tsine min domin baya a cikin hayyacinsa a yanzu, da ba ke ma ba zai tsaba umarninki ba, idan kika yi fushi da shi ba zai ga da kyau ba, idan kuma hakan ta faru da shi, ke da mu abun zai shafa, domin ke uwarsa ce babu yadda zaki da danki sai hakuri, mu kuma yayansa har kasa ta hade bamu da wanda ya fi shi, amman matansa za su iya gina kansu har su manta da shi, wuya bata kisa Hajiya, kuma duk yadda suke nufina da sheri Allah zai kareni, ina jin tsoron fushin iyayena akaina, yardar Allah tana tare da yardar iyaye, mahaifiyata bata da lafiya kuma bana kusa da ita, ki fahimta Hajiya su suke su raba ni da Appa, dan Allah karki bari haka ta faru, ki yafe mishi ki sauko daga fushin
Chapter 71 · 0% Book details