Sashe 14
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsorata ba yi zaton akwai mai kallonta ba. Da sauri ta cire gilashin idonta ta share hawayenta da hannu biyu ta mike tsaye. Ya Yasir yaushe ka shigo? Tun dazu abun karyawa muke hadawa da Hamad Ta fara takawa ta nufi kofar kitchen din da yake tsaye. Kuka kika kwana kika yi jiya ko? Idonki har ya kumbura, kuma kin san matsalar idonki why zaki jawa kanki wata matsalar Yaya idan na tuna Amma bata nan sai na ji babu dadi, kukan zo min yake Addu'a zaki yi, kuma ki daina damuwa Amma zata dawo da yardar Allah Haka Appa yace maka? Ta tambaya tana kallonsa wasu hawayen na sauko mata zuciyarta kuma cike da daukin ya amsa mata da eh zai haka yace. Aa haka dai nake sashe, kuma ni na san haka zai faru ko dan ku, baki ga yadda hankalinsa ya tashi ba jiya saboda fada miki da Khairi ta yi, karki so ganin fuskarta yau sai da na kumbura mata baki Hamad dake can cikin kitchen yana juya plantain yayi murmushin jindadi jin cewar an kumburawa Khairi fuska. Hurriya kuma zuciyarta ta cika da tausayinsa. Da baka doke ta ba Yaya ai gaskiya ta fada min Ba haka ya kamata ta yi ba, kuma be kamata daga ke har ita ace kuna shiga maganar manya ba, dan haka ke ma ki kiyeye kar na cire miki ido Ta yi dariya tare da maida gilashinta bayan ta share hawayenta. Saboda ya dauke musu kewar Amma ya zo part din ya fara hada musu abun karyawa yana cikin hadin ne Hamad ya shigo sai ya kira shi suka cigaba da yi tare, bayan sun gama suka hadu a dinning har Hurriya suka soma karyawa tea kawai Hamad ya sha sai yankan bread daya ya ce ya koshi, Yasir ya kalleshi sai dai be ce masa komai ba domin ya fi kowa sanin ba a cilasta Hamad yin abun da be tashi yi ba a kwashe lafiya, zai iya cilasta masa kuma ya ci amman kuma za su yi fada su rabu da bacin rai. Jiya ma haka yayi be ci abinci ba Hurriya ta fada tana tauna bread din dake bakinta. Ya saka tunanin abun da ya faru ne a ransa, kina ganinsa kamar be damu ba ko? Ya fiki damuwa daman mu maza haka muke muna boye abu a ran mu babu mai sanin muna da damuwa sai idan an bincika ko kuma an saka mana ido Hurriya ta dan yi murmushi kadan. Amman mazan ba kowa yake da zuciya kamar Hamad ba, ya cika fushi Akwai su, wasu sunada fushi sosai a mata ma ana samu balle kuma maza, baki dai taba haduwa da su ba ne, ai halitta ce za a iya samunta a gurin mace haka ma gurin namiji, shi ma Hamad zai daina idan ya kara girma yayi wayo Bata sake cewa komai ba har ta gama karyawa sannan ta tashi da sauri ta nufi upstairs. Bari na yi wanka na saka uniform To sai ki yi sauri domin kusa latti Ya mike tsaye ya fice daga bangaren zuwa bangaren mahaifinsa domin gaishe, kamin ya isa bangaren mahaifinsa ya hango shi tsaye waya a hannunsa yana dannawa, hakan ya saka Yasir ya cira kafa ya karasa gurin mahaifinsa sai yaja ya tsaya yana sauraren wayar da Appa yake. Kamar da karfe goma dai, amman ina son a kwashe komai kamin yara su dawo daga makaranta Yasir ya dan kalleshi zuciyarsa na raya masa kayan Amma za a kwashe. Ashe kuwa ya canka daidai domin a karshen zancen sai Appa ya karasa da fadin Zan turo address din da kuma number wayarta ko da ba ku gane gurin ba Ya sauke wayar ya shiga message dinsa ya fara rubutu location din. Yasir ya mika gaisuwa cikin girmamawa kamar yadda ya saba. Lafiya kalau an tashi lafiya Lafiya kalau Appa Daga haka Appa be sake cewa komai ba shi ma kuma be ce ba, daman baya tunanin Appa yayi maganar Amma ko wani abun da ya shafe ta da shi idan dai ba umarni zai ba shi akan wani abun ba, shi kuma be isa ya daga kai ya kalli mahaifinsa yayi masa magana akan lamarin aurensa ko wani abun da ya shafi matansa ba. Hurriya sun tashi kuwa Appa ya tambaya, domin tun tashinsa zuciyarsa take son zuwa duba yaransa sai dai gudun kar ace ga nuna banbanci ko kuma su ya fi kaunarsu da sauran yara ya saka ya danne ya boye abun. Sun tashi tare muka karya ma, amman Hamad be ci wani abun kirki ba? Ba shi da lafiya ne? Lafiyarsa kalau Hurriya tace jiya ma be ci komai ba Appa ya sauke ajiyar zuciya a hankali ba tare da ya bari sautin saukar numfashin ya fito ba. Har lokacin kuma be kalli Yasir dake tsaye gefensa ba kamar mai jin kunyarsa. Suna tsaye gurin har yara suka fara zuwa karbar chocolate da juice din da ya saba raba musu idan za su tafi makaranta, Appa ya koma ciki sai Yasir ya bishi ya riko masa suka fito da kayan waje sannan ya zauna a one of kujerarun dake gurin, ya fara raba musu suna karba yaran Hajiya Kaltume ne a gaba, Khairi kam baki ya kumbura gashi ta turo shi gaba ita ala dole an mata ba daidai ba fushi take, sannan Namra ta zo ta karba, a da can Hurriya da zumudi da far'a take zuwa karba kuma a kullum Hamad sai ya rigata karba, domin shi baya bata lokaci a komai ba kamar ita ba sarkin latti, cin abinci ma sai kowa ya cinye ita bata cinye nata ba. Appa ina kwana Lafiya kalau Hurriya an tashi lafiya? Alhamdulillah Ta mika hannu biyu zata karba, Yasir ya rigata ya karbe yana dariya kamar yadda ya saba, kasancewar bata a cikin yanayin farinciki sai kawai ta yi murmushi ta hade hannayenta. Appa ya dauko wani ya mika mata. Karbi, ina Hamad? Ta saka hannu biyu ta karba taba ba shi amsa. Yana bus ya ce shi ba zai karba ba yau Appa ya ji babu dadi sai dai be nuna ba kuma be sake cewa komai ba, Hurriya har ta juya sai kuma ta juyo ta kalli Appa. Appa yaushe Amma zata dawo? Kallonta kawai mahaifinta yake, kamar yace me yasa kika min wannan tambayar domin be gama saka kalar amsar da zai ba su ita da Hamad, musamman ma ita da take da shakuwa da shi sosai wata kila Hamad zai bar abun a zuciyarsa dai dai yayi ta fushi da shi. Yasir ne yayi hanzarin tarewa Appa numfashin da ya rasa ina sauke shi. Hurriyya idan zaki yi magana mai tsada da Appa, daga ke sai shi ya kamata ku yi, ki daina yi a gaban mutane kin ji Ta amsa masa da kai, sannan ta kalli Appa Na gode Appa Allah ya saka da alheri Ta juya ta fara tafiya zuciyarta babu dadi. Godiya ce ta yi masa irin wadda ta saba masa a duk lokacin da ya bata chocolate din ko kuma yayi mata kyauta kasancewar abun da Amma ta koya musu kenan, amman a yau sai ya ji godiyarta a wata sigar ta dabam, yake jin kamar abun da ya aikatawa mahaifiyarsu ne take masa godiya a kai, gashi dan murmushi da far'a da kuzarin da yake gani a fuskar yarsa yau ya kau, dan'uwanta kuma ko ganinsa be yi ba. Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Shi ne abun da ya iya furtawa yana binta da kallo zuciyarsa na masa zafi, tunanin dama da hadu na kokarin hade masa su rikita masa kwakwalwa. Yasir ya kalleshi sai dai be ce komai ba. Idan sun dawo makaranta kai ko daya daga cikin direbobin gidan nan wani ya kai su gida su duba Amma Toh Appa In Shaa Allah Appa ya juya ya koma ciki, Yasir na binsa da kallo kansa a daure yana mamaki wane kalar laifi Amma ta yi masa da har ya yanke wannan tsatsauran hukunci haka. *** *** *** Ruma ta turo kofar dakin ta tsaya daga jikin kofar ta kalli Khairi dake zaune gaban madubi tana shafawa bakinta magani ta ce Khairi wai Ina Hajiya tace miki zata tafi? Ba ni ta fadawa ba, Maama ta ce gidan Hajiya Fatee zata tafi Toh amman har yanzu zata dawo ba? Na kira wayarta be shiga Maybe can zata wuni, ai dole dai idan dare yayi kin san zata dawo Khairi karfe 6:30pm ake magana fa, kuma ta fita tun safe Aa Ruma kin cika matsala, Hajiya ai ba yarinyar ba ce idan lokacin dawowa yayi ai ita zata dawo, kika san abun da ya saka ta dade? Kin san dai Hajiya Fatee aminiyar Hajiyarmu ce, waya san me taje yi a gidan Khairi ta amsa mata da kamar fada domin ta hana ta shafa maganin da take cikin salama sai damunta take da tambayoyi. Ruma ta tabe baki ta fito taja mata kofar tana sake gwada line Hajiya domin ita idan Hajiya bata a gidan duk jinsa take ya zama dabam wannan ya saka wani lokacin ma har bin Hajiya take idan zata fita, kusan duk kawayen Hajiya sun san yar autar Hajiya Ruma saboda yawan lake mata da take. Har ta isa dakinta gwada line take amman kiran yaki shiga baturiyar sai tabbatar mata take da ba a samun Hajiya. [10/18, 5:35 PM] Nana 1: Suna shigowa cikin gidan Gwaggo Hurriya ta shiga dakin da sauri tana neman Amma. Gwaggo ta yi dariya tana daurawa jikarta dankwali Maraba da Hurriya yanzu ake tafe Eh Gwaggo ina wuni Lafiya kalau ina Hamad? Shiga nan shigowa, Gwaggo Ina Amma? Tana dayan dakin dake kusa da na su Rukayya Da sauri Hurriya ta tashi ta fice daga dakin Kakarta zuwa dakin da Amma take, tana shiga dakin ta fada jikin Amma kamar bata san tana dauke da cikin kanensu ba, sai kuka ya biyo baya ta kankame Amma sosai kamar za a kwace nata ita. Cikin karfe hali da dauriya irin na uwar da bata son raunin yayanta ya kamata har ta yi kuka a gabansu ta shafa bayan Hurriya tana dariyar da sautinta yaki fitowa, hakan kuma ba karamin taimakawa idonta yayi ba gurin zubar