← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 143

Sashe 26

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki kira Salame yanzu Hajiya Kaltume ta mike tsaye tabur tabur ta fice daga dakin, Hajiya Fatee kuma ta shiga kiran Salame da wayarta. Ina yake? Hajiya Kaltume ta tambayi one of masu yi ma Hajiya Fatee aiki da ta zo sanar da Hajiya. Yana can gate Muje na ganshi Mai aikin ta wuce gaba Hajiya ta sauko tana bin bayanta har suka fita falon suka isa gate ta tambayi mai gadin ina yake. Yana waje Hajiya kullum sai ya zo kuma ita Hajiya ta ce kar a barshi ya shigo Ya bude mata karamar kofar gate din ta leka waje ta ganshi zaune daf da gate din, a take gabanta ya yanke ya fadi domin ya tuna mata da lokacin da suke cikin daji hannun yan ta'adda, ga fuskarsa duk tambo alamar ya sha sara har ya gaji, bakinsa baki kirin ido kamar an daka tarugu tsabar ja, jiki a murda kamar gashin kansa, kana ganinsa ka ga rikakken dan ta'adda. Kai ne kake neman Hajiya Fatee? Hajiya Kaltume ta tambaya cikin karfi hali domin zuciyarta har wani zillo take. Ni ne Allah ya taimakeki, Hajiya Wallahi ina cikin matsala ne, su kuma wadan nan watsatsin masu aikin kullum na zo sai su hana ni shiga, ba dan ina ganin mutumcin Hajiya Fatee ba da yanzu na farka cikin mai gadin nan Wallahi, sai dai Hajiya tana da kima a idona kamar uwa take a gurina ba zan iya haka ba Magana yake da irin muryar mazan nan da shaye shaye ya gama canja kalar muryarsu ta koma mai ban tsoro. Hajiya Kaltume ta yi murmushin karfin hali. Ka kyauta haka ake so ai, ya sunan ka? Sunana Isiyaku, amman dai wasu kan ce min Danja yan sunanayen nan dai na zamani Hajiya Toh Amman me kake so gurin Hajiya? A take ya fara kuka kamar wani yaro ko wawa kukan da babu hawaye sai zallar iskanci. Hajiya Gyatuma aka kwatar a asibiti, kuma ba ni da ko sisin na magani, ita Hajiya Fatee ta sani ba na wani aiki bana sana'ar komai tun da na bar gidan nan ban sake samun wani aikin ba, ina cikin matsala bana da gata sai Allah sai Hajiya Fatee so nake ta taimaka min da kudin magani, kar gyatuma ta mutu Wallahi Allah akwai matsala idan ta mutu ba a taimaka min ba, duk mai hannu a ciki sai na ci uwatar... Yana fada yana hada hannu biyu ya buga, Hajiya Kaltume ta dan ja baya sannan ta kalli mai aikin ta ce. Zaki iya tafiya Sai da mai aikin ta yi nisa sannan ta taka kafarta ta fito daga cikin gidan ta taka nesa da gate din yadda mai gadin ba zai ji abun da zata fada ba. Sannan ta tsaya ta kalli Danja ta ce. Nawa ne kudin maganin? Toh Hajiya dubu talatin ne, amman dai ko dubu biyu ko biyar aka taimaka min da su duk taimako ne Kana da account Akwai account Hajiya amman bana da shi aka Wallahi, kwanyar ce mun sha miyar kuka, daddawa duk ta kwashe basirar, tuwon dawa ma haka ake baza mana shi a ture, kai mun ci wuya Wallahi ga talaucin nan har yanzu be bar mu ba Hajiya Kaltume ta yi dariya har lokacin tsoro be fice ta ba, domin muryarsa ma abar tsoro ce balle kuma ka kalleshi. Kana da waya? Ya dan sosa kansa ya shafa aljihu. Wayar ce Hajiya ko an siya idan ka ji eh ya ne tana damun cikinka dole mu siyar mu siye abinci, line ma dari da hansi na siyar da shi shekaranjiya Toh yanzu idan ina son magana da kai za mu yi kenan? Ki fada min gidanki kawai zan zo na sameki har dakinki Aa ni da Hajiya Fatee duk ba mu gama warkewa daga damuwar da muka shiga ba, baka san yan ta'adda suka kama mu ba? Kai na ji Hajiya, zuwana talatin gidan nan sai ace min bata nan, wai wasu ne suka kamata, da an fada min ba za a biya sisi ba zan karbota ni sai a ba ni kudin, akwai mutanenmu fa masu harkar kuma ni Wallahi jan wuya ne, bana inda bana iya shiga, karfe be fasa ni bundiga bata kama ni sai dai ayi min tambo, danjar nan da kika ji ance Hajiya ni fa danja ne, uban fitina kuma bana tsoron kowa Kai zaka iya aikata komai kenan Danja? Zan iya komai Hajiya mun zubar da hannaye mun cire kafa, rai ma mun wulgar da shi barzahu, Allah dai ya shirya mu kawai Shiyasa Hajiya take tsoron ka, ni ma ina gudun na janyo ka jiki na jawa kaina matsala Kai... Kuturi Ya rike baki. Wai Hajja Fatee tsorona take? Ita din ai uwa ce ba za a mata komai ba, wani ma be isa ya mata ba balle kuma ni, ba dan ita ba da yanzu na barar da hanjin masu aikin nan nata, alkur'ane da yanzu ka ga hanta ya lilo shushushushushuuuuuuu Ya nuna yadda hantar zata rika raea idan ya sareta. Toh yanzu dai zan shiga gida, zan aiko mai aiki da number wayata idan ka samu waya sai ka kira ni mu yi magana, amman dan Allah ka daina damun Hajiya Fatee da yawan zuwa An gama amman Hajiya yanzu akwai wani abu nan? Ina fatar ke ma kina da yan abubuwa yan timatinmai eh... Eh.. Kin dai gane Zan aiko mai number tare da kudin da zaka hau babur ka koma Tana fadin haka ta yi gaba tana nufi gate zata koma ciki, shi kuma ya bita da kirari yana daga mata hannu. Chau chau chau chachachau lafiya lau ne Hajiya, Allah dai ya kara miki kwanciyar hankali ya kara miki iba kai kana ganin Hajiyar nan ka san akwai manyan kaya, Allah ya kara sutura Cikin gidan Hajiya Kaltume ta koma ta shiga dakin Hajiya Fatee ta samu biro ta mikawa Hajiya Fatee domin ita bata iya rubutun ba. Rubuta masa number ta a nan Numberki kuma? Me ya faru? Karki jawa kanki matsala fa irin wadannan ba su jin magana Ke dai rubuta babu komai, ke na ke yi ma jihadin ai, wayo yake masa Hajiya Fatee ta karba ta rubuta mata number ta mika mata. Hajiya Kaltume ta bude jakarta ta dauko 3k ta hade ta takardar ta fita falo ta bawa mai aikin ta umarce ta da ta kai masa. Sannan ta juyo ta dawo dakin tana tambayar Hajiya Fatee ya aka karkare da Salame. Na kirata na mata bayani, ta ce ai ya canja line saboda rufe masa wacan da masu gidan line suka yi, amman yanzu zata turo min sabuwa numbersa kuma zata kira ta masa bayani Haka nake son ji, to yanzu ki kwnatar da hankali ki kira ki fada masa ya shirya komai na sa ya zo garin nan zamu aika da mota a dauko shi a kawo mana har gida, daga nan sai mu gabatar masa da matsakarmu Amman kina ganin zai yarda ya zo? Hajiya Fatee miye kudi ba zai yi ba? Muradi dai abashi kudi shi kuma ya biya mana bukata kawai Ni dai Allah yasa cikin nan ya tausu, idan ba haka na zan shiga uku ga shegiyar suruka zata ji dadi Komai zai wuce Hajiya Fatee ki kwanatar da hankali Cewar Hajiya Kaltume ga aminiyarta tana murmushi. IYAMI POV. . Iyami ba a zama haka, ke kanki kin san mijinki yana sonki, ga yaya yanzu kuma ga cikin nan da kika shiga watan haihuwa, kamata yayi ki nemi taimako idan ma wani asirin aka yi masa aka rabaku a karya shi, ki koma dakinki bana son ki haihu a gida Wallahi Amma ta yunkura da katon cikinta ta tashi zaune daker tana kallon Hindu dake maganar. Hindu, Wallahi ban taba yi ba, su kansu da suke ganin kamar asiri na yi ma Alhaji yake ta so na ko na malleke shi, ban taba bada naira biyar na ce a mallake min Alhaji ba, tsantsar biyayya ne kawai da kawar da kai da kuma jin maganar duk abun da ya fada, ni yanzu ko zaki dora wuka a wuyana ba zan iya fada miki sunan Malami daya da na sani ba a garin nan, ban taba yi ba, Gwaggo ma bata taba ta yi ba mu ba mu da kowa sai Allah Na sani, to ai tambaya ake kin ga har na tsarin jikinki sai ki sha kuma ki bawa yayanki, domin su ma ba barinsu zata yi ba Ni dai ba zan iya ba, na kai kukana ga Allah shi zai min magana, ko yanzu ai ba yadda suke so suka samu ba, duk wata sai ya aiko min da abinci da kudi saboda cikin nan, yanzu kuma kina ganin yadda aka cika harabar gidan nan da itace saboda na shiga watan haihuwar, na san idan ra'ayinsu za a bi ba zasu so haka ba, yarana kuma idan ya auna lokaci ya kan aiko da su su gan ni na gansu, an rabu ne kawai amman kamar ana tare, idan Allah yayi zan koma sai ki ga na koma kamar yadda ban saka ran auren Alhaji ba Allah yayi kuma aka yi auren Toh Allah yasa haka shi ya fi alheri, amman dai da kin tafi ba a san inda za a dace ba Allah ya hada mu da dacewar Ameen Ta amsa ba dan ta jidadin yadda Iyami ta ki amincewa da zuwan ba. [10/20, 6:26 PM] Nana 1: Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy Salame na turo number Malamin Hajiya Fatee ta kira shi a waya, suka gaisa ta fada masa abubuwan da suka faru ya jajanta mata, ya kara mata da cewar shi ma layinsa aka rufe shiyasa bata ji shi ba. Hajiya Kaltume ya karba suka gaisa sannan ta dora masa da banin abun da ya sami Hajiya Fatee, daga karshe suka yanke ranar da zai shigo garin. Sannan Hajiya Fatee ta iya fita dakinta ta samu ruwan tea ta sha domin bata iya cin komai. Hajiya Katume bata jima a gidan ba Fadeel ya shigo gaishe da mahaifiyar, da zai fita Hajiya Kaltume ta bukaci ya sauke ta gida. *** *** *** Ba kadan ran Momy ya ba
Chapter 26 · 0% Book details