Sashe 103
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigo falonta ta samu masu aikinta na kwashe kayan da suka ajewa Hajiya Turai bata taba ko daya ba. Kar a taba komai aje su a kitchen Kulu ta amsa da sauri. Toh Hajiya Momy ta haura stairs ta shiga dakinta, wayarta ta dauka tana murmushi maganar da Hajiya Turai ta fada mata cewar yace ta samu suruka ya faranta mata rai. Akan haka ne ta gwada kiransa ta ji lafiyarsa a yau domin tun da ya tafi bata kira shi ba, sai dai tana magana da shi ta chat kamar yadda mahaifiyarsa ma tace. Sai da tana kiran sunan sai kiran ya yanke alamar ba za a iya samunsa ba. Wata kila yana gurin da babu network ne Ta furta kana ta bude data ta shiga whatsapp dinta ta duba last chat dinsu two days sai ta aje masa sako tana murmushi. My Son, ya aikin na ku? Hajiya Turai tace min Abuja aka kai ku ashe, amman baka fada min ba, Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya Tana kokarin aje wayar reply dinsa ya shigo bata san yana online ba sai a lokacin. Amin Momy na kusa dawowa jibi nan, Ammy ta zo kenan? Eh kasan idan ta shigo Family House bata barin garin nan sai ta biyo gurina, ta fada min albishir din da aka yi mata muna fatan jin labari mai dadi Ya turo mata emoji din murmushi sannan ya aiko mata da sako. Za ku ji ba da jimawa ba Momy. Hurriya tana lafiya Momy? Hurriya??? Na dauka zaka tambayi Namra ne Ya turo mata murmushi shi dai yana kokarin isar mata da sakon zuciyarsa cikin hikima tun da har ta fada masa Ammynsa ta tsegunta mata wani abu a kansa. Duka daya ne Momy Aa ba daya ba ne, Namra yar 'uwarka ce jininka zaka iya juyata yadda ka ga dama ka tambaye ta ko ka saka ta yin wani abu, amman Hurriya baka da alaka da ita Alakar musulumci ta fi ta jini Momy ta kashe data ta aje wayar da mugun mamaki a fuskarta. Kar dai ace abun da Namra yake hasashe ya tabbata kar dai ace Hurriya yake nufi da yarinyar? Idan ba haka ba me ya kawo zancenta a yanzu. Ta sake daukar wayarta ta bude data ta masa reply. Haka ne, amman ina son ka sani babu wata alaka tsakaninka da Hurriya, ya kamata ka sani matsayinku ba daya ba Wannan karon bayan ya karanta be sake ce mata komai ba har ta gaji ta aje wayar ta mike tsaye fice daga dakinta. Dakin Namra ta shiga sai ta same ta kwance kan gado tana waya. Aje wayar nan ina son magana da ke Namra Namra ta tashi zaune tana kallon Momy da already ta zauna gefen gadonta. Me ya faru Momy? Tafiyar da Hajiya Turai ta yi a yanzu ta fada min wata magana da Captain ya fada mata, na yi zaton da ke yake, sai dai a yanzu da na ke chat da shi sai ya ke tambayata ina Hurriya? Namra ta yi murmushi. Ai na fada miki Momy baki yarda ba Ba wai yarda ne ban yi ba, ina ganin dai kamar Captain ba zai tsaya kula yarinya irin Hurriya ba Saboda me? Ga alama ya bar mana kamin ya tafi? Kuma shi Captain ba irin rayuwarku ce da shi ba, be cika duba arzikin gidansu ba Ba zan bar wannan ba To ya zaki yi Momy? Ba ayi ma Captain dole kuma iyayensa suna son farincikinsa fiye da na su babu wani abin da zamu iya yi Iyayensa sun fi ni kyamar talaka, kuma Hajiya Turai ta san yadda nake da Hurriya dan haka ba zata yarda danta ya aure ta ba, bana ma tunanin auren zai yiyu domin Captain baya iya jure komai, daga yanzu ina son ki yi duk wani abun da zaki dauki hankalinsa ki kwantar masa da hankali ita kuma zan yi maganinta na san yadda zan yi da ita Momy ni fa ba zan cusa kaina a gurin namiji ba, idan har zan yi haka miye amfanin amsa suna na mace? Idan yana ra'ayi shi zai kawo akansa a gareni, ba wai na shige masa na nuna masa so ba? Baki son sa ne? Ko kin manta burin da muke da shi akanku? Yanzu ma sai da mahaifiyarsa ta ce zata fi kowa farinciki idan hakan ta faru tsakaninku, haka kika yi saka har ta yi nasarar raba ki da Salim yanzu kuma haka zaki zuba mata ido ta rabaki da Captain? Karamar yarinya kamar Hurriya? Namra ta sauke ajiyar zuciya. Momy idan yana ra'ayina shi zai kusanto da kansa a gareni kamar yadda yake kusantar da kansa gurin Hurriya Take dai jan hankalinsa, saboda ta fiki wayo da iya kisisina, ki zauna nan kina tunaninki na banza da shirme A fucewa Momy ta mike tsaye ta fice daga dakin, cikin kufula da fusata ta tura kofar dakin Hurriya ta shiga. Ke...! Hurriya ta tashi gaban madubin da take ta juyo ta kalli Momy dake kallonta kamar maciji yayi arba da kyanwa. Daga yau babu ke babu Captain, kar wata magana ta sake shiga tsakaninki da shi, kuma ko kallonsa kika sake yi sai kusa kasheki... Na fada miki Hurriya ta daga kanta da sauri, Momy ta ja kofar dakin ta fice, Hurriya ta dafa zuciyarta domin ba kadan Momy ta tsorata ba. All because of Captain? Ya Allah.... Kamar za su cinye ni ni miye nawa a ciki? Saboda kawai yana kula ni, su basa kaunar wani ya nuna min tausayi Ta koma ta zauna tana busar da iskar bakinta, gaba daya ma sai ta ji gidan ya fita ranta. A karo na biyu ta mike tsaye sai dai banbancin wannan tsayin da na farkon wacan na shigor da Momy ta yi ne a birkice tana mata masifa wannan kuma na neman barin gidan dakin ne. Green hijabi dinta ta dauka ta saka ta saka shoes dinta ta fice daga dakin, ta san ba ta isa ta tambayi Momy permission din fita daga gidan ba daman babu ruwanta da ita ko da zata fita ta dade a waje balle kuma yanzu da take jin haushinta. Haka ma ba zata tunkari Hajiya Kaltume tace mata zata fita ba daman ba bangarenta take ba, kuma duka duka yau ta dawo daga gidan bayan shafi sati daya da ta yi a asibitin. Tana fita harabar gidan na Momy ta isa gate dinta sai yaja ta tsaya tana tunanin ta saci kafa ta tafi gidansu Husna ko kuma dai ta hakura ta koma a gidan da baya mata dadin zama a yanzu? Jingina da ta yi da gate din tana kallon Babban gate din gidan da masu gadi suka bude. Ganin Motar Appa ya kara karya mata guiwa daman shi baya son fitarta tun tana da gata a gurinsa balle kuma bayan da ya saka mata takunkumin zama gida da hana ta zuwa gurin Amma ba tare da dalili ba. A madadin direbansa ya nufi bangarensa sai ta ga akalar motar ta nufo gurin da take tsaye wato bangaren Momy, Hurriya ta bar jikin gate din da sauri ta juyo zata dawo ciki gabanta na faduwa zuciyarta na raya mata Momy ta hada ta Appa ne wata kila saboda Captain shiyasa har ya dawo yanzu kuma ya nufo bangaren yayi mata fada. Sai dai horn din da ta ji anyi ya katse hanzarinta na guduwa ta koma bangaren na Momy, a lokacin da ta juyo sai ta an faka motar daidai gate din Momy, an sake danna horn. Cikin karfin hali da hararon laifinta ta nufo motar ta mahaifinta da be cika hawa ba sai lokaci zuwa lokaci, daman haka yake idan ya hau wannan gobe zai iya hawan wata. Daidai gurin gilashin motarsa dake back seat ta tsaya domin ta san bangaren da mahaifinta yake zama a duk lokacin da direba yake tuka shi. Appa ya sauke gilashin motar ya kalli yarsa. Hurriya na ganki tsaye a nan kamar cikin damuwa, na saka direba na zo kuma sai kika gudu? Na dauka fada zaka min Ta fada a shagwabe tana taba yatsun hannunta. Fada me kika yi? Ta yi shiru tana kallon kasa, sai tausayinta ya kama shi, soyayyar da yake mata irin ta uba da a tana ta dawo masa a hankali. Shigo mota Ta daga kai ta kalleshi sannan ta zagaya ta shiga ta dayan side din, direban yayi baya kadan ya canja akalar motar suka nufi bangaren Appa. Wani abun aka miki ne? Ta kalli Appa tana mai mamakin yadda yake son ya ji damuwarta a yau, abun da aka haka rame aka binne shekaru hudu da suka wuce. Ta girgiza kai To ya na ga duk kin bata rai? Wani abu kike so? Ta sake dubansa neman sanin damuwarta da yake kokarin yi a yanzu ya fi komai faranta mata rai. Ina son na tafi na duba Amma ne! Ta furta abun da ba da shi ta fito bangaren Momy ba, farko fitowarta na neman son tafiya gidansu Husna ne, sai dai kuma bata san kalma da zata fito a bakin Appa ba idan tace masa gidansu kawarta Husna zata ce bayan sun yi baran-baran da mahaifinta saboda munafurcin da aka mata sherin cewar ta kulla. Ki saki ranki, daman takardu na dawo na dauka ki jira ni a mota yanzu idan na fito sai mu sauke ki a can na wuce, amman karki kai dare Ba zan kai dare ba Appa Ta amsa muryarta na karkarwa saboda kokarin danne kukanta da take. Ta manta when last ta shiga mota daya da mahaifinta, ta manta when last mahaifinta ya nuna damuwa da ita, ta manta rabon da magana mai taushi mai dadi ta shiga tsakaninta da mahaifinta. Ta zauna a motar na tsawon lokacin da ya fita ya shiga bangarensa ya dauko abin da zai dauko ya fita ya dawo cikin motar. A lokacin da ya dawo cikin motar sai ta karkarta idonta tana kallon mahaifinta irin kallon da an shafe mata yinsa a rayuwarta. Direba na tuki Appa yana duba takardun da ya dauko ita kuma tana kallonsa idan hawaye suka sauko mata sai ta share cikin hikima ba tare da ya gani ba, lallai