← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 143

Sashe 117

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zata rufe maka ido, ka kasa yin biyaya ga mahaifiyarka Jamal? Akan yarinyar daka hadu da ita da girmanka? Ka bijirewa mahaifiyar fa ta haife ka ta yi wahala da kai? Ko dan saboda kai kadai Allah ya ba ni shiyasa kake min haka? Ta karashe maganar idonta na cika da kwalla. Ya kalleta da fuskar da babu wasa a cikinta. Zan hakura da Hurriya Ammy, matukar hakan shi ne zai faranta ranki, na hakura da ita Ammy, soyayya ta yi kadan ta yi min irin wannan rufin, zan hakura da nawa farinciki Ta share hawayenta tana murmushi ta dafa shi. Allah ya maka albarka, ba zaka gane amfanin abun da na yi maka ba sai nan gaba, yarinyar ba ta dace da kai ba, be kamata ta zo a matsayin surukar mu ba Ya daga mata kai yana murmushi kadan, sannan ya sauka daga kan gadon ya zauna a kasa ya kama kafarta ya rike. Ina rokon alfarmar ki bar ni na karasa aikin da na dauko, na yi ma yarinyar nan alkwarin zan gyara mata komai, shi wannan karki hana ni Ammy Ta kama hannunaa da sauri cikin farinciki. Ba zan hana ka ba, na amince ka taimake ta, matukar ba zaka auro min ita a matsayin mata Na gode Yayi mata godiya ransa babu dadi, domin a iya gaskiyarsa yayi mata alkawarin hakura da Hurriya saboda bata sonta, ba zai zabi farincikinsa sama da na mahaifiyarsa ba, sai dai yayi ma kansa wani alkawari daya zai taimaki Hurriya zai cireta a damuwa kamar yadda ya fada. Daddy yana nema na bari na shiga dakinsa Yana can bangaren mahaifiyarsa, dazun sau biyu Bashir Sarauta na aiko masa da mutane yana neman ka ba shi dansa Be ce komai ba ya dauki wayarsa da keys din Nene dake kan gado ya fice daga dakin, gaba daya sai yanayinsa ya sauya, rashin kuzari da walwala sun tattara a fuskarsa da jikinsa. Kamar wanda aka yi ma mutuwa haka ya shiga bangaren kakarsa dake cike da mutane a falon da yaranta da jikokinta cikin anta har da Daddy dake zaune kusa da ita. Kowa zai iya shaidar Captain baya cikin farinciki domin abun a bayyane yake a fuskarsa balle kuma mahaifinsa da ya fi kowa sonsa. Ina makullin motata? Ashe fitina zaka je ka tayar shi ne ka karbi motata? Nene tana maganar tana kallonsa, sai ya karaso ya mika mata key motar ba tare da yace komai ba, sannan ya nemi gurin ya zauna yana mamakin kansa da ada ne idan aka bata masa rai kadan sai yayi kamar zai tashin kowa balle kuma babban abu kamar wannan, amman a yanzu ya kasa yin komai sai ma sauyin yanayi da ya zo masa. Jamal.... Lafiya? Nene ta tambaya mahaifinsa kuma sai kallonsa yake yana karantar damuwarsa. Captain ya kalli Nene ya kalli kowa dake falon sannan ya mike tsaye Ba komai, Daddy ka ce kana son ganina? Momy Ikilima ta ce. Captain akwai wata matsala ne? Ya girgiza mata kai alamar babu. Daddynsa ya sauke ajiyar zuciya cike da kulawa ya ce Shiga ka jirani a falon Hajiyar Maru Ya amsawa Daddy da kai sannan ya fice daga dakin. Baka tambaye shi ina ya kai yaron mutane ba? Kuma na ga yanayinsa kamar da matsala, Allah yasa ba kashe shi suka yi ba, kasan zuciyar Captain fa idan abun ya motsa baya iya rike kansa Zan yi magana da shi Hajiya zan ji ko minene Daddy ya mike tsaye ya fice daga falon, kowa sai mamakin yadda yanayin Captain ya canja. A falon Hajiyar Maru wato step mother dinsa Daddy ya samu Captain zaune ya soke kai kasa yana jiransa. Karantawa min abun da ya saka ka cikin damuwa? Daddy ya tambaya tun kamin ya zauna. Captain ya dago ya kalli Daddy ya fara magana da mu ryar da ke kara bayyana damuwarsa. Ammy ce.... Ya fada masa abun da ya faru tsakaninsu ya kuma jadda masa cewar ya hakura da Hurriya saboda mahaifiyarsa. Daddy yayi murmushi ya kawar da kai kamin ya juyo ya dauko masa zancen daukar Adam da aka yi, a nan ma Captain be boyewa mahaifinsa komai ba, har video da ya dauka na Adam sai da ya nuna masa. Samarin yanzu hauka tana damunsu, idan yarinya tace bata sonka sai ka koma bibiyar bayanta kuma? Da alama dai ba son gaskiya yake mata ba shiyasa ya koma bibiyar rayuwarta Ni ma haka na ce Captain ya fada babu kuzari babu nishadi da jindadin da ya shigo da shi. Daddy ya ce. Amman Barrister tana da gaskiya, mahaifin yarinyar ba zai kawo matsala ba, ka san wasu iyayen basa son bibiyar irin wannan lamarin An abun haushi ma mahaifinta be san ina son yarinyar ba, be san na dauki wannan matakin ba, na shigar da karar ne a matsayin wanda zai aureta ba tare da tunanin wata matsala zata biyo baya ba, amman yanzu ina tunanin zan yi magana da Barrister na fada mata a canja abun Saboda me? Ammy bata so kuma. Na fada mata na hakura Daddy Hakan yana da kyau, amman ka bari mu yi magana da mahaifinta mu sanar masa halin da ake ciki idan ya aminta sai a sauya labarin daga kai zuwa mahaifinta kai tsaye, a matsayin mahaifinta ya shigar da karar ba kai ba, daman hakan zai fi mutuncin saboda kai ba aurenta ka yi ba, da ace kai mijinta ne kana da full hujja Okay, Daddy amman idan ka tafi please ka lurar da shi wasu abubuwan na rayuwa, na tafi asibitin ban ga yarinyar ba kuma na tafi gurin Momy tace min yarinyar tana gurin mahaifiyarta, ina tunanin korarta yayi gashi bata gani kuma mahaifiyarta bata da lafiya bakinciki sai yayi mata yawa Daddy ya ji tausayin Hurriya ya kama shi. Amman me zai hana a nunawa mahaifinta video nan maybe zai sauko ya yafewa yarsa laifin da bata aikata ba Aa bana son nuna masa shi a yanzu, already case din yana hannun DSS idan aka fitar da video lauyoyin Adam zai su iya cewa an masa cin zafi ne an masa da karfi ya fadi abun da ba ayi ba, kuma na yi ikirarin ban dauke shi ba fitar da video zai rushe wacan ikirarin nawa, and Salim zai iya samun kofar shigar da koke a kaina, bana son ya samu wannan damar, amman idan aka je kotun shi da kansa zai sallamo yarinyar ai kuma dole kowa ya san me suka shirya kuma na saka a bincika mutanen da suka yada hotunan kowa zai fadi inda ya samu ai daga nan gaskiya zata fito So shari'a biyu za'ayi kenan? Yeah... Yarinyar nan mai tsada ce Daddy, su sun shigar da ni saboda na karya ma dansu hannu, mu kuma mun shigar saboda dansu ya ci mutuncin Hurriya, and na yi alkawari kowa sai ya karbi kasonsa sai na kunyata su kamar yadda suka kunyata yarinyar nan Yana fada yana jaddawa jikinsa na rawa yana matse hannunsa. Allah kadai ya san halin da take ciki yanzu, sanadinsu ta rasa idonta gaba daya daman ba lafiya ta wadace ta ba Daddy dai sai kallonsa yake da yanayin. Zan tare da mutane a gobe zan jajanta masa abun da ya faru kuma na fada masa matakin da ka dauka, idan ya ba mu hadin kai shi ke nan idan kuma be aminta ba dole mu yi aje case din Daddy please ba zamu aje case din ba, na mata alkawari ko da ba zan aureta ba be kamata na kasa cika alkwarin da na yi mata ba Daddy be sake cewa komai ba, ya ciro wayarsa dake aljihu yayi yana tabawa. Can ya dago ya kalli Captain yana murmushi. Lawyer na ne ya aiko min sako, wai Bashir Sarauta yace ba a janye case din a gobe, wata kila yana tunanin saboda an kai case din dukan da ka yi masa a kotu ne ya saka ka sake daukeshi Ya zo nan ne? Ya zo nan amman ban yi magana da shi ba na fada masa be kai wannan matsayin ba a yanzu, da kam ina ganin mutuncinsa amman ban da yanzu, kuma na fada masa idan ya sake zargin a na da daukar yaronsa sai na shigar da kara a kansa Captain yayi murmushi da be wadaci fuskarsa ba. Daddy wannan ai shi ake cewa fin karfi Daddy ma yayi murmushi mai sauti irin na masu dollars and pounds. I have to do the needful kamin na bar garin nan, gobe da yamma zan koma Kaduna ban sani ba ko Ammynka zata bi ni ko kuma zata tsaya jinyar anta ne Captain yayi murmushin da ya kusan za a iya cewa ya zame masa dole ne kawai, sannan ya mike tsaye yayi ma mahaifinsa sai da safe ya fice. HAJIYA KALTUME POV. Tun jiya da muka yi waya da ke baki sake kirana ba, abun har ya soma ba ni tsoro, da na shirya zuwa gidanki a yau Hajiya Fatee ta yi murmushi. Ai ni dole na zo na same ki Hajiya Kaltume shiyasa da Fadeel na kira cikin na ce ya zo ya kawo ni gidan nan, amman Hajiya gajin hakuri kika yi ne har kika aikata mata haka? Ina fa wai ni? Wannan ai can ya fito tsakaninta da dan'iskan saurayinta, wata kila matsala suka samu shiyasa ya watsa hotunan, ai ni ya biya ya hutar da ni wannan kadai ya isa ya hana Hurriya aure, domin babu wanda zai daukarwa yayansa uwa irin wannan? Sai dai a samu dan baro can ko masu gyaran talkama a hada su, idan ma ta samu domin babu mai auren makauniya Kuma kika ce ta rantse da kur'ane? Haka Khairy tace, wata kila kuma wani ne acan waje yake taya mu fadan, kuma shi ma yaron nan ta yi masa wulakanci ba, kuma abun da zai baki mamakin idan ba su saba haduwa ba a ina ya samu hotunanta Hajiya Fatee ta kyalkyale da dariya ta bawa Hajiya Kaltume hannu suka tabe. Ai wannan abun yayi dadi Wallahi ana ganin yarinya kamar ta kirki ashe ita ma yar banza ce To kin gani dai gashi Allah ya tona asirinta, ko uwarta ai zaman banza ta so samu
Chapter 117 · 0% Book details