Sashe 142
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na yi auren a karbi rayuwata maybe shi ne last abu da zan yi a rayuwata, wata kila zan tafi ne kawai na bar muku yarinyar nan, ko yanayin aikin da nake ma rayuwata kullum a cikin hatsari take komai zai iya faruwa.... Wane irin magana ne wannan? Ta daka mishi tsawa. Wane zance kake haka? Me yake damunka? Ina ce komai ya wuce ai, me kuma ya sake dawo da zancen mutuwa?, bana son wannan maganar karka sake Ya amsa mata kai yana murmushi. Ba zan sake ba Ammy Ya kwanta a jikinta kamar yadda yake mata a lokacin da suke cikin Kaduna idan yana gida tare da ita, babu ruwansa da girman da yayi kwantawa yake a jikinta yayi ta zuba shagwaba, kamar wani yaro. Kansa ya shafa yana kallonsa ita kam ba zata iya jurar rasa danta ba, zata haka for now domin ta san gaba ba zai dade ba, yadda yake da fushi ma wata kila da kansa zai zo ya fada mata ya saki Hurriya wata rana, domin zuciyarsa ba ko wace mace zata iya zama da shi ba, shi ma ba zai jure wani abun ba. Dan haka zata aje makamanta a gefe ta saka musu ido, gudun kar ta rasa anta kuma ya dauke ta a matsayin makiyiyarsa. Wannan ne abun da ta ayyana a ranta. HAJIYA KALTUME POV. Daga min mana Ruma kafar nan ciwo fa take min amman sai ki rika dora min kanki nan kamar baki tausayina, gashi idan ina tafiya kamar zan yi dingishi haka nake yi, ina tunanin Egypt zan tafi a duba min ita, tun da nan sun gagara gane komai Ruma ta tashi daga kwancen da take a jikin Hajiya Kaltume ta kalli Khairy dake zaune tana gyara akafaitar. Yau ke da kanki kike gyara kafarki? To ya zan yi? Ni tsoron fita nake yanzu, mutane za su fara kallonka saboda video nan da ya fita wata kila ma har a nuna ka ace ita ce Khairy ta fada kamar zata yi kuka. Hajiya Kaltume ta ce. Ke daina damar da kanki, abun ne dai kin riga min yi da kin yi shawara da ni da ba zaki aikata ba, ku yara ne ba ku san bandar kasa ba, sai ku rika gaggawa kuna son aikata abun da zai kaiku ya baro, gashi nan duk kin bi kin rame, kin tsallawa a madadin ita aka yi ma ta shiga damuwa gashi nan ma shirye shiyen aurenta kawai ake yi, ni damuwa ke damuwa abu ya taru yayi mana yawa, ni na rasa ina ma zan saka kaina na ji sanyi Hawaye ya zubo a idon Khairy. Da na san haka abun nan zai zama Wallahi ba zan aikata ba, kuma Wallahi ba ni na yada hotunan ba, ni dai kawai na nasa barazanar zan yada ne, shi ne yayi min shairi yace ni na aikata, gashi ya fadi zancen fyaden nan kowa ya ji, na muzanta Hajiya na ji kunyar duniya Ba ke kadai ba, abun ya shafi kowa ai, da murna nake da Hurriya ce ta janyo sai gashi reshe ya juye da mujiya, ga abokiyar taya ni yakin tana can babu lafiya, ni na rasa ma ina zan kama, abubuwa sun tsaya min cak...! Ina tunanin shiryawa zan yi na tafi gurin Yaya Altine... Bata rufe zancen ba Alhaji Musa ya turo kofar falon ya shigo da sallamar fuska kuma babu annuri. Hajiya ta amsa Khairy ta sauke kai kasa tana jin kunyar hada ido da kanen mahaifin nata, ruma kuma ta gyara zamanta tana masa sannu da zuwa sai ya amsa yana zaunawa. Yauwa... Sannu dai Hajiya barka da gida Hajiya Kaltume dake jin kamar ya zo yayi mata albishir ne na ganin ya daidaita tsakaninta da Appa ta amsa masa tana murmushin karfin hali. Lafiya Kalau Alhaji Musa ya yaran? Alhamdulillahi... Maa Sha Allah... Sai kuma shiru ya biyo baya tun bayan da Hajiya Kaltume ta yi magana ta karshe. Khairy ta daga kai kadan ta kalleshi ta ga ita yake kallo sai gabanta ya fadi, ta mike tsaye zata bar falon ya katse shirunsu ta hanyar dakatar da ita. Zauna Ummulkhar maganar ai duk a kanki ne... Wato Hajiya dazun ni da Yaya mun tafi gidansu Hajiya Iyami, to ni ina daga waje saboda na dan ba su guri ne su gana, sai gashi ya fito yana fada min iyayen yaron nan ne suke son ganinsa.... Daki daki Alhaji Musa ya jera musu abun da ya faru har zuwa karshe. A takaice dai yanzu shi yaron yace baya ciki idan ta samu wani ta yi aurenta Khairy ta fashe da kuka mai karfi daman ta saka ran haka, ganin yadda yaki ya daga wayarta tun daga lokacin da abun ya faru har zuwa yau da aiko musu da mummunan sako, Ruma ma kallon Khairy take cike da tausayinta domin ta san abubuwan za su mata yawa ne. Fasa auren na Khairy da aka yi ba daga hankalin Hajiya Kaltume ya jefata a tunani ba kamar jin cewar Alhaji Musa ya bawa Appa da Amma guri domin su gana sai ta ji kamar an watsa mata garwashi a zuciya. Su gana kamar yaya? Daman ganawa suke a yanzu? Ko da yake ga zahiri tana ganin shirye shiyen auren Hurriya da ake sai dai ta ji labari yadda aka yi ko za'ayi a gurin anta Yasir idan ta shinshini gulma, be bawa Momy ta yi komai ba ita da take karkashinsa a yanzu balle kuma Ita da igiyar aure ta raba, yanzu hankalin Appa ya koma gurin Iyami kenan? Gashi har da zuwa da kanensa ko dai auren zai maida? Tun da yanzu ta samu lafiya kamar yadda anta ya fada mata tun kwanakin baya? Ita kam abubuwa sun ribchabe mata a yanzu komai ya shige mata hudu... Bata gama sakar zuci ba Alhaji Musa ya kira. Hajiya kin fahimce zancen nawa? Sai ta kalleshi kamar wata yar marainiya idonta na cika da hawaye, ta rasa laifin me ta yi abubuwa suka zo mata a haka. Na fahimta Alhaji Musa, to me zan ce kaddarori ne gasu nan sun rufe mu.. Shiyasa aka ce idan zaka gina ramen mugunta ka gina gajere, yanzu gashi garin yi ma yar'uwarki sharri kin kunyata kanki kin kunyatata kin bata sunan gidanku, ina amfanin haka? Hajiya Kaltume ta dafe kanta. Yara ne sai ka rasa gane me ke cin zuciyarsu batsa tsayawa su yi tunani A nan ya samu zaren zancen ya rufe ta nasa fadan yana karanta mata inda yake ganin abubuwan da yake yi ma yaran ba daidai ba ne. Komai dai aka yi uwa ake dorawa laifi, to na ji Allah ya yaye mana Ya tashi ya fice daga falon ba tare da sallama ba. Yanzu ni Hajiya Fatee zata yi wannan cin fuskar, ashe ko mutuwa na yi ita din ba mai rufa asirin yaya ba ne? Har zata kyale Fadeel ya aiko wai ya fasa aurenki? Ita Hurriya ba gata nan makauniya ba amman a haka da siraicinta da komai ta samu dan manya mutane ya aureta? Ruma ta share hawayenta ta ce Hajiya Saboda Hurriya bata aikata ba ne aka yi nata sheri aka ce ta yi, shiyasa Allah yayi mata wannan sakamakon, daman sakamakon masu hakuri mai girma ne, shiyasa yake da kyau mu kiyayi iyakokin Allah domin ba za mu iya jurar radadin ukubar sa ba, gashi yanzu tun ba ayi nisa ba ta fara ganin illar abun da ta aikata Ke dalla can rufe mim baki, tun kamin a haife ki na san wannan! Tashi ki ba ni guri, daman ke da Yasir haka kuke kamar ba ni na haife ku ba Ta lalabo wayarta dake hannun kujera ta shiga kiran Hajiya Fatee.... Fadeel ya gyara mata fillon dake bayanta ta jingina da fillon tana runtse ido, ta cije baki alamar ba karamin ciwo take ji ba. Wayarki ce take ringing a miko miki? Ta daga mishi kai, sai ya tashi ya nufi gurin da wayar take ya dauko ya miko mata. Hajiya ce take kira Hajiya Fatee ta karbi wayar ta duba ta aje domin ba ta da kalaman wanke kanta a gurin aminiyarta a yanzu, ita ma ta kanta take. Wata kila ta kira tayi maganar auren da na ce na yanje ne Shi ne ma, da dai ka yi hakuri Fadeel ka rumgume kaddara kamar yadda mijin Hurriya ya rumguma Hajiya ko na auri yarinyar nan ba zan samu aminci da ita ba, daman can ba sonta nake ba saboda ke na nake son na aureta shi na dan kin matsa, kuma yanzu kowa ya ga abun da ya faru babu wanda zai so ta zama uwar yayansa fa, indai zata iya aikawa yar'uwarta haka ina da sauran mutane ko abokiyar zama? Amma Hurriya kaddara ce ta fada mata, ni Wallahi da wannan din ma be aureta zan iya aurenta yarinyar tana da kirki ai Hajiya Fatee ta sauke ajiyar zuciya ya hade yawu. Yanzu dawowa zaka yi da Afrah kenan? Haka nake tunani Hajiya saboda akwai yara a tsakaninmu, kuma daman bata min komai ba haka nan kawai na turata gida ban san me ya zo kaina ba, yarinyar nan tana min biyayya sosai ke ma kuma tana miki kawai dai kin dauki karan tsana kin dora mata ne Hajiya Tana yi fa, tana min biyayya gwargwadon hali, gashi nan ai na koma da ciwo, daman wanda be gode Rahamar Allah ba zai gode azabarsa... Ta karashe zancen da kuka. Wannan kuma wata jarabawa ce ta Allah Hajiya, wannan ciwon ai ba san minene ba ciki ya fara kumbura kuma kin ce ba ki son aje asibiti, gashi tun da muka dawo ciwon zuciya be barki ba, ga cikin nan naki tsoro yake ba ni, idan na ce zan tafi asibiti kuma ki ce ba haka ba, a nan gida kowa duk wanda ya zo ba hadin kai kike ba su ba kuma basa gane komai Zan tafi ba yanzu ba, Fadeel lokacin da zaka kai ni asibitin zai zo, yanzu na hausa nake son gwadawa ina tunanin aikin jinnu ne, akwai inda Murja zata karbo min magani na fara sha Toh Allah ya sauwake Ya fada tare da damuwa sannan ya tashi ya