Sashe 9
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
domin ta kira ni tana ja min kunne akan yaran nan Ko kadan maganar da Hajiya Kaltume ta yi bata yi ma Appa dadi ba, sai yake jin kamar bata son zaman yaransa a gurinta ne, hakan kuma sai ya kara jefashi a cikin damuwar sakin mahaifiyarsu da yayi gashi nan ya koma nema musu gurin zama domin ba zai iya barinsu a katon part din uwarsu su biyu kawai ba babu mai kula da su. Hurriya yata ina kike son zama? Ya tambaya yana kallon fuskarta, Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume sannan ta kalli mahaifinta ta ce. Gurin Hajiyarka ko Gwaggo Ba zan iya bari ku zauna hannun kowa ba matukar ina raye, na fi sonku a kusa da ni na rika yaran wasu ma ta ina zan bada nawa riko? Idam har ba zan iya bari ku zauna gurin Iyami ba to ba zan iya hakurin ku zauna a gurin kowa ba, je ki kira Hamad Hurriya ta tashi ta fice, Hajiya Kaltume ta bita da kallo Appa kuma ya sauke ajiyar zuciya. Yaran nan sun zamar min kamar wasu marayu, Wallahi yau saboda tunanin abubuwan da suka faru na kasa sukuni Akwai damuwa kam sosai, na da zaka hakura ka dawo da mahaifiyarsu da duk yafi wannan nema musu gurin zama da kake, idan ma wani laifin ta yi maka ka yafe mata dan Allah ko mu da muka kwana biyu aka saki a yanzu ai sai mun ji dabam balle kuma ita da take da sauran kurciyarta Appa be ce komai ba bayan sauke kai da yayi kasa, domin baya jin dawowa da ita mafita ne kamar yadda sakin ma ya kasa zame masa mafita domin ko yanzu jin yake kamar akan aya yake saboda tunaninta domin yana matukar son matarsa ga kuma tunanin makomar yaranta. Hajiya Kaltume ta tsare mijinta da ido ganin ya noce kai kasa sai zuciyarta ta raya mata zai iya dawowa da ita kenan ganin yadda ya zurfafa a tunani ga kuma son yaranta da yake. Sai a lokacin da Hurriya ta dawo dakin tare da Hamad sannan Hajiya Kaltume ta kawar da kai tana kwafa a zuciyarta, Appa kuma ya dago ya kalli Yayansa. Hurriya ta zauna a inda ta zauna dazun Hamad kuma ya tsaya jikin kofa fuskarsa ba yabo ba fallasa. Hamad ka ci abinci? Ya amsawa Appa da kai. A take Alhaji Haruna ya kalli Hajiya Kaltume. Ba a basu abinci ba Kaltume? Tuwo na girka, ka san Hamad ba ya cin ciwo kuma basa cin abinci da ake girkawa masu aiki Idan shi baya ci ita Hurriya bata ci? Haba Kaltume kin san uwar yaran nan bata cikin gidan nan a matsayinki na babba ki kasa kiran yaran nan ki ba su abinci? Ban yi tunanin ba su ci ba, ranka ya dade ayi hakuri ba za a koma ba In Shaa Allahu Hurriya zaki ci tuwo? Hurriya ta daga kai a hankali daman tuwo is one of her favorite saboda abincin Appanta ne ita kuma duk abun da Appanta yake so tana sonshi, kuma yawan girka shi da Amma take ya saka ta saba da cinsa, domin Alhaji Haruna ba shi da wani abinci da ya fi tuwo duk arzikinsa ya fi son agirka masa tuwo a gidansa domin abun da ya saba da shi tun kamin zuwan arzikin. Zan ci tuwo Appa Ya kalli Hamad da ko a yau ko sannu da zuwa be masa ba kuma be gaishe ba, abun da be saba ba domin duk tsaurin kansa yana gaishe da Appa yana masa sannu da zuwa kamar yadda Amma ta koya masa. Kai kuma me kake son ci? Je ka kira Dahiru ko Bello ya kaika Restaurant ka siyo abun da kake so Bana son komai Ya amsa kai tsaye ba tare da ya kalli kowa ba. Appa ya kalleshi da kyau. Hamad zo nan Ya shiga cikin dakin sai ya zauna nesa da Appa kamar wani bakonsa ko wanda be saba da shi ba, bayan kuma a da can ba haka yake masa ba idan yayi nesa da shi to yayi laifi ne, amman idan babu laifi baya zama nesa da mahaifinsa kuma sukan zauna su yi hira da juna ayi wasa da dariya sai dai ba kamar yadda suke yi da Hurriya ba. Me aka yi? Waya taba ka? Babu ba ayi min komai ba Hajiya Kaltume ta tabe baki tana murmushi. Kai ma dai Alhaji, a gidan nan ba zai taba Hamad ya kwana lafiya? Idan ma an fi karfinshi ai kasan yadda yake yi ma mutane ruwan duwatsu ko kuma ya shammaci mutum yayi masa wata etar Hamad ya dago ya kalli Hajiya Kaltume da irin kallon da ya fi kama da harara, daman can shi ne mai taya Amma kishi wani lokacin, Hurriya kam team babu ruwanmu ce. Toh na ga yana ta bata rai ne kuma yace ba zai ci abinci ba? Uhm. Hmm Kawai Hajiya Kaltume ta ce ta cigaba da kallon Appa dake tambayar Hamad ina yake son zama. Ina Hurriya zata zauna? Gurin Momy Appa ya amsa masa. Nima zan zauna a can Toh yayi kyau, amman dai ka saki ranka Hamad ka ji? Kuma ka ci wani abun yaushe rabonka da abinci? Na sha zobo da rana Zobo ai ba abinci ba ne, zaka sha tea da bread a hada maka? Bana son komai Appa bana jin yunwa Shikenan zan yi ma Nafisa magana sai ku maida kayanku part dinta Appa ya fada cikin yanayi na rashin jindadin dansa be saka komai a ciki ba. Hamad ya mike tsaye ya juya. Appa ya bishi da kallo yana fadin. Hamad babu ko sai da safe? Sai da safe Appa Ya fada ba tare da juyo ba har ya fice. Hurriya ta mike tsaye domin yunwa ta matsa mata lamba. Appa ina tuwon? Appa take tambaya sai Hajiya Kaltume ta amsa mata. Je bangarena ki zuba ki ci, mahaifinki ya rima ci balle ku ci tare Ta nufi kofar fita da saurinta. Sai da ta fice Appa ya kalli Hajiya Kaltume ya ce. Dan Allah a rika kula da yaran nan, su da marayu duk daya yanzu Alhaji, dan Allah na ci wannan alfarma dan Allah ko dan yaran nan, mahaifiyarsu ma tunaninsu sai ya isheta kuma kai yanzu baka lura Hamad fushi yake da kai ba? Fushi me? Ka kore mahaifiyarsu mana Ba kin cw bata fada musu ba? Eh amman ka san shi ya yafi yar'uwarsa wayo, ba mamaki ya gane, ita kanta Hurriya idan ta fahimta ba zata jidadi ba Appa ya sauke ajiyar zuciya. Ba zan iya ba ne Kaltume, gobe za a zo da motoci akwaishe mata kayanta Subhanallahi Alhaji har saki nawa ka yi mata ne? Daya Amman za akwashe kaya da wuri haka? Wai me yayi zafi ne shi ba wuta ba? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Ta fashe da kuka ta mike tsaye ta fice daga dakin tana rusar kuka kamar gaske. Appa ya busar da iskar bakinsa shi kansa ya san it's too early ace an kwashe kayan Amma a gidan daga sakinta, sai dai kiran da Bappa yake masa yake son amfani da damar ya nuna musu babu sauran zama tsakaninsada Amma, domin ya kasa amsa wayarsu tun jiya saboda be san abun da zai fada musu ba. Kai ya gigirza sannan ya tashi tsaye ya fice daga part dinsa zuwa part din Hajiya Nafisa wato Momy. HURRIYA POV. Hurriya na shiga bangaren Hajiya Kaltume ta samu Umm Khairi zaune a dinning tana cin nata abincin daren, da a bangaren mahaifiyarta ne sai da ta bude ta zuba amman a nan dole ta tsaya a zuba mata ko kuma a bata izinin zubawa. Yaya Khairi Hajiya ta ce na zuba abinci Gashi nan ai dauki plate ki zuba mai isarki Hurriya ta dauki plate ta bude manya warmers din ta ta dauki mulmular tuwon da aka nade a leda ta raba uku ta zuba daya a plate ta rufe ta bude dayan ta zuba miyar kubewa anye ta saka nama da man shanu sannan ta rufe ta ja kujera har ta zauna ta tuna bata wanke hannu ba ta tashi ta shiga bandakin dake falon ta wanke hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin tuwon, sai da ta yi nisa da cin abincin sannan Khairi ta kalleta. Hurriya Hurriya ta dago a hankali ta kalli yayarta Khairi wadda ta kira sunanta. Na'am? Me Appa yace miki da ya aiko a kira ki? Tambayarmu yayi ina muke son zama Toh ina kika zaba? Ni dai na ce gurin Gwaggo ko Hajiya, amman yace aa sai dai gurin Momy Khairi ta yi fuskar tausayi. Allah sarki, Wallahi na tausaya muku babu dadi rayuwa gidan babu uwa a gida, da ma dai Appa zai yi hakuri da ya dawo da Amma, Hurriya na ga Appa yana jin maganarki why not ki roke shi ya dawo da Amma idan ma wani laifin ta yi masa ya yafe mata Hurriya ta yi mata wani kallo na rashim fahimtar inda zancenta ya dosa. Amman zata dawo idan ta haihu ai Toh Allah yasa ya maida ita, wata kila akwai gyara ai Wallahi duk ban jidadi ba dazun har da kukana Hurriya na jin haka sai kwakwalwarta ta dauka sarai ta gane karatun Khairi a take wani irin tashin hankali ya same ta, idonta dake cikin farin gilashi suka cika da hawaye ta kasa hade lomar tuwon dake bakinta. Slowly ta mike tsaye taja kujera baya ta fara tafiya zuciyarta na buga kamar zata fasa kirjinta ta fito, tana fita falon ta watsa da gudu bangarensu da karfi ta tura kofar falon Amma ta shiga. Hamad na kwance kan kujera yana kallon remote a hannunsa. Hamad wai Appa sakin Amma yayi? Wai rabuwa suka yi? Yaya Khairi ta fada min Tana maganar yana kuka even though bata gama tabbatarwa ba. Hamad ya tashi zaune yana kallonta. Ai ke ce mahaukaciya shiyasa baki gane ba A nan Huriyya ta samu damar fashewa da kuka mai karfi, ta juya da sauri ta nufi bangaren mahaifinta. *** *** *** Ah Ah Alhaji ina ce Kaltume ce Babba a gidan nan? Me zai hana su zauna a bangarenta? Appa ya mike tsaye. A nan nake son