Sashe 132
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku. Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 47 Amma ta kalli Gwaggo mamakin bayyane a fuskarta. Alhaji ne, wai zai aiko da direba a dauki Hurriya ya kaita asibiti ta duba mijinta Gwaggo ma mamakin ne fal a ranta. Ba shi da lafiya ne? Da alama kam, amman Gwaggo ta ya zata tafi duba shi mutunen da be taba zuwa gidan nan ba tun da aka daura musu aure ni ban san shi ba shi ma be san ni ba? Ko dai shi ma baya son auren ne? Ko kuma marar lafiya ne aka aura mata? Shi nake tunani Gwaggo, kar abun yayi ma Hurriya yawa, na ji mahaifinta ma kamar a cikin damuwa Allah dai ya kyauta, wannan abun da daure kai yake Kuma kin ga Kaltume da Nafisa ba za su so Hurriya da alheri ba, za su iya zugawa mahaifinta ya aura mata kowa saboda ta sha wa halar rayuwa Amman a yanzu ina ganin kamar Alhaji ya fara dawowa hayyacinsa ai, Allah dai kadai ya san me yake nan Amma ta fada tana aje kofin maganin dake hannunta sannan ta yunkura ta tashi tsaye cikin rashin kuzari irin na wanda be gama warkewa daga ciwo ba ta taka ta fita daga dakinta. Dakin Rukkayya ta nufa domin a can Hurriya take rayuwa a yanzu, lalulen dakin Amma ta fara yayewa sannan ta shiga dakin, Hurriya na jin yanayin tafiyar ta Amma da bata gama kwarewa ba ta tashi zaune idanuwanta cike da duhu tana kallon saitin kofar. Amma ta zauna kusa da ita tana kallonta. Hurriya ina son ki ba ni aron hankalinki Hurriya ta juya ta gefen da take jin muryar Amma ta mika mata dukan natsuwarta. Ba dan kina yata ba, hakika ke yarinya ce mai hakuri da sanin ya kamata, kuma kin hadu da kalubalen rayuwa da kananan shekaru daman haka tsarin rayuwa yake, wani da dadi wani babu, eani kuma na sirka masa, dan haka ina son ki kara hakuri akan wanda kike da shi kuma ki karbi kaddara a duk yadda ta zo miki, a matsayi na uwa zan yi ina nawa kokarin na ga baki cutu ba a rayuwar gidan aurenki, sai dai kuma idan na hango wata matsala ko wahala da zaki sha zan tare ko da bani da karfi haka zan ta yaki har Allah ya mu nasara Na gode Amma Allah ya miki albarka, Hurriya kin san mutumen da mahaifinki ya aura miki? Kin taba ganinsa ko da sau daya? Ta yi shiru na wasu dakiku kamin ta daga kai. Na san shi Marar lafiya ne? Ko yana da wata nakasa ko aibu? Ba shi da shi ko daya Amma, a lokacin da nake gidan idan Momy ta hanani abinci shi yake kawo min wani abu na ci, ko lokacin da Namra ta shake ni shi ya mareta yana da kirki, amman yana da saurin fushi da zuciya kamar Hamad Amma ta ji sanyi a ranta jin kadan daga hallaya da siffar mijin da yarta ta aura. Zuciyarta kuma sai ta karkata akan furucin Hurriya cewar Namra ra makureta. Me kika yi ma Namra ta makureki? Hurriya ta bata labarin abun da ya faru, Amma ta girgiaza kai, ta sani daman jininta ba zai sha da dadin a gidan Momy ko Hajiya Kaltume ba. Ajiyar zuciya ta sauke Appanki ya kira yanzu, yace direba zai zo ya dauke ki ya kai ki asibiti ki duba mijinki wai ba shi da lafiya, ki shirya Rukkayya zata rakaki Toh Amma Amma ta tashi ta fice daga dakin, Hurriya ta kai hannu tana tana awarwaron da Captain ya saka mata a hannu da sunan wani abokinsa ya bata, tana jin kamar babu dadin jin cewar ba shi da lafiya, ko dai baya son auren ne dole aka masa? Ko kuma wani abu ya faru? Kwantawa ta yi kan tana tunani kala kala a ranta, zuciyarta na raya mata taya mutum kamar Captain zai yarda ya aureta bayan duk abun da ake cewa ta yi? Kuma gashi bata gani a yanzu, wata kila dai dole aka yi masa, amman kuma yadda Momy take jinsa anya zata masa dole? Bayan Namra ta mata gargadi akansa Momy ma ta yi mata. Sai da direban ya shigo sannan Rukayya ta shigo dakin ta saka Hijab dinta ta sakawa Hurriya ta kama hannunta suka fita Amma na Allah ya tsare, Gwaggo kuma na fada mata idan ta shiga ta gaishe da kowa. CAPTAIN POV. Idanuwan da ya rufe ne ya sake budewa sakamakon bude kofar dakin da aka yi, Salim ya sake dawowa hannunsa rike da leda ya nufi gurin da aka tana da ya aje ledar sannan ya kalli Captain. Sannu Allah ya baka lafiya, ga apple nan na san kana son Apple na siyo a waje ne, anjima zan dawo Allah ya kara afuwa Sannan ya kalli Ammy dake zaune. Ammy zan tafi sai anjima zan dawo Allah ya ba shi lafiya Amin Salim an gode Har ya fice Captain be ce masa komai ba. Abun da kake yi wani lokacin baka kyautawa Captain, na san kana da fushi amman danne zuciya ake, ko sai anjima baka cewa yaron nan ba, ba dan kana da aboki kamar Salim ba da yanzu ba ku shirya ba, amman yana mutunkata yana sonka, duk abun da kake masa baya dubawa yana nan tare da kai, duk da yana karkashinka yana baka girma da kulawa na abokantaka ba na aiki ba Nan ma be ce komai ba, Ammy zata sake wata maganar wayarta ta yi ringing sai ta mike tsaye ta fice daga dakin. Captain ya sauke ajiyar zuciya ya ya dan dago kadan, ya sake bude wayarsa ya kunna video ya sake kallo. Ina fatan hakan ya saka ki farinciki Hurriya, and Sister nan da ta aikata miki wannan abun i hope bakincikin da zata shiga zai ninka wanda ta saka ki Ya fita daga whatsapp din ya shiga contact dinsa ya kira Nafi'u. After sun gaisa ya gabatar masa da bukatarsa. Asiri na tuno na abun da ya faru da yarinyar nan so zan turo maka video yanzu ina son ka yadashi iya yadda zaka iya, ya karade ko'ina a kafofin sada zumunta Please Za'ayi haka ranka ya dade ka aiko da video Okay, ba zan baka komai ba a yanzu dai na ga yanayin aikinka, idan ka cancanci da yawa zan baka Zaka gani Sir Ya sauke wayar ya sake komawa Whatsapp dinsa yayi masa sharing din video. Ya sake kiran wani yayi requesting irin abun da ya bukata a gurin Nafi'u shi ma ya tura masa video sannan ya koma ya kwanta. Bayan kamar minti talatin ya ji an bude kofar dakin sai ya sake bude idonsa Rukkaya ta fara daga kai ta kalli sake kallon kofar dakin domin ta tabbatar nan din ne sannan ta kasara turo kofar dakin tana sallama. Sallamu Alaikum Be amsa mata ba domin be san ta ba, be kuma san manufar shigowarta ba har sai da Hurriya ta bayyana a bayanta. Oh My god Ya tashi zaune da sauri farinciki ya cika fuskarsa, hannu ya saka ya kashe ruwan ya cire a hannunsa ya rufe gurin da jinin zai iya biyowa sannan ya mike tsaye ya gyara rigarsa kamar ance masa Hurriya tana ganinsa. A tsakiyar dakin Rukkayya ta ja ta tsaya tana kallonsa. Direban Appan Hurriya ne ya ce mana nan zamu shigo, dan Allah ko kai ne Jamal? Yes... Angon Hurriya Ya fada yana nufar Hurriyar dake bayanta tana rike da hannun Rukaiyah. Hannunsa ya kai ya kama dantsen hannunta ya rikata yana kokarin fitowa da ita bayan Rukayya. Assalamu Alaikum Hurriya ta fada tana jin tsoron da wani yanayi na dabam, domin wani be taba kaiwa a jikinta haka ba a take jikinta ya fara rawa. Murmushi Captain yayi Rukaiya ma ta yi murmushi tana mamakin a yadda ta samu Captain domin dukansu ba su saka ran namiji ne mai kyau da tsari da cikar kalama ne ba irin Captain. Ban san ya kike da Hurriya ba, dan Allah ce ta sake hannunki ko kuma ke ki sake hannunta Ya bukaci haka ne saboda Hurriya ta ki yarda ta saki hannu Mama Rukaiya. Ni kanwar Mahaifiyarta ce Oh Ashe mamanmu ce, sorry ban amsa sallamarki ba, a yafe min Momy Rakayya ta yi murmushi ta saki hannun Hurriya, Captain ya mika hannunsa ya rika hannun da Rukkaya ta saki ya jata har gurin gadonsa ya zaunar da ita. Sannan ya nunawa Rukkayya kujera. Bismillah Ta karasa ta zauna tana masa ya jiki. Alhamdulillah, ko da aka daura auren ba ni da lafiya shi ya hana ni fita ko'ina balle na je na gaisa da ku mu san juna Idan ka samu lafiya ai sai ka yi Allah ya kara afuwa Amin thank you Ya zauna kusa da Hurriya yana kallonta. Baya bukatar tambaya ya san wannan duk shirin mahaifinsa ne, dan haka ya dauki wayarsa yayi ma mahaifinsa text. Thank You, you're the best Dad in the whole world Ya aje wayar a gefensa ya maida hannunsa a gurin Hurriya dake matsawa a hankali domin tana jinsa daf da ita. Ya jikin? A madadin ya amsa mata sai ya kalli dan space din dake tsakaninsu yayi murmushi, wani kalar nishadi da farinciki ne zuciyarsa na ganin matarsa labarin zuciyaa tambayi fuska in ji hausawa, sai yake jin ya warke daga fever ma. Rukayya ta mike tsaye tana rike da wayarta. Bari na jira a waje Dama dai kin wuce gida zai fi, domin Hurriya ba yanzu zata koma ba sai dare Gwaggo bata ce na barta ba, cewa aka yi