← Book details Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 143

Sashe 8

Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aminta ba saboda yana son yayansa kamar yadda yake son uwarsu, Allah ya tabbatar mana da alheri Hajiya Binta na kaiwa nan ta katse kiran. Wani irin bille baki Hajiya Kaltume tayi ta kube shi. Munafurcin banza da wofi, wato ga Kaltume makiyiyar Iyami da yayanta har da wani kira ki bani amanar yara, ko mutuwa ta yi ai ba zan karbi amanar yayanta ba balle tana da rai, idan kin isa ki saka ya dawo da ita mu gani, har kina fada min yana son yayansa kamar yadda yake son matarsa tsabar kin raina ni Duk wani farinciki da walwala dake zuciyarta da fuskarta ya gushe tun daga lokacin da ta ji cewar sakin aya aka yi ma Iyami kuma an bata kyautar kudi da gida. Wallahi Iyami kin cuce ni, ko a haka dai kin ci ribar mijina, kin haihu da shi dan ki ci gado, kuma yanzu ya sake ki ya dauki gida da miliyan ashirin ya baki, waya taba yi ma kyautar gida a cikinmu matansa, sai dai ko wace ta siya da kudinta Password din wayar ta cire ta duba kiran dake kasam na surukarta Hajiya Binta ta taba na Hajiya Fatee. Kamin ta amsa duk ta kagu har ta fara saba da marwa a dakin. Assalamu Alaikum Kaltume Hajiya Fatee zama be gan ni, tsugune bata kare ba, Saki daya Alhaji yayi ma Iyami, kuma wani abun da ya fi ko wane bakin ciki kudi ya dauka ya bata har naira miliyan ashiri Million ashiri? Ai ba nan haushin yake ba, ya bata kyautar gidansa dake samaru, yanzu uwarsa ta kira tana fada min har wani gargadi take min saboda ya san gatan jikokinta, kin san ba jikokin da take so irinsu, kuma tun da saki daya ne zata iya buga kafa a kasa tace sai ya maida uwarsu Tsab kuwa wannan shegiyar tsohuwar zata iya, saboda ba sonki take ba Ina fa, kuma ba ba zancen dawowarta kina ganin zan yarda Iyami ta bar gidan mijina kuma ta yi arziki da dukiyar mijina? Wallahi bata isa ba ai yadda ta ci amanata haka ni ma zan nuna mata ruwa ba sa'an kwando ba ne, sai an koya ma Iyami hankali, dan haka ki shirya tafiya gobe goben nan nake son mu tafi ba sai wata rana ba, kar mu sake ayi mana sakiya, domin ita ma zata iya shiga nata malaman ta janyo hankalinsa Maganarki haka take Kaltume, karki damu zan kira shi tun yau na fada masa gobe zamu zo, amman fa ki zo da wuri saboda kin san dajin nan babu an mutum ga halin da ake ciki kara mu yi tafiyar safe kar mu yi mugun gamo In Sha Allah karfe 8am a gidanki zata yi min, sai na zo Daga haka suka yi sallama, Hajiya Kaltume tana kwafa tana jinjina lamarin. IYAMI POV. Ban san me ya hana shi daukar wayata ba, kunyar abun da ya aikata yake ji ko kuma rainin wayo ne da raina talaka Gwaggo ta kalli Bappa dake maganar ta girgiza kai. Alhaji Haruna ba shi da dabi'ar raina talaka, domin be taba mana haka ba wata kila dai yana jin kunyar abun da ya aikata ne, wata kila kuma baya son ka yi masa magana komawarta ne Iyami ta kalli Bappa cikin karfin hali ta ce. Bappa da dai zaka kyale shi da ka kyauta min, domin na yi ta tambayarsa ko na masa wani laifin ne, amman ya ce ban masa komai ba, kawai dai bana jin natsuwar zaman aure da ni ne a yanzu Tun da can be san da wannan ba sai yanzu? Kuma be tashi sakinki sai yanzu da ciki wata shida? Ba saki yayi mata na wulakanci ba, ya kyautata mata daidai gwargwadon yadda ake son kyautatawa a saki da zaman aure, kuma aure rai ne da shi ko babu komai idan lokacin rabuwa yayi dole sai an rabu, mu dan bashi lokaci har ya dawo hayyacinsa ni na tabbatar Alhaji Haruna yana son Iyami akwai dai abun da aka yi Wannan karon Gwaggo ce take maganar. Bappa ya mike tsaye yana ja tsaki. Akwai yadda aka yi na me? Ku yi komai ba za su bar shi ga Allah ba sai kun ci wani abu, yanzu zaki iya cewa asiri aka yi masa, kar ma ki kawo wannan maganar, ni na fita Toh Allah ya dawo da kai lafiya Ameen Ya fice yana sake gwada kiran number Alhaji Haruna Mai Yadi. Fitarsa da kamar minti uku Hindu ta shigo dakin tana sallama, Gwaggo ta amsa mata. A bakin kofar dakin ta saki jakar hannunta tana kallon amiyarta. Iyami da gaske Alhaji ya sake ki? Iyami na kallonta sai hawaye suka zubo mata, Gwaggo na ganin haka ta mike tsaye ta fice daga dakin domin bawa kawaye damar tattaunawa. ________________ Masu karatu kuna ganin Alhaji Haruna ya yi ma kansa mai kyau kuwa? Ya Hurriya zata ji idan ta san cewar Appa sakin Ammanta ya yi? [10/18, 5:34 PM] Nana 1: https://chat.whatsapp.com/GJ9hOtbWbfDKmq8NrKsDIG Akwai matukar mamaki ace duk son da Appan Hurriya yake miki ya sake ki, saki fa Iyami? Amma ta saka hannu biyu ta share hawayen fuskarta. Ni ma dai ganin nake kamar ba sakin ba ne, saboda ban saka ran ba mutuwa ce zata raba ba, har yanzu tunani nake ko dai boye min yayi? Wata kila na masa wani laifi ban sani ba Bayan kin ce ya fada miki baki masa komai ba? Hindu namiji na sakinka haka nan? Ai na ga sai da dalili Dalili daya ne Iyami sa'ar da matansa suke nema sun samu, kin mata a cikin manyan mata kuma tsofin mata kike zaune? Matan da sun kusa sa'ar gwaggo? Wace ce warinki a cikinsu? Iyami babu kalar kazafi da kage da ba su miki ba duk dan saboda ki bar gidan amman burinsu be cika ba sai a yau, maganin ma na san sun gwada Allah dai ne be ba su sa'a ba sai yau Hindu Waallahi ina son mijina, mijina kuma yana so na amman yau komai ya kare Amma ta fashe da kuka. Har sai kin fada? Ai kowa ya san yadda kuke zaune ya san mijinki yana sonki kuma ke ma kina sonsa, sakin ma da zai miki Iyami na musamman yayi wane namiji ne zai saki mace ya dauki dukiya ya danka mata? Ai sai zababbu cikin mata, kuma ko yanzu karki yanke kauna In Shaa Allah zaki koma dakinki ki cigaba da addu'a nima kuma zan taya ki kuma ki saka ayi miki a islamiyayo nima kuma zan zaka ayi miki Kasa cewa komai Amma ta yi sai kuka take kukan da da zaka iya rantsewa mutuwa aka yi mata, idan ta tuna da sakinta Appan Hurriya yayi sai ta ji zuciyarta ta narke ta rasa me ke mata dadi a duniyar nan da ace mutuwa yayi sai ta dangana amman tunawa cewar yana raye kuma shi da kansa ya zabi rabuwa da ita ya fi komai daga mata hankali. Toh wai a can kika bar su Hurriya? Ya ce zai rike su Ta amsa mata cikin kuka. Hindu bata wani dade a gidan ba ta mata sallama ta fita domin komawa nata gidam ta dora girki. Haka ta wuni a daki idan Gwaggo da jikokinta suka shigo sai ta boye fuskarta ta danne kukanta har sai idan ta kadaita ita kadai, tunanin yaranta ya tsaya mata a rai, tana ta auna lokacin dawowarsu makaranta da kuma irin abubuwan da suke idan sun dawo, da dare yayi sai ta kasa bacci domin wannan ne daren farko da zata kauna a gidansu tun bayan aurenta shekara goma sha shida. Ko biki ake a gidan ko wata hidima Appa baya barin ta kwana ko da kuwa ba girkinta. Daren sai ya zame mata wani dare na dabam da bacci ya gagara kusantar idonta ma balle har ya sace ta, kukan ma sai ta neme shi ta rasa wata zuciyar nata raya mata hanyoyin da zata bi ta shirya da mijinta sai ta saka zaren idan ta karshe sai ga ba hanya ce mai bullewa ba, dare ne da yayi mata tsawo fiye da sauran dararen da suka gabata, karfe biyu da rabi ta doro alwala ta fara raya daren da sallah nafila a haka aka kira sallah asuba akan idonta. HURRIYA POV. Da murna ta shigo dakin Appanta ta zauna kusa da shi a kasa kamar yadda ta saba, sai ya kai hannu ya shafa kanta zuwa bayanta yana murmushi irin murmushin nan dake dauke da so da kauna da kuma farincikin abun da idanuwa suka yi arba da su. Hurriya toh yaya? Lafiya kalau Appa, ka dawo lafiya? Lafiya Kalau, ina can gurin aiki zuciya na nan tare da ku sai tunaninku nake Ina Hamad Shi ya ce ba zai zo ba? Ta amsa tana kai hannu ta gyara gilashin idonta. Hajiya Kaltume dake zaune kan carpet ta yi murmushi, irin murmushin nan da ya zame mata dole ne, domin ta kasa hadeye maganar da Appa yayi cewa yana gurin aiki zuciyarsa na gurin yayansa ta ce. Hamad ai ba zai zo ba, dazun ma dukanta yayi ya fasa mata gilashi sai da Yasir ya shiga tsakaninsu Appa ya kalli Hurriya cikin yanayin damuwa. Me ya hada ku? Ta zayyana masa abun da ya faru daga karshe ta rufe da fadar Yasir ya shirya su. Appa ya sauke ajiyar zuciya Ina ganin yaran nan za su koma gurin bangarenki sa zama Kaltume, saboda a rika saka musu ido, kar wata Hamad ya ji ma yarinyar ciwo, daman ko dan kula da abincin da wasu abubuwan dole su koma can Gurina kuma Alhaji? Ni da nake da yan mata cike da daki? Kuma ka san yadda bama jituwa da uwar yarinyar nan yanzu nan Hurriya ko kaya ta taka na cire mata cewa za ayi na cutar da ita, ba zan hana ta zama ba idan haka kake so, amman dai da zaka barta a hannun Nafisa wata kila zamu samun zaman lafiya, daman Nafisa bata da yara da yawa uku ne kawai kuma mazan fita suke Namra ce kawai ka ga ta samu yar'uwa a kusa ko? Amman ni Hajiya ma sai tace na mata ba daidai ba
Chapter 8 · 0% Book details