Sashe 22
Huriyya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ni Nafisa, yaushe aka yi haka? Kuma shi kenan daga fada maka zance karya da gaskiya sai ka hau ka zauna har da zuwa gurin fada ba tare da ka tsaya ka bincika ba? Shiyasa ka dauko su ka kawo min? Me yasa ba a kaiwa Kaltume ba? Ita da yake tsoronta kake sai Nafisa da aka raina itace mai dadi hawa, gashi sai mulki take mana ciki gidan ita da yaranta Daga ke har ita karkashin kulawata kuke kuma karkashin ikona, dan haka duk gurin da nake ra'ayi a can yarana za su zauna, kuma ina gargadinki wannan ya zama na karshe da zan sake jin wani abu marar dadi akan Hurriya da Hamad, zan iya canja mata ban zanja yaya ba, gaba daya yarana babu na yarwa kuma bana son a batawa kowa Eh amman ai ka ware wadanda kake so kake kauna, na tabbatar da nawa yayan Kaltume ko Iyami take yi ma wani abu ba zaka yi magana ba, amman da yake yayan mowa ne ai gashi nan ka shigo falo cikin bacin rai saboda an taba yan gold, ni da zaka nuna musu kauna ka dawo da uwarsu ai da duk yafi wannan nema musu yanci da kake, idan ya so sai ta rike yayanta na rike nawa Abun da na ga damar aiwatarwa shi zan aiwatar, babu mai fada min gabas, na san Allah, daman ke haka kike banta zuwa da wata magana ba ki musa min ba, ban taba fada kin yi shiru kin saurareni ba sai kin fada, sa'insa da ni ba yau kika fara ba, daga ke har Kaltume babu wadda nake jin sanyinta kowacce ku da lagon da take matsawa ta bata min rai Momy ta fashe da kuka domin kalaman Appa sun mata zafi, ta san abun da Appa ya fada akam Iyami gaskiya ne, domin ya saba yi mata fada ko a gabansu kamar yadda su ma zai iya musu a gabanta ko kuma ya tara su gaba daya yayi musu fadan idan wani abu ya faru, su kan tanka shi su kare kansu ko maida martani amman Iyami bata cewa idan yana fada har yayi ya gama, ko daga kai ba zata yi ta kalleshi ba, wannan ta saka suke yawan yi mata kallon munafuka, hawaye shar Momy take yi daman kuma bata gama hucewa daga bacin ran abun da aka yi ma Captain ba. Eh sai Iyami, abar kaunarka, yanzu gashi nan ka rufe da fada akan yayanta, matarka Kaltume kuma ta takura min ta takurawa bakina, yanzu Captain ne ya zo, ka san dai yadda nake da Captain amman haka matar nan ta saka aka fasa mata tayun mota saboda bakin ciki, ban gama huce wannan haushin ba gashi nan kai kuma ka zo ka rufe ni da wani, toh Wallahi ka jawa yayanka kunne su daina munafurci, kuma ka jawa matarka matarka kunne ta fita safgata da ta bakina babu ruwanta da ni idan ba haka ba Wallahi za 'ayi tashin hankali da ba taba yi ba ko a lokacin da ka auro karamar yarinyar can Iyami Ni dai na fada miki, karki sake banbanta min to a duk daya suke a gurina, babu wanda ya fi wani, zan iya canja mata ban canja a ba bana ni da kamar ana! Yana kawai nan ya juya ya fice, cikin motarsa ya koma yaja ta zuwa bangare ya ajeta ya fito ya taka da kafa ya nufi bangaren Hajiya Kaltume yana shiga ita ma ya salllami yaranta suka haura sama ban da Yasir da baya gidan ma a lokacin ya fita gurin safgoginsa, Namra kuma ta fita zuwa bangarensu. Fada yayi mata sosai yana ja mata kunne akan abun da ta saka aka yi ma Momy. La'ilaha Illallahu ni Ummul Kultoon, yaushe kuma aka yi haka? Ni miye ruwana da Nafisa balle kuma bakinta, yanzu Fisabillahi na rasa me zan saka ayi mata sai fashe tayar baki? Abu dai kamar karamar yarinyar? Ni da nake ta kaina ma? Yaushe na fito daga daji? Kofar daki ma bana sha'awar fita balle kuma har na saka ayi wani abun, shigowar nan da ka yi ma hankalina sai da ya tashi Ni dai na gargadeku, bana son wani tashin hankali kowa ya zauna lafiya kuma ya tsaya a iya matsayinsa, ku bar ni da abun da yake damuna, kullum ni ne cikin fitina kamar akaina aka fara mata aure da mata biyu Mata uku dai Alhaji, yaushe ka saki yarinyar can Iyami da har zaka dawo kanmu nu kadai, musamman ni, taya za a ce na fasa tayar mota? Yara ma wa zan saka yayi wannan aiki? So take ta zugaka ka koreni a gidan kamar yadda ka kori Iyami, to Wallahi ni kam zama daram dam dam dam sai mutuwa, kuma Alhaji dan Allah ka rika bincike kamin ka fara fada, Wallahi sheri ne kawai na kishiya da neman hada mata da miji, abun da ba ayi ba da kurci ayi shi yanzu Na dai ja muku kune, kowa ya tsaya iya matsayinsa bana son sake jin wata fitar Har Appa ya fice Hajiya Kaltume bata gama mamakin jin irin kagen da Momy ta yi mata ba, Salma ce ta fara saukowa sannan Khairi suna tambayar me ya faru domin sun lura da yadda mahaifinsu ya shigo cikin fushi. Wai munafurci matar nan ta hada, wai na tura an fashewa bakinta tayun mota, shi kuma babu tsayawa bincike da yake ta mallake shi komai ta fada masa shi yake yi kawai ya zo ya rufe ni da fada, ai bari Wallahi ita ma sai ta bar gidan nan Kamar yadda Iyami ta fitar da ni, waya sani ko gurin tsafinta ta tafi aka bata wani asirin ace ta zo ta hada mu, gaba daya ta mallake Alhaji ta juye masa kai komai ta fada sai ya hau ya zauna Tab Lallai Momy ta yi nisa, wane irin fasa tayun mota kuma? Hajiya Kaltume ta kalli Salma dake maganar. Sheri ne kawai a samu yadda za a hada ni fada da Alhaji sai ya sake ni Haka Hajiya ta yi ta jininin maganar tana ta masifar har yamma. *** *** *** Hajiya Binta dake gidan baya tana shafa kan Hurriya dake kwance jikinta ta ce. Tsoho kamin ka kai ni gida, ina son ka biya da ni gidansu Iyami na dubata yaranta ma su ganta Kamar wadda aka cewa ya shiga ramen wuta haka Appa yaji, ko kadan be son abun da zai kusantashi da Iyami gashi kuma be isa ya musawa Hajiya ba. Toh Hajiya amman idan na aje ki Yasir zai zo ya dauke ki ya maida ke gida su kuma yara ya dawo da su Toh zamu tafi gidan makiyiyarka ba, Allah ya kyauta Haba Hajiya irin wannan maganar be dace ba a gaban yara ban da alheri me iyami ta yi min da zan dauki kiyaya na bita da ita Hajiya dai bata sake cewa komai ba har Appa ya canja hanya ya dauki hanyar gidansu Iyami. A bakin gate din ya faka, ya fito ya budewa Hajiya ta fito tare da Hurriya sannan Hamad ya bude front door ya fito. Ba zaka tsaya ta fito ku gaisa ba? A gaishe ta dai Hajiya Ya amsa yana kin hada ido da Hajiya Binta, girgiza kai kawai Hajiya ta yi ta cira kafa suka karasa bakin madaidaicin gate din da tuni Hamad ya bude har ya shiga ciki. Yanayin yadda Hajiya Binta ta tararda Iyami be mata dadi ba, daman kuma ta san za'a rine wai an saci zanen mahauciya, mai ciki ba a rabata da laulayi balle kuma ita da take cikin damuwa, sai dai ganin Hajiya Binta ya saka ta ji kamar an dauke mata ciwo, suka ta yi hira kamar yadda suka saba. Jiya muke zancenki da Gwaggo na ce ina tuna haihuwar Hurriya da irin hidimar da kika yi Hajiya Binta ta yi murmushi. Abu kamar jiya, yanzu Hurriya ta cika sha shida cif Hurriya ta wara ido tana mamaki yadda ta manta birthday dinta. Eh fa Hajiya amman ai sai October 10 To October ba ya kusa ba? Miye rage yan kwanaki ne kawai Hajiya zaki yi ma Appa magana yayi min celebration please Iyami ta ce. Kin san halin Appanki ba son irin abubuwan nan yake ba, shi gaba daya rayuwarsa irin ta mutanen da ne Zan masa magana da kaina, maybe zai yi min gashi ma dazun ya fada mana a falon Hajiya ya ce ni da Hamad a waje zamu yi karatu Mamaki ya cika Amma har sai da ta bude baki ta kalli Hajiya dake murmushi. Shi da kansa? Shi da kansa fa, sai dai ki yi ta addu'a kuma ki yi musu, ai maso uwa ya so yayanta, abu dai ne idan ya zo babu yadda za'ayi sai hakuri kawai, amman sakin nan ba karamin mamaki ya ba ni ba Amma ta sauke kai kasa tana jin wani rashin dadi yana ziyartar zuciyarta. Hurriya ta tashi ta fice zuwa dakin Anty Rukayya haka take jjnta kamar wata sa'arta saboda tana wasa da ita sosai kamar yaya da kanwa, wannan ya saka Hurriya bata kallon Rukayya a matsayin kanwar Amma sai idan babin girmamawa ne, ba ita ba ko Hamad wasa yake da ita, daman kuma hausawa sun ce karamar uwa madaukar zunubi. Amma ta ce Haka Allah ya so Hajiya komai Allah ne yake tsarawa Allah dai ya ba mu ikon cinye jarrabawar wannan jarabarwar Toh Ameen ina nan ina ta addu'a, da yardar Allah Iyami sai kin koma dakin domin sakin nan naki har hawan jini yake son tasar min, Allah ya sauke ki lafiya, da na shiga gidan ma sai na ji duk yayi min dabam Ameen Amma ta amsa tana jin zafin barin gidan Appa da ta yi, ba tare da laifin komai ba. Gwaggo ce ta shigo suka suka ta hiran kowa yana fadin abun da ya fahimta game da lamarin, Amma kuma tana fadar yadda Appa ya canja mata tun kamin sakin. Cikar da cikin Hajiya Binta yayi a gidan danta be hana ta cin abinci a gidan Amma ba, saboda tana son Amma kuma ta san idan bata ci ba Amma zata ji babu dadi domin abinci Amma take